← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 66

Sashe 47

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Aishan tayi cike da tausayi tace mishi, "wai Daddy ta ke ce maka, halan tana maka kallon Baban ta ne", ta faɗa tana cigaba da share hawayen tan, hararan ta yayi yace, "dama waye idan ba Daddyn ta ba? Ni yarinyar nan ma da wuri zaki yaye ta ki bani ita, don naga baza ki iya kula mun da ita ba", ya faɗa yana miƙawa Aisha hannu ganin ta taho da gudu wurin shi tana buɗe hannu alaman ya ɗauke ta.

Hararan shi Aunty haiwa tayi sannan tace, "Daddyn ta ranan da zai rasu yace ya bawa Ummi ita kyauta duniya da lahira, kuma yace a barta tasha nono sosai, saboda haka ni bazan baka Æ´ata ba, bayan baka da mata, kuma ni bazan yayeta da wuri ba", ta faÉ—a tana share hawayenta.

"Wannan kuma tunaninki na shirme kikeyi, ke zaki hanani auren ne? Zan ɗauki ƴata, don yayah haifa mun yayi ya tafi ya bar ni da ita, kuma bazan barki da ita ba don naga baki san yadda ake renon yara ba, don kema baki wuce rainon ba", ya faɗa yana miƙewa tsaye, dai-dai lokacin indo ta shigo parlourn tace.

"Yayah Abdallah da gaske nima ina zaune a wurin yace yabawa Abban kyautar yarinyar shida Ummi, kuma yace kada a yaye mishi Æ´ar shi da wuri", hararanta yayi yace, "ina wasa dake ne? Nawa Haiwan ta ke da za abarta da yarinya"?.

Tsaki yaja, sannan yayiwa Umma halima sallama sannan ya juya É—auke da Aisha a kafaÉ—an shi, da ta ke tayi musu bye bye.

Suna fita Aunty hauwa ta dubi Umma halima tace, "Umma kinjo abinda ya faɗa ko? Kadafa ya ƙi dawo mun da ƴa ta"? Umma halima tayi murmushi tace, "bai isa ba ae Hauwa, kada ki damu da maganan shi, babu mai ƙwace miki yarinyar yanzu, ae zata zama miki rarrashi ne, yadda Umar yace haka za'ayi, mu koma duk mai son ganinta sai ya bita inda ta ke, shi kuma Abdallah idan yana son riƙonta ae sai ya haɗa gaba ɗaya ya riƙe ku".

"Chabɗi jam, ae Umma halima ni ban taɓa maganan minti goma da shi bama, kullum sai naga kaman kallon banza ma yake mun, shiyasa ma bana shiga shirgin shi, tayaya ma zan zauna a gaban shi bayan ba ɗan'uwa na bane", ta ƙara faɗa tana turo bakinta gaba.

Dariyan da Umma halima bata shiryah ba yazo mata, tana duban Aunty hauwa tace, "hauwa ae yanzu mun zama Æ´an'uwan juna, ae Umar ya haÉ—a mu tun da yabar mana Aisha a tsakanin mu, kuma akwai yanayin da Abdallah zai iya ajiyeki daga ke har Aishan a gidan shi, mu kan ma zamu fi son hakan, amma yanzu tashi ki koma É—aki kici gaba da addu'o'in ki, kada mi shagala ko".

Murmushi Mama tayi tana duban idon Umma halima lokacin da Aunty hauwa ta wuce É—aki tace, "Allah ya amsa mana hakan ae zaifi kawo kwanciyar hankali" umma halima ta juya suka cigaba da zantawa a tsakanin su.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/24, 14:40] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 38📑*

*____________* 📖 Tashi Aunty hauwa tayi zata wuce ɗaki tace wa Umma halima, "hmmm nikan ae bazan iya zama inuwa ɗaya da Abdallah ba, don wani irin son girma ne da shi, kuma bazan bashi Aisha ba don duka zai na mata, fuskan shi babu fara'a ko kaɗan", ta faɗa lokacin data ƙarasa shiga ɗakinta.

Murmushi Umma halima tayi tana jujjuya kanta, "yaro yarone" ta faÉ—a ita kaÉ—ai tana murmushi, a haka Mama ta fito suka ci gaba da hiran su.

Uncle Abdallah lecturer ne a ABU Zaria, yana koyar da English, sannan kuma masters yake da shi, zuwa yanzu yana PHD ɗin shi, kuma ya kusa ƙarasawa, shi mutum ne ɗan bokon gaske, saidai wani halinshi guda ɗaya na ƙin son shiga mutane, shine abun da duk familyn su basu so, domin kafin kaga murmushi a fuskar shi toh sai wani muhimmin abu na gaske, kuma baya shigewa kowa kuma koda mahaifin shi ne, da sun gaisa zaka ga yaja bakinshi ya tsuke, saidai yayita bin mutane da kallo, sau dayawa ma idan kaji muryanshi toh shida Baba Umar ne, amma ya wuce shi bazaka ji bakin shi ba, kullum zaka ganshi da laptop kawai ya na danne dannen shi a ciki, Abdallah kenan.

Rayuwa babu wuya, yau ana saura kwana ɗaya Aunty hauwa tafita a takaba, duk wani a halin gidan Baban Narabi sunzo wuni gidan, duk wanda ka dubi fuskan shi zaka ga yanayi na jimami a tare da shi, zuwa azahar su Ummi da Abba suka ƙaraso Narabi, domin mu an bar mu a chan lagos, gidan abokin Abba aka kaimu, da yamma kuma sai ga Uncle Abdallah ya iso, amma ko kaɗan bai leƙa inda Aunty hauwa ta ke ba, aikowa yayi aka ɗauka mishi Aisha kawai, inda suka san shine yazo, ganin haka Aunty hauwa tafara nuna ɓacin ranta da fargaban kada ya ɗauke Aisha, Ummi ce tayita bata haƙuri tana nuna mata ta kwantar da hankalinta Abdallah bai isa ya ɗauki yarinyar ba bada izinin Baban shi ba, kuma ae bayi da mata ina zaikaita? Haka dai Aunty hauwa ta kwantar da hankalinta.

Washegari Baban Narabi yasaka aka taho da ita chan main house ɗinsu, inda lokacin kuma ƙanin Bappanta da kuma Uncle Auwal sunzo daga misau, a lokacin ne taga limamin garin da wani alƙali da wasu ƴan'uwan Baban Narabi guda biyu, abin tausayi a ranan aka raba gadon Baba Umar kaf, bayan anyi mishi addu'o'i, dukkan ilahirin gidan kuka sukeyi, abin tausayi hattah Baban kasa daurewa yayi, shima kukan ya dinga yi kaman yau aka mishi rasuwan.

Bayan komai ya lafa, Baban Narabi ya danƙa gadon Aisha gaba ɗaya a hannun Abba, sannan ya ɗauki kason shi daya gada ya raba shi kashi uku, ya ɗauki kashi biyu ya ƙarawa Aisha, sannan ya ɗauki kashi ɗaya ya danƙawa Uncle Abdallah yace, "Abdallah wannan dukiyar dana gada ne a wurin ɗan'uwa, amma ina son duk wani abu da zai kai lada kabarin shi kamun da shi, yazamo sadaƙatul jariya wa Umar ɗina", ya ƙarasa yana share hawayen shi, shima Uncle Abdallah sunkuyar da kai yayi yana share hawayen shi.

Baban Narabi hana su Aunty hauwa tafiya yayi a ranan yace su bari sai gobe da safe idan Allah ya kaimu, babu yadda suka iya haka suka kwana a gidan, washe gari da safe motan Uncle Abdallah yazo ya É—auke su har misau, amma bashi ya kaisu ba wani abokin shine, Ummah halima tayi kuka kaman ranan aka mata rasuwan, haka dukkan su Æ´an gidan suka haÉ—a mata da kaya mai É—umbin yawa wai na fita takaba, mazan su da matansu, har da iyayen Aunty suwaiba sun aiko mata kusan kala uku da kaya wa Aisha, uban gayyan kuma akwati guda ya haÉ—awa Aisha, amma ita ko zani É—aya bai mata ba.

Sun koma misau basu fi kwana biyu ba Ummi ta tattara su suka wuce lagos,ta kai kusan wata uku acan aikin ta ya samu a specialist hospital bauchi, lokacin ya zama dole ta yaye Aisha, bayan ta tafi ne kuma Uncle Abdallah yazo ya duba Aisha.

Duk yadda mutane suka so auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah abin yaci tura, don Baban Narabi babu yadda baiyi da uncle Abdallah ba amma sai yace wai ae ita bata ƙiran shi ta gaishe shi, haka Baban zaiyi ta faɗa amma Uncle Abdallah yayi shiru.

Aisha tanada 3yrs mu kuma muna da 8yrs uncle Abdallah yayi aure, inda ya auri wata yarinyar ƴar zaria, student ɗin shi ce, a lokacin ya fara tayar da maganan shifa so yake riƙon Aisha ya dawo hannun shi, ganin haka Abba ya neme shi yayi mishi kacha-kacha, yace mishi koda Baba Umar yana raye tunda yayi mishi alƙawarin ya bashi Aisha, to ko shi bai isa ya karɓi Aisha ba ballantana shi Abdallan, shima Baban Narabi bai ƙyale shi ba, inda Umma Halima da Aunty Amina suka nuna mishi bai kyauta ba, dama ya yadda ya auri hauwa ne toh ko hutu sai Aisha ta dinga zuwan musu, amma bayi da ikon karɓan Aisha a hannun Baba Gambo, haka suka mishi babu daɗi, rai a ɓace ya miƙe yana duban Aunty hadiza da tunda aka fara maganan bata ce uffan ba, ita dai kuka kawai ta keyi, ya dubeta yace, "kin sa mutane a gaba kina ta kuka, toh ni kuma yayah kuke so nayi? Kullum sai kuce wai na auri Hauwa, meye riban auren tan bayan ba bani riƙon ƴar za'ayi ba? Kuma ita kun taɓa ce mata ta aure ni? Kala kusa yarinya ta rainani nace ina sonta", ya faɗa kaman zaiyi kuka.

Hararan shi Aunty Amina tayi sannan tace, "dalilin ka kenan da yasa kaje ka auri wanda ta kusan sa'ar ka? Don wallahi wannan mata taka fadilan tayi kusan sa'ar ka, kuma tunaninka ita hauwan ce yakamata tace tana sonka? Ina ka taɓa ganin anyi haka"?

"Toh ae sai kuce mata kun bata ni bawai ni ayita mun masifan naje na zubar da girmana a gabanta ba, ga shi dama yarinyar ba kunya bane da ita, sai tayi tayiwa mutum kallon sa'anta, ni ko na aure ta wallahi bazan É—auki raini ba a wurinta, gashi ita tana bauchi ni ina zaria yayah za a yi"?

Yana gama faɗin abinda yake ranshi yaja tsaki shi kaɗai, murmushi Umma halima tayi, tana duban shi tace, "tun farko mai yasa baka ce kai girman kai bane yake damunka a ranka, har saida komai ya ƙure tukun zaka nuna mana gaskiyan abinda na daɗe ina ganin zahirin shi a fuskar ka"?, Aunty Amina ta dubi Umma halima tace, "kaman yayah lokaci ya ƙure Umma"?.
Chapter 47 · 0% Book details