← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 66

Sashe 30

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbu da Ummi ne suka zo taryan mu, haka muka shiga motan su in da driver ya ke jan mu har gida, a hanya Amaal kaman zata shige cikin Ummi, sai wani shagwaɓa ta ke ta mata, akan ko ina a jikin ta ciwo yake yi ma ta, ita kuma Ummi sai rarrashin ta ta ke yi, a haka har muka iso gidan, ni dai sai bin su da kallo kawai na ke yi, don gaba ɗaya sun ban sha'awa, sai smilling na ke tayi ina kallon su.

Kai gidan su Amaal ya haɗu, domin bansan yadda zan kwatan ta muku irin kyaun shi ba, duk da gidan mu yana da kyau amma tsarin ginin larabawa ba wasa bane, duk da muma daga waje Daddy ya kawo zanen da za'a mishi, amma gidan su Amaal ya ɗauki hankali na over, muna shiga parlon gidan gaba ɗaya ma sai naji ya tafi da hankali na, gaba ɗaya wani tsari ne da bazan iya rubuta shi ba a ɗan ƙaramin book ɗi na ba, sai dai kawai ku kwatantashi.

ga wani ƙamshi na musamman da ya ke yi, ɗakin Amaal Ummi ta raka mu in da shima aka mishi gyara na musammam, duk yadda ɗaki na ya kai da girma na Amaal ma ya yi biyun shi, domin wani gyara da akaman sai ya baka mamaki, bed biyu aka saka amma duk da haka da sauran space a ɗakin, bamu daɗe ba Ummi tace muyi wanka mu fito parlor mu ci abinci, haka muka shiga muka yi wanka, wani riga da wando ɗan pakistan Ummi ta kawo mana muka saka, sai ƙamshi muke yi kaman daga paris muka fito.

Muna kan dinning babu abinda ka keji sai ƙaran spoons, sai kuma daga parlor kana jin sautin news da a keyi a TV, gaskiya larabawa sun iya girki, idan ba wai santi ba sai nace sun fi ko wani ƴan country iya abinci, domin naji daɗin abincin da Ummi ta mana, domin duk dukiya na gidan su Amaal amma Ummi tana shiga kitchen, duk da yawan masu aiki da ke gidan amma tana saka hannu a aikin kitchen kaman wata ƴar nigeria, hakan yasa naga Amaal ta iya girki kala-kala, ga snacks da drinks iri da kala da ta iya, don bansaka girman kai ba duk sai da na koya a wurin ta, nima na gwada ma ta na ƙasan mu.

Parlor muka dawo muka zauna muna ta hiran school, anan Ummi ta ke gaya mana next week Faisal ma zai zo hutun 3weeks, haka muka yita hira kaman zasu ƙashe mu.

Kullum garin Allah ya waye sai mun yi waya da Daddy, yana gaya mun irin dauriyan da yake na rashin gani na, hakan zan ta bashi haƙuri, har da yace mun dabadan wani business daya sako shi a gaba ba zai tafi china, da yazo ya mun ko 1week ne, haka kullum za muyi ta hira, kuma yana gaya mun sunyi waya da Dr Hussain.

Allah sarki Baby nah, kullum dare idan muna waya ya dinga ƙorafin wai rana baya gudu dare ma baya gudu, haka zan ta mishi dariya, watara na muna hira nace,

"Dr mu to kaje wurin su Ummin ka mana ka yi hutu, kada kaÉ—aici ya dame ka kaji Dr nah".
Na faÉ—a kaman zan mishi kuka.

Kashe wayan ba tare da yace mun uffan ba, da sauri na saka hannu na rufe baki na ina tuna ranan fa yace mun kada na sa ke mishi magana su Hassan da su Abban shi, a zuciya na nace,

"me yasa bana jin magana ne".
Da sauri na ƙira wayan shi amma firr yaƙi ɗauka, haka na yi haƙuri na kwanta ina ta saƙe-saƙe a zuciya ta.

_DON ALLAH KUYI HAƘURI BANA JIN DAƊIN JIKI NA NE._

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/20, 12:37] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 24📑*

*__________📖* 2dys da zuwan mu DAMMAM Faisal ya iso, kai masha Allah wato Faisal ya ninka Amaal kyau sau babu adadi, ga wani class a tattare da shi, lokacin da na fito parlor inda suke ta murnan ganin shi tsayawa nayi ina kallon inda yake bakina ɗauke da murmushi, Amaal ce ta nuna mishi ni tana dariya tace, "Humairah" da sauri ya juyo inda nake ya ƙura mun ido yana murmushi shima.

Ganin haka ya saka ni takowa zuwa inda suke cikin tafiyata kaman na tarwaɗa tsaban yauƙi daya mun yawa, wani ɗan sautin dariya ne marar ƙarfi ya ɗan suɓuce mishi a bakin shi, a hankali ya furta, "woow beautifull" sannan ya juya ya kalli Ummi yana murmushi yace, "Kai Ummi yarinyar tana da kyau da yanga, Ummi ina son yanga a wurin mace" hararan shi Ummi tayi tace, "Hummy sister ka ce fa, don haka bana son fitina".

Ina ƙarasowa na mishi sallama har lokacin bakina ɗauke da murmushi, da sauri ya kamo hannu na ya jawo ni jikin shi ya rungume ni irin yadda suke gaisuwan su, sannan ya sumbaci kuncina, ba karamin faɗuwar gaba naji ba don gaskiya ni ba'a taɓa mun haka ba, gara ma Abbu da safe haka yake mana amma bana jin komai saboda shi ae uba ne, amma wannan gantsamemen saurayin fah? Ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinshi kaman wani amaryah, cikin ƙarfin hali nake gaisheshi saboda har lokacin bai sake ni ba saidai ya ɗago ni daga jikinshi yana riƙe da kafaɗa na duka biyun, ga wani murmushi mai masifan kyau a fuskan shi.

Ya kamata naji haushin abinda yamun amma sai naji na kasa saboda wani irin kyau da kwarjini da ya mun, ga shi mai tsafta É—an gayu, ina murmushi na saka hannu na ina cire nashi da yake kafaÉ—a na, a hanakali yace, "kina da masifan kyau Hummy, kyaun ki mai kyau ne" gabana naji ya faÉ—i, gaskiya Faisal ya haÉ—u duk da bai kai Dr nah kyau ba, amma yau É—aya yamun abinda Dr na ya kasa yimun kusan 4month, yau kalman da nake so naji a na yawan furta mun ni mai kyauce Faisal ya furta mun har yana wani kashe mun ido.

Wucewa nayi inda Ummi ta ke zaune na zauna a gefenta , har zuwa lokacin fuskana ɗauke da murmushi, domin haka kawau Faisal ya sauƙe mun wani nishaɗi a zuciyata, gaskiya ni Humairah me kyauce, amma haka kawai nake jin son kyawawan mutane, don bana mantawa idan kakata wadda ta haifi Mamana idan tazo duk inda tayi na dinga kallonta kenan, domin ba ƙaramin kyau takeyi mun ba, gata da gashi mai tsawon gaske, bana gajjiya da kallonta, haka ita kanta Amaal bana gajjiya da ganinta domin kyau ta keyi mun, yau ɗaya naga Faisal yafi mun Amaal kyau, gashi shima yana yaba nawa kyaun.

Da sauri na ɗaga kaina domin jin abinda Faisal yake gayawa Amaal, "sister dama haka Hummy ta ke da kyau shi ne baki taɓa nuna mun ita ba? bayan na biki ko a photo ne ki nuna mun ita amma kinƙi, ashe mai kyau aka ɓoye mun? gaskiya gara da nazo na ganta da kaina", ya juya wurin Ummi yana murmushi ya dafa cinyan ta yana magana cikin shagwaɓa, "gaskiya ni Ummi ina son Hummy na gaskiya bana wasa ba, gaskiya Ummi nikan dani ta dace, ko ajiye mun ita na kusa gama karatuna", ya faɗa yana kwantar da kanshi kan cinyan Ummi, idon shi kuma duk ya sauƙe mun su, sai wani kashe mun ido kawai ya keyi da zaran mun haɗa ido, nidai kunyan shi kawai nakeji, sai wani smilling mai ɗauke hankali na ke tayi.

"Baka isa ba wallahi bros Faisal, ta yayah ma zanyi wa Dr Hussain haka? gaskiya toh wasan ma ya isa haka, bayan Hummy da Dr sun amincewa junan su, gaskiya kabar maganan nan bazai taɓa faruwa ba", ta faɗa tana miƙewa tsaye, idon ta akan Ummi tace "Ummi ki gaya mishi gaskiya ya dai na irin haka, ni bazai saka naji kunyan Dr ba", sannan ta kamo hannu na tace, "mu tafi ɗaki hummy".

Miƙewa yayi shi ma yana hararanta yace, "wallahi sis baki isa ba, kinsan haka ta ke shi ne zaki wani sako ni acikin shirmenki, toh ni ma ae namiji ne saidai kowa ya gwada jarumtar shi, wanda yayi nasara Humairah ta zama rabon shi, kuma kibar yarinya ta zauna a inda ya mata bawai ki kai ta bedroom ki kulleta ba", ya ƙarasa faɗin maganan yana kamo hannu na, da sauri na juyo na dubi Ummi da ta zuba mana dukkan idonta akan mu bakinta a buɗe, maida kallo na nayi kan shi amma da sauri na kawar da kaina ina ƙoƙarin ƙwace hannu na, domin ni ban san me nake gani a cikin idon shi ba, gashi bana son ya riƙe ni amma kuma bani da ƙarfin gwiwan hana shi, narai-narai nayi da ido alaman zan mishi kuka domin nakasa ƙwace hannu na.

Sun kuyawa yayi dai-dai kunne na yace, "kada ki tafi da bugun zuciyata ya ke ma'abociyar kyau na duniya, nafi son na dinga ganin kyakkyawan idon ki da ɗan ƙaramin bakin ki mai matuƙar tafiya da hankalina a kusa dani ya mai kyau", wayyo Allah jina nayi numfashi na yana shirin tafiya lokaci ɗaya, abin na kwace hannuna daga nashi sai na samu kaina da ƙara damƙe hannun shi cikin nawa, wanda bansan dalilina nayin hakan ba.

Ganin haka ya daka Ummi miƙewa da sauri tace, "sakar mata hannu fav, baka san abunda kake yi mata ya saɓawa shari'an musulunci ba, ko ce maka akayi hannun Amaal kake rike da shi? bana son sakarci, sake mata hannunta ta bi ƴar'uwarta".
Chapter 30 · 0% Book details