← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 66

Sashe 18

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya na yi har ina buga ƙafa na, muka tafa da Hassan sannan nace,
"Allah Ummi bazan faɗawa wata mace tana da kyau ba har sai matar da zan aura, ita ma kuma har sai ta shigo gida na zan gaya mata, domin zai fi mata daɗi, amma haka kawai na ƙarasar da kalma mai girma da daraja tun a waje? Lokacin da ya kamata na faɗa kuma ya zama bai mata daɗi ba? Gaskiya Ummi na ma gudu".

da gudu na fita a ɗakin Ummi, wanda ina jin dariyan Hassan kaman zai tada Parlon ita kuma Aisha sai kuka ta ke tayi, Ummi na bata haƙuri.

Fita ya yi a kitchen É—in cikin jimamin rashin familyn shi da ya yi na shekaru da dama a tare da shi? Ko ya ya Ummi ta ke? Ya ya Hassan zai ji idan ya buÉ—i ido bai ganshi ba a rayuwar shi? Duk da suna yawan faÉ—a amma suna son junan su wanda babu wanda ya ke shiga tsakanin su, don ko suna faÉ—a idan wani ya saka baki to sun daina, sai dai su rungume junan su suna dariya, kuma ko ya ya Aisha ta ke? Ko yanzu yaran ta nawa? Wata aura? Allah sarki Abban su ko ya ya zai ji idan babu ni a rayuwar shi? Duk da sun kasance Æ´an biyu amma Abba yafi nunawa Hussain soyayya, Allah sarki Aunty Hauwa ita kam yasan hala sai tafi Ummi shiga damuwa.

Har ya shiga part É—in shi hankalin shi a tashe, yarasa me yasa tun haÉ—uwar shi da Hummy ya zama kullum suka haÉ—u sai ta tuna mishi da wani abu na familyn shi.

Kwanciya ya yi a parlor, sannan ya ƙira ni, ina ɗauka muryan shi a hankali yace,
"Babyn baby na tafi don Allah ki bawa baƙin nan abincin, naga kin wuce ɗaki bamuyi sallama ba".

"Naji yanzu ma ina kitchen É—inne, gudnyt".
na faɗa mishi ina kashe wayan, don har yanzu raina a ɓace ya ke da shi.

*#Comment, Vote & Share.*

*©AUNTY NICE CE* ✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*RIGIJI GABJI,RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO MASOYA_*

_*MARUBUCIYAR NAN TAKU WADDA TA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI INGANTATTU MASU TSUMA ZUCIYAR ME KARATU WATO HASSANA D'AN LARABAWA ,MARUBUCIYAR*:_

_SANADIN HOTO_
DA
_HASSANA DA HUSSAINA _

_*YAU TA SAKE DAWO MUKU DA SABON LITTAFINTA WANDA YA ZARCE DUK LITATTAFANTA A KOMAI WATO CIN AMANAR RUHI,KAI DAGA JIN SUNAN KUN SAN AKWAI TAFKA TAFKA DA K'ULLE K'ULLE ,AMMA ZATA WARWARE MUKU K'ULLIN DA ZARAR KUN BIYA 200 DOMIN SAMUN LITTAFIN,KAR KU BARI YA WUCEKU ,DOMIN WANI IRIN LABARI NE DA BAKU TAB'A CIN KARO DA IRINSA KO MAI KAMARSA BA,FAD'AKARWA ,NISHAD'ANTARWA,ILIMANTARWA,TAUSAYI,DA SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA ,TARE DA WATA IRIN CIN AMANA DA BAKU TAB'A RISKAR IRINTA BA,KU DAI KU HANZARTA NEMAN MARUBUCIYAR DOMIN KU SIYA KU KARANTA AKAN KUD'I K'ALILAN 200*_

_*ZAKU IYA NEMANATA AKAN LAMBARTA KAMAR HAKA,08080049548 DAGA NAN ZATA GAYA MUKU YADDA ZAKU BIYA KUD'IN ,KU DAI KU HANZARTA KAR AYI BABU KU ,KU TUNA DA SUNAN LITTAFIN*_

CIN AMANAR RUHI

_*NA MARUBUCIYAR KU HASSANA D'AN LARABAWA*🥰🥰🥰🥰_

*SHAFI NA 13 📑*

*__________📖* Ni dai ban san me ya faru ba, sai farkawa na yi cikin dare naga waya ta a yashe a gefe na, murmushi na yi ni ɗaya wayan na ɗaura a bedside drower, wato bacci nayi Dr yana mun waƙa ko? Kaɗa kai na nayi na shiga toilet.

Bayan na idar da sallan asuba, kitchen na wuce na zauna na fere dankalin, sannan na soya na soya ƙwai da plantain, na so na yi peppesoup, amma ganin babu time yasa kawai na kai musu kan dinning na ajiye ketchup a kan dinning ɗin, flasks na cika da ruwan lipton mai kayan ƙamshi, ina gama jerawa nayi sauri na shige toilet na yi wanka, gudu-gudu na fito na shirya, sannan na ɗauki breakfast ɗin kaɗan naci, note na ɗan rubutawa su Ummi sannan na ɗauki handbag ɗina na wuce zuwa school.

Ina fitowa na haɗu da Dr shima ya fito zai wuce school ɗin mu, murmushi yamun nima na mayar mishi, ƙarasowa yayi har in da na ke, sannan ya buɗe mun front sit na shiga, shi kuma ya zagaya wurin zaman driver.

Yana ta da motan na gaishe shi, yana kallon kan hanyan ya amsa, sannan ya tambaye ni ya ya baƙi na suka kwana? Ina murmushi na ce mishi, "lafiyan su ƙalau, amma basu fito ba na fito yanzu".

"Break fast fa, kin musu dai ko"?

ÆŠaga kai nayi alaman ehh na musu.

"Ni ne kawai ba kiyi dani ba ko?".
Hannu na saka na rufe baki na ina dariya.

"Hmmm dole kiyi dariya mana, tun da kin cika cikin ki ni kuma kin barni da yunwa, amma babu komai zanje wurin khadija nasan zata soya mun egg nasha da tea", ya faÉ—a yana murmushi.

Hararan shi nayi na turo baki na gaba ina ta ƙunƙuni.

"Ki faɗi abinda ya ke bakin ki zaifi miki sauƙi, amma harara na ba zai miki sauƙi a ranki ba".

"Ni bance komai ba, tun da nasan matar ka bata iya girki ba, hala ma idan taje soya ƙwan ya ƙone bata san yadda akeyi ba".

Dariya ya yi ya na shiga gate É—in school É—in, juyowa ya yi ya kalle ni bai ce komai ba sai murmushi, yana ta rawa da kanshi yana murmushi yana kallo na.

Muna isowa ƙofan department ɗin mu ya yi parking idon shi yana kallon wani wuri yana munafukin murmushi.

Hararan shi nayi a hankali na dubi in da ya ke kallon, Dr Khadija ce tsaye tana rufe motan ta, gefen ta kuma wata friend ɗin ta ce a tsaye suna magana, dawo da kallo na nayi kanshi, buɗe motan nayi na fita bata re da na ce mishi komai ba, ganin saura 15mnt a shiga mana class nayi sauri na ƙara sa hall ɗin da muke lectures, ina ganin yadda Dr Khadija da ƙawar ta suka bini da kallon mamaki, haka ma wasu daga cikin students da lecturers suka dinga bina da kallon mamaki.

Ina wucewa shima ya fito bayan yayi parking motan shi, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce office ɗin shi, ganin haka yasa Dr Khadija bin bayan shi da sauri ranta a ɓace, duk ƙiran da ƙawarta ke mata bata kula ta ba, ita dai sauri kawai ta iso shi taji dalilin shi na ɗauko ni a motan shi.

Ina shiga class ƴan class ɗin mu suka yi ta tambaya na ina Amal, wasu na gaya musu bata da lafiya, wasu kuma na sha re su ina duba note ɗin cost accounting da Ezeh ya miƙo mun, kuma ina maida hankali na kaɗan kanshi da naji shi ƙasa-ƙasa yana ce mun.

"Beauty dama Dr Hussain brother É—in kine ko?".
Ina kan buɗe note ɗin ban kalle shi ba nace, "Uncle ɗina ne, shi ɗin ƙanin Daddy na ne".

"Heyy no wonder mana naga yana tolerating ɗin ki, kaman wancan ranan da ki ka ba shi haƙuri ai ya dawo ya ci gaba da lectures, so yanzu kawai kice zan kama ƙafan ki don gaskiya bana son na faɗi a course ɗin shi seriously, kinsan 4 credit unit ne, kuma ga shi shine *PROGRAMME CO-ORDINATOR* Namu, don ma naji ance Professors ɗin nan ake bawa Heads of Departments, amma da an bashi na department na mu, saboda ƙoƙarin shi a department ɗin".

haka muka yi ta magana akan course É—in, kafin lecturer su fara shigowa.

Dr Khadija tana shigo mana ranan naga bala'in ɓacin rai kwance a fuskar ta, sai wani ɓata rai ta keyi kaman an saka ta dole, kuma tambaya ɗaya zata ɗaga ni tayi mun, abinda na lura nema ta keyi ta ga gazawa na, amma daya ke ni ɗin ba kanwar lasa bace, sai ta kasa samun in da zata ƙure ni, domin idan ba yabon kai ba, idan ku ka cire Ezeh to duk class ɗin ba zaka samu na sama dani ba, amma baza kasan hakan ba, sai an taɓo ni, saboda ni karatu na bana nunawa mutane bane.

Tana gamawa ta dubi ƙofa dai-dai lokacin Dr Hussain ya iso, dawo da kan ta tayi ta dube ni, fuska a ɗaure cikin shegen haɗaɗɗen turancin ta kaman na tsohuwar baturiyar england tace na sameta a office after na gama lectures.

Bance mata komai ba sai bin ta da ido da nayi ta tayi har ta bar class É—in, a lokacin Dr Hussain kuma ya shigo, ina ganin shi ya kauce ma ta ta fita, domin da yi tayi kaman zata bangaje shi, amma ba zaka gane ya ya yanayin fuskar shi yake ba, saboda babu yabo babu fallasa akan face É—in shi.

Tun da ya fara lectures bai kalli in da nake ba, sannan idan ya yi question baya duban in da na ke ballanta na ya mun tambayan, haka ya gama lectures É—in shi, yana gamawa ya tako har in da na ke zaune, yana kallon cikin ido na yace,

"kada na yadda naga kinje ƙiran da Khadija ta miki kin ji ko".
ÆŠaga mishi kai nayi alaman naji.

Yana duba na fuska a ya mutse yaÉ—an sunkuyo da fuskan shi saitin in da nawa ya ke yace,

"yunwa na keji Babyn baby".
ya ƙarasa faɗi kaman zai mun kuka, juyawa nayi da sauri na dubi ƴan class ɗin amma sai naga duk idon su yana kan mu.

ya mutsa fuska na yi ina nu na mishi alaman ana kallon mu fa, amma sai ya wani É—aga kafaÉ—a irin ko ajikin shi, ya sa ke sunkuyowa ya kwaikwayi murya na yace,
"Baby yunwa, wayyo babyn baby".
ya faÉ—a yana É—aura hannun shi akan cikin shi.
Chapter 18 · 0% Book details