← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 66

Sashe 62

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raba jikin su Aisha tayi ta turo baki gaba tace, "naƙi wayon ni zan haifawa Yayah Hussain mata, don ni ya chanchanci na zaɓa mishi mata, Mamie ni zan haifa mishi mata, da ina son na haifi ɗa namiji don na saka sunan yayah Hussain, amma yanzu mace nake so, na saka mata Aisha juniour don na bashi ya aura, kuma na saka shi yayi ta mata son da bai mun ba", ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.

Ranan naga soyayyah tsakanin uwa da Æ´arta, haka dai na koma ban shigo ba awanann lokacin, sai kusan magrib na dawo muka gaisa.

Bayan kwana biyu da zuwan Aunty hauwa Aisha ta tashi da naƙuda mai zafin gaske, wanda tun safen mukayi aisibiti da ita ana ganin haihuwar kaman yanzu amma abu shiru har azahar, dole ta saka na gayawa Umminta da Aunty hauwa, ganin yadda take ta neman su, da yake Ummin suna tare da Aunty hauwa a bauchi, ae kafin la'asar har sun iso Jos, kai hattah Baban Narabi sai da yazo, ranan naga dangi da irin soyayyar da suke nunawa Aisha, don Uncle Abdallah har labour room ya shiga, amma ganin yadda Aisha ta kumbura da kuka ya fito yana a nemo mishi likita ya cirewa ƴar shi cikin, gaba ɗaya hankalin su ya tashi ganin yadda Uncle Abdallah yake zubar da hawaye.

Ana ƙiran Dr yace babu komai mujira zuwa 1hr idan bata haihu ba sai ayi mata CS ɗin, amma ya kwantar mana da hankali akan cewa haihuwar fari ne ya jawo haka, bayan sallan ishaa, Aisha ta saka aka ƙirani nazo, hannu ta miƙo mun ta riƙe ni gam-gam.

"Baban Ahmad ka yafe mun duk abinda na maka, wanda na sani da wanda ban saniba," hawaye yana bin gefen idonta, kasa magana nayi sai jujjuya mata kaina da nakeyi, Aunty hauwa ce da Ummi da suke zaune a É—akin suka fara mata magana ta É—aina irin wannan maganan insha Allahu zata haihu lafiya, haka kowa ma yasha wahalan, murmushi tayi idonta da hawaye ta dube ni.

"Ka nemo mun Yayah Hussain ɗina kabashi abinda zan haifa kace ya riƙe mun amana, na bashi duniya da lahira, idan ba shiba bana so ka bawa kowa riƙon babyn, kai da kanka nake so ka riƙe bawai don nafi sonka a kan iyaye na ba, kawai ina son duk abinda zan haifa ya tashi a gaban mu, hannun iyayen shi, saboda duk abinda zai faru da shi ba za ace sunyi sakaci ba, kasan me yasa"?,

Ta tambayeni, wanda da sauri na jijjiga mata kaina da idona da yake tsiyayan hawaye, alaman ban sani ba.

Murmushi ta sakeyi tace, "Ummi na ta min riƙon da ko Aunty hauwa bazata iya mun ba, ta bani tarbiya da kulan da ko iyayena ba lallai bane su bani, amma abin baƙin ciki lokacin aure na da kai sai naji ɗaya daga dangin Baba na tana cewa, abin tausayi saboda riƙon muguntar da akayi mun da sakaci saboda ni ba ƴar Ummi ba, shiyasa ta bari ɗanta yayi raping ɗina don mugunta, gashi yanzu yarinya ƙarama marainiyar Allah zata ƙare da auren tsohu, ni kuma jin haka ya sa nayi alƙawarin ko bana sonka, zan zauna da kai na maka biyayyah don Ummi na tayi alfahari dani, saboda haka duk abinda zan haifa kai nake so ka riƙe bashi ko kabata irin naka tarbiyan da kulawan, har sai ka samu Yayah na ka danƙa mishi riƙon, don nayi imani da Allah ko mace ne, zai kula da ita bazai iya cutar da ita ba, koda shi kaɗai ne tare da ita ba zai cutar da ita ba", ta ƙarasa tana sauƙe ajiyar zuciya.

Kukan su Ummi ne ya ƙaru, ita kuma Aisha ta cigaba da faɗin, "Ummi ki yafe mun, mamie na ki yafe mun, kucewa Yayah Hassan ɗina na yafe mishi duniya da lahira, kuyi haƙuri bawai na hanaku riƙon abinda zan haifa bane, don nasan duk duniya babu wanda zai kai Ummina son riƙewa, amma bana son ƙara ja mata baƙin jini, kawai na amince ke ko mamie na ku riƙe babyn har zuwa 2yrs, sai ku maida riƙon hannun mahaifinta ko mahaifin shi, ku gayawa Yayah Hussain nayi burin sake ganin shi a rayuwata, amma insha Allahu abinda zan haifah zai nemo shi", ta faɗa tana runtse idonta da ƙarfi.

Likita ne ya shigo yace mu fita za a shiryata suyi mata CS, domin ga chan Babanta a waje sai faɗa yakeyi, jin haka ya saka na ɗan rankwafa na sumbaci goshinta na mata fatan alkhairi, Ummi da Aunty hauwa ma da ƙyar aka fitar dasu a ɗakin, inda nake jin muryan Ummi tana cewa, " Aisha insha Allah ke da hannun ki zaki raini abinda zaki haifa, kuma insha Allahu tare da abinda zaki haifa zaku nemo yayanki", ta faɗa tana ta kuka.

Fitowar nurse ne ya saka mu saurin zuwa inda ta ke, amma bata ce mana komai ba ta wuce da sauri ta ɗauko abu ta koma, chan bayan wasu mintuna sai gata ta fito da yarinya fara sosai a hannunta cikin farin kayan sanyi, da sauri Ummi ta ƙarasa jiki na rawa ta miƙa hannu tana faɗin, "Alhamdulillahi me muka samu? Yayah jikin ƴarmu kuma"?

"Baby girl" nurse ɗin ta amsa mata batare da wani rawan jiki ba, murmushi nayi kaɗan dana dubi fuskar ƴar bayan Uncle Abdallah ya ɗago mun yana murmushi yace, "kaga mun ɓarauniya, wato ta sato mun kaman nin ƴata kaf ko"? Ya faɗa yana juyo mun da fuskar ƴar dana kasa miƙa hannu na karɓa, Ummi ce da take ɗan murmushin yaƙe tace, "tace kaidai ka gode Allah da kuka samu wannan baturiyar ƴar ta ɗauko kamanin mu sak ita ma bata ɗauko naku ba", murmushi yayi yana duban Aunty hauwa yace, "Hauwa kishi ne haka da gaggawa? Don kinga wacce ta fiki fari da manyan ido"? Ita dai Aunty hauwa yadda nakasa maida hankali kan ƴar ita ma haka tayi, dole aka miƙawa Baban Narabi da Mama kaltun take zaune a gefen shi.

Yana karɓa kuma dr ya fito tare da abokan aikin shi, Hannu Uncle Abdallah ya miƙa mishi yana "sannun ku da aiki Dr, gara ae da akayi aikin, ae kunga uwa da ƴar duk sun huta", ɗaga kai Dr yayi yace, "Tabbas kuwa duk sun huta, domin ita ma Jaririyar ta huta da neman hanyar da zata fito, itama uwar ta huta da rayuwar da muke ciki mai cike da ƙalubale," shiru ya ɗanyi..... chan kuma sai yace, " ina mai bawa ahalin Aisha haƙuri da wannan babban rashi da akayi na wannan baiwar Allahn Aisha, domin a yau Aisha ta amsa ƙiran mahaliccinta, wanda dukkanmu munyi imani da Allah shi muke jira, saboda haka kuyi hakuri, wanda yafi mu sonta ya karɓi abinshi, amma gashi ya bamu madadinta".

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[9/12, 12:06] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1442H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 49📑*

*__________📖* ƙuuuu naji wani ƙaran da sai da yaso firgita ni, a razane kowa ya ɗago kanshi ya dubi uncle Abdallah da ya wanke Dr da mari, jikin shi na rawa ya chakomo wuyan rigan Dr yace, "kana hauka ne zaka ce Aisha ƴata ta rasu? Dubi iyaye da kakanunta da har yayunta duk a tsaye babu wanda ya mutu sai ƴata kake nufi? tou bazan yadda ba, komawa zakayi cikin ɗakin ka ɗauko ta mu chanja mata asibiti, ita kaɗai fah yaya Umar ya haifah, wa kake so na gani a madadin ɗan'uwa na"? kuka kuma ya fashe da shi bayan ya gama surutun shi wa Dr, hannu Baban Narabi ya miƙa ya riƙo Uncle Abdallah, sannan ya fara bawa Dr haƙuri, amma Dr bai wani ɗaga hankalin shi ba, yace wa Baban, "Baba ae haka zafin bugun mutuwa yake, mun saba ganin sama da haka ma, mudai addu'an mu Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya raya abinda ta haifa".

Sai lokacin idona ya kuma wurin su Ummi, amma wayam naga babu kowan su daga ita har Aunty hauwa, sai a lokacin naji muryan nurses ɗin suna basu haƙuri akan su ɗaga Aisha su bari a shiryata, nidai yadda kasan gunki haka nake bin kowa da kallo, sai wani bugawa da zuciyana yake yi kaman zai fito, a lokacin na daure naja ƙafana zuwa ɗakin da Aisha ta ke ciki, abunda na iya tunawa ɗaya ne, ina shiga naga gawan Aisha kwance akan gadon, gefe ɗaya wurin kanta kuma Aunty Hauwa ce ta kife tanata kuka a jikin Aishan, Ummi kuma ta riƙe ƙafan Aishan tana kuka tana magana, wanda gaba ɗaya bana fahimtan me suke cewa, ban ƙarasa sanin me ake ciki ba, sai zuwa wani lokaci naji muryan Baban Tilde yana cewa.

"Alhamdulillah! Muhammadun ma ya farfaÉ—o, a dakata yaje yayi mata addu'a", haka naji muryan Baban Tilde akaina.

Jin haka ya saka ni da sauri na miƙe zaune, da ƙarfi na furta, "Baba da gaske ne Aishan nawa ta rasu? Ko dai na razana da wuyan haihuwar da take shane nayi mafarkin ta rasu? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ina Aishan ne take Baba"? na faɗa ina miƙewa tsaye.
Chapter 62 · 0% Book details