← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 66

Sashe 64

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan har na dawo gidan tou zamanta dawowa yake yi inda nake, domin side É—ina sai da nayi mata É—akin wasanta, babu abinda ban zuba mata ba a É—akin, duk lokacin da take wurina tou biyeta nake yi muyita wasan tare, wanda hakan baya yiwa matar gidan daÉ—i, ganin haka ya saka ta rage shigowa side É—ina sai dai idan kwanciya zatayi.

Allah ya jarabce ni da son Humairah sama da komai a rayuwata, sannan duk inda zanje hankalina da tunanina yana gareta, shiyasa duk wani tafiya da zan daÉ—e na daina shi.

Humairah na da shekara tara, Allah ya karɓi ran dattijon kirki, wato Baban Narabi",......... Da sauri Dr Hussain ya ɗaga kai ya dubi Daddy a razane yace, "Baban Narabi ya rasu"?.

"Baban Narabi ya rasu Dr, mun shiga tashin hankali na rasuwar wannan dattijon, wanda bamu wani daÉ—e da shiga cikin jimamin rasuwar shi ba, Allah ya sake aiko mana na Baban Tilde, tsakanin su wata uku daidai, don ko takaba mama kaltum bata fita ba Baban mu ya rasu", tsayawa yayi da labarin, saboda ta'aziyan da Abbu da Dr suka fara yi mishi, kuma da alama Dr yaji rasuwar Baban Narabi ba kaÉ—an ba.

"Humaira nada shekara 10 chif-chif akayi auren Fatima da Dr Hassan", ...... Da sauri Dr Hussain ya É—ago yace, "Hassan yayi aure da Fatima"?

Murmushi Daddy yayi yace, "yanzu auren su shekara shida kenan, don yanzu haka yaran su biyu, Babban cikin ne, Aliyu haidar, inda akace sunan ka yaci, amma suna ƙiranshi da Haidar, ta biyun kuma sunan Ummi taci, amma suna ƙiranta da Nabeeha, yanzu haka suna zaune a garin Abuja, inda Hassan yake aiki achan, kuma yana da chamber shi na kanshi a chan.

Aunty hauwa duk lokacin da tazo nigeria sai tazo tayi kwanaki a wurin Humaira, amma yanzu rabonta da humairah kusan 2yrs kenan, tun zuwanta sunan ƴar su Hassan Nabeeha bata zo ba sai last month, Fatima ma idan tazo tana zuwa ta duba Humaira haka ma Ummin ku, nidai sau kusan biyu nakan ɗauki Humaira muje har misau da bauchi gidan Ummi nakai musu Humaira mu wuni mu dawo, don tana ƙarama sosai ma nakan kaita mu wuni a bauchi mudawo.

Kunji tarihi na da Humairah kenan a taƙaice.

Shikuma Dr a zuciyar shi yana cewa, "lallai Aisha ba so na mata ba, duba da yadda zuciyata gaba ɗaya ya nace akan humaira, gaba ɗaya inajin ban taɓa son wani abu sama da ita ba, idan na rasa yarinyar nan ban san yayah zanyi na dawo dai-dai ba", ya gama magana da zuciyar shi yana kan binta da kallo.

Shawara aka tsayar tsakanin Daddy da Abbu akan dole Dr ya haƙura a je Nigeria wirin Abban shi, domin bazai taɓa yiwuwa a tsayar da magana ba tare da sanin iyayen shi ba, amma firr Dr yace shi bazai koma ba, kuma Humairah ma bazata je wurin Ummin shi ba, idan itama Hassan ya gani yace yana sonta fa?.

Murmushi Daddy yayi yana duban Dr Hussain yace, "amma ashe surukina ɗin ragon namiji ne ban sani ba, har kana tunanin akwai wani da zai iya ɓanɓareka a zuciyar Hummy"?

Girgiza kai Dr yayi jiki a sanyaye yace, "nidai kawai ina tsoron mu koma Abba yace babu aure tsakani na da Humaira ne, ni nafi son ayi auren a nan tukun a koma chan É—in".

Abbu ne ya gyara zama yana murmushi yace, "Haba ɗana! ae idan babu aure tsakanin ka da Humairah ae tun anan ɗin ma baza mu aura maka ita ba, Aisha ae ba ciki ɗaya kuka fito da ita ba, da ace ciki ɗaya kuka fito da Aisha da babu abinda zai sa ka auri Humairah, tou amma yazo da sauƙi akwai aure tsakaninku, saboda haka ya kamata kaje kaga a wani hali da yanayi iyayenka suke bayan tafiyan da kayi na tsawon shekaru, inaga hakan shine yafi zama dai-dai", Abbu ya faɗa yana bubbuga kafaɗan Dr.

Shirye-shiryen tafiyan mu nigeria ne aka shiga fafah, haka muka hallara gaba É—ayan mu sai garin jos, ranan da muka isa mun samu Yayah Kabir ya dawo daga school, oyoyo yaje yayiwa Daddy sannan ya dinga bin kowa yana gaishe su, yana ganina ya É—aga mun hannu kawai ya wuce cikin gida.

Parlourn Daddy duk aka wuce daga nan ni kuma da Ummi da Amaal muka shiga side ɗina, Gaggo nanny na muka samu zaune a parlour tana kallo, da gudu naje inda take na rungumeta, itama babu abinda ta keyi sai murnan ganina, tana cike da mamaki tace, "uwar ɗakina yau kece a ƙasar namu babu notice"? Dariya mukayi dukkan mu dasu Ummi, duk da bawai fahimtar abunda take cewa sukayi ba, sannan na gaya mata tare mukazo da Daddy na da baƙi, jin haka ta fita da sauri tafara haɗa musu abin sha, kafin ta haɗa abinci.

Munayin sallah bayan mun hutu Ummi tace mun muje na kaita ɗakin Mama domin su gaisa, da mamaki na kalli Ummi nace, "Ummi bazafa ta kulaki ba, ko Kaka tazo gidan nan har ta tafi basu kulata ita da su Yayah Ahmad, kada muje ta wulaƙanta ki Ummi nah".

Haka dai Ummi na ta sakani dole muka je side ɗin Mama, duk yadda nasan Mama da baƙin halin kada wani ya raɓe ta idan ba ita da ƴaƴanta ba, amma abin mamaki Ummi ta mata kwarjini haka ta zauna suka gaisa, inda Ummi take gaya mata ni ƙawar ƴarta Amaal ne, hakan Mama ta daure ta nuna jin daɗinta da zuwansu, bamu ƙara wasu lokaci ba muka koma nawa side ɗin.

Waya Daddy yayiwa uncle Abdallah ya sanar mishi da komai daya shafi Dr da Humaira, kuma ya gaya mishi duk mun taho tare, Uncle Abdallah yaji daÉ—in labarin dawowar Dr Hussain, sannan kuma yace a nemi Abba agaya mishi.

Haka Daddy ya ƙira Abba ya gaya mishi labarin komai da kuma zuwan mu, Alƙawari Daddy yayi mishi akan zuwa gobe idan Allahu ya kaimu zai kawo mu har Bauchi.

A washe gari mukaje bauchi gaba ɗayan mu, inda muka samu uncle Auwal, uncle Baba, Aunty Fatima da mijinta Hassan da yaransu duk sunzo su, domin tun a jiyan Ummi ta ƙira kowan su ta gaya musu zuwanmu, hattah su Mama da Addagana da Bappan su Ummi duk sun zo, Umma da yake ta daɗe da dawowa gidan Abba saboda yawan rashin lafiyan da ta keyi kawai sai Abba ya dawo da ita gidan, gefen Aisha aka gyara mata ta zauna a wurin.

Abin tausayi muna shiga parlourn Abba inda gaba ɗayan su suke zaman jiran isowar mu, da gudu Hassan ya taso yazo ya rungume Drn mu, dukkan su kuka suka saka suna rungume da junan su, da ƙyar ya sake Drn mu ya samu ya ƙarasa gaban Ummin ya tsuguna yana kuka baice mata komai ba, ganin haka itama Ummin ta fara kwanɗa mishi pillown kan kujeran tana kuka tana kwaɗa mishi, ganin baxata daina ba Drn mu ya rungumeta yana kuka, itama rungume shu tayi tana faɗin.

"Haba Baba nah! Me na maka haka da zafi na chanchanci ka gujeni irin wannan tsawon shekarun? Katafi kabarni, Aisha ma ta tafi tabarni, da wanne kuke so naji? Kasan zafin rashin Aisha da nayi kuwa? Kasan Aisha ta tafi ta barni bayan bata sake jin yadda dani ba, ta hanani riƙon abinda ta haifa? Kasan zafin rashinka yadda na dinga ji a rayuwata kuwa"? Kuka mai sauti Ummi ta cigaba dayi tana rungume da Drn mu ƙyam a jikinta kaman wani zai ƙwace mata shi.

Abba na murmushi yace, "yau ko naga inda ake mun fir ƙarfi? Farko ɗan'uwan shi ya rigani rungume ɗana, na tashi zanji ɗumin ɗana kuwa wannan matar ta rigani, gashi kuma ta gama chin zalin kyakkyawan fatan ɗan nawa da duka, kuma ta hana ni naje inda yake"? Ya faɗa yana matsawa kusa da Drn mu.

Da sauri Drn mu ya tashi ya rungume Abba yana cigaba da kuka, da ƙyar ya buɗe baki yana, "Abba ku gafarceni tafiyan danayi na barku, Abba kuyi haƙuri bazan sake ba, nayi laifi bazan sake ba".

Jin abinda yake faɗa nayi tsulum nace, "dama ina zaka sake tafiya bayan na chafko ka kadawo gida? ae yanzu zan maka ɗaurin da akeyiwa ragon layyah da karfi bazaka sake tafiya ko'ina ba, amma idan Ummi ta cigaba da kuka kuma zan ɗauke ka mugudu mu ɓuya, tun da nice na nemo ka, bazamu dawo ba har sai Ummi ta daina kukan shagwaɓa", na faɗa ina duban cikin idon Ummi, don kullum nazo gaisheta ko ita tazo ganina ta ringa mun kuka kenan tana tuna Mummy nah, har sai nace mata idan bata daina ba zan daina zuwa wurinta tukun ta daina.

Murmushi Ummi tayi ta jawoni jikinta ta rungume ni ƙam, tana bubbuga baya na tana cewa, "ni Fati naga ta kaina da wannan sarkin surutun, tou yanzu yayah zamuyi ƴace ko jika? Wanne zamu kama ne"?

Gaba ɗaya parlourn dariya aka fara, inda na dubi Ummi nace, "nifah jikace, don gaskiya bazan yadda da wayon nazama ƴaba, amma ita Aunty hauwa saboda masifarta zan yadda ta zama mun kaka, don idan uwace toh ta dinga masifance ni kenan bani da iko da bakin ramawa, amma ke kam naƙi wayon ni jikace, kuma Dr na ma jika zai zama miki gaskiya", na faɗa ina turo mata bakina gaba.

Ranƙwashi na Drn mu yayi yace, "Ummin nawa kike tsagalgalewa"? Dariya dukkan su suka fara inda Aunty fati ta jawo ni jikinta ta rungume tana faɗin, "doughter wato uwar tawa kike cewa mai masifah? Tou bari ta iso zuwa gobe kiga iko da gadaran da zata sauƙe miko, ta hanaki auren ɗanta naga yanda zakiyi kina tsagalgale mana iyayen mu", ........ Tashi nayi da sauri daga jikinta na dubi Uncle Hassan da tunda muka iso yakasa sake wa, saidai idan anyi abu ya share hawaye ya kuma binmu da murmushi, "Uncle Hassan kaji Aunty Fati wai baza a bani babyn baby ba? Uncle kafi kowa kusanci da baby kace mata kabani shi", nafaɗa ina turo bakina gaba.
Chapter 64 · 0% Book details