Sashe 10
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙura mun ido yayi amma fuskan shi kaman zai yi murmushi, sai kuma ya kanne yace,
"to ke in banda abin ki ta ya ya ina da khadija zan ga kyawun wata? Ni fa banga kyawun da ake cewa kina da shi ba, kawai dai suna son ki ne kuma suna son ki kwantar da hankalin ki ne kawai, shi yasa su ke yaudaran ki".
"Baki na a buÉ—e ina kallon shi kaman na zunduma ihu nace, "Dr Khadijan da gaske matar kace? Kuma kana son ta sosai"?
Tashi ya yi ya tsaya yana gyara rigan shi, alaman kuma zai tafi ne, yana duba na yace,
"idan ta tashi ki gaishe ta, 2:00pm zan zo na É—auke ki muje kiyi lunch".
sannan ya juya zai fita.
Da gudu na bishi har wajen, hannu na saka na juyo da shi da ƙarfi na, idona yana zubar da hawaye nace,
"bana son Dr Khadijan, kuma bata mun kyau, kuma bazan bika lunch É—in ba, babu ruwa na da kai daga yau, munyi faÉ—a Dr'n mu! Munyi faÉ—a Dr na!! Bana....".
Sai kuma nayi shiru ina riƙe da hannun shi ina kuka na.
"To sa ke mun hannu na tafi wurin mai sona, wanda baza ta taɓa fushi da ni ba, wanda ta ke mun kyau sosai, kema ki koma wurin su Peter suyi ta ce miki ke mai kyau ce kinji".
ya faÉ—a yana neman zare hannun shi daga cikin nawa.
"Nima ai banyi fushi da kai ba, ni bana so kaje wurin Dr Khadija ne".
na faɗa lokacin Dr Abdallah yana shirin ƙarasowa in da muke.
Bansan dalila ba kawai sai naji Dr Hussain ya mayar da hannun shi ya sake riƙe nawa hannun, ya saka hannu ɗaya yana share mun hawaye na, murya ƙasa-ƙasa yace,
"mun shirya to, zaki bini muje lunch tare?".
Ɗaga mishi kai nayi alaman na yarda, sai ya yi murmushin da ban taɓa ganin irin shi a fuskar shi ba yace
"to bana son ki kula wancan balaraben Dr, kinga shi bai san ki ba, bai san Daddy'n ki ba, zai iya cutar da ke, tun da shi namiji ne ko? Saboda haka idan kina son mu shirya wataran na gaya miki abinda kike so to kada ki kula shi kin ji?".
Murmushi nima nayi sannan nace, "bazan kula shi ba ko yayi mun magana zan É—aure fuska na".
na faÉ—a ina kwatan ta mishi yadda zan yi da fuskar, wanda abin mamaki sai gani nayi ya tuntsure da dariya, nima cikin mamakin abin da ya yi nima na yi dariyan, sannan na ce,
"Kaima baza kaje wurin Dr Khadija ba yau? Kamun alƙawari ka daina ganin kyawun ta sama da nawa?".
Matse hannu na ya yi da ƙarfi ya na murmushi yace, "bazan je ba yau, sai ranan da naga kin kula Dr nima zan je, kuma ba zan sake shiryawa da ke ba, su Peter ma kawai gaisawa zaku na yi, bana so kina zama da su kuna hira kinji".
ÆŠaga mishi kaina na yi ina murmushi, shima yimun yayi sannan ya sake hannu na ya juya ya fita, ban bar wurin ba har saida na daina ganin shi tukun na koma É—akin.
Ina shiga ya yi dai-dai da Dr Abdallah zai fito a É—akin, Amal kuma ta na zaune an saka mata pillow ta É—an jingina kaÉ—an, gefen ta kuma nurse ce a tsaye tana taimaka mata.
Kallo na ya yi yana murmushi yace,
"Hello Preety"
Hararan shi nayi na ja baki na na yi shiru ban kula shi ba, sai naga ya yi É—an dariya ya juya yana duban Amal,
"Amal friend ɗin ki bata magana ne? Bayan yanzu na ganta a gaban tsohon saurayin ta ta na ta doka murmushi, sai ni ne zata ƙi amsa gaisuwa na?".
Ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin fuskar shi.
"Saurayi na kuma? Dr Hussain É—in ne saurayi na? Baka san yana da mata mai kyau ba zaka ce mun saurayi na, ni kam"....
Sai na rufe baki na tunawa da Dr yace ka da na kula shi.
Amal kallo na ta tsaya tana yi, saboda a ɗan zaman da tayi dani taɗan fahimci wasu daga halaye na, don bani da ɓoye a abu so za kayi saurin fahimta na.
"To idan ba saurayin ki bane mai yasa Dr Abdallah yana miki magana ki ka yi shiru?".
Amal ta gaya mun da muryan ta mai fita a hankali.
Kama baki na yi ina kallon ta sannan nace,
"kema baki da wayo ko Amal? Bakiga Dr Hussain yana da mata ba, ta ya ya za'ayi ya zama saurayi na? Kawai ya hanani kula maza ne saboda kada su cutar da ni, kuma ni bazan sake kula kowa ba".
na faÉ—a ina zama a kan kujeran.
Dariya Dr Abdallah ya yi yana kaÉ—a kanshi ya fita a É—akin.
Amal ma dariya ta ke yi tana kallo na, sannan ta jijjiga kanta ta koma ta kwantar akan pillow tana ta dariyan ta, hararanta nayi na ja tsaki nace,
"kema kina da problem, ta ya ya ma za'ayi na so Dr Hussain? Ni dai kawai burgeni ya keyi, kuma yana mun kyau, gashi yana da class, kinsan ina mai son turare a rayuwa ta".
Dariya Amal ta sake yi sannan tace, "Allah ya nuna mana lokacin".
Nima Aunty Nice ina kallon Amal da alaman tambayan ban fahimci me ta ke nufi da Dr Hussain saurayin Hummy ba ne, amma sai naga tana mun dariya alaman baza ta faÉ—a ba, naje na yi nawa tunanin na gane, kallon Miss Xerks na yi da alaman tambaya, amma sai ta kawar da kanta gefe alaman baza ta ce komai ba, saboda haka readers don Allah ku gaya mun mai kuka fahimta ne?.
*©AUNTY NICE CE*âœðŸ»âœðŸ»âœðŸ»
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
   *1441H/2020M.*
 Â
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONâœ*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
    ```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*ðŸ‡ðŸ¼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICEâœðŸ¼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 7📑*
*__________📖* Tun da muka shigo compound ɗin gidan mu ido na ya sauka a side ɗin Dr Hussain, gaba na sai faɗuwa ya ke yi, domin hango motan shi a parking lot ɗin gidan, wanda daga motan shi ne sai na David, daga dukkan alama sune suke gidan, don nasan Peter ba sosai ya cika zaman gida ba.
Hannun Amal na riƙe, ɗayan hannu na kuma ina riƙe da jakan kayan ta, duk na rasa samun nutsuwa a zuciya ta sai faɗuwar gaba na ke ji, a haka har muka ƙara sa na buɗe ƙofan gidan mu ka shiga.
Muna shiga parlon Amal ta kwanta tana ta ya mutsa fuskan ta, ni kuma na wuce É—aki na kai mata kayan ta, cikin parlor na dawo na zauna a gefen ta ina duban ta da tausayi.
Miƙo ƙafan ta tayi in da na ke ta ce, "don Allah Sister danna mun ƙafa ta, duk ciwo suke mun".
ta faÉ—a kaman zata zubar da hawaye.
Tausayi ta bani na ta shi da sauri na fara daddana mata ƙafafun ta, sai nishi ta ke yi, muna cikin haka wayan ta ya fara ringing, (Ammi na) na gani yana yawo a kan screen ɗin wayan, da sauri na bar abinda na ke na miƙa mata wayan, abin tausayi da ƙyar ta ta shi zaune ta ɗauke wayan, bayan sun ɗanyi magana da Ammin ta, sai Abbun ta ya karɓi wayan shi ma suka yi magana, can sai ta miƙo mun wayan, ina karɓa Abbun ta yace mun,
"Humaira na gode da ɗawainiya ko, idan kin ga jikin zai tsanan ta ki kira number Dr'n ta don Allah, yanzu zan kira shi na sanar mishi, za ki ga Dr Abdallah a contact ɗin ta, duk yadda ake ciki ki sanar mana, mun gode da ƙoƙarin ki, Allah ya miki albarka".
Ina a jiye wayan na dube ta da alaman ta na son yin bacci, a hankali nace, "Sister me zan dafa miki?".
Da ƙyar ta buɗe idon ta, girgiza mun kai ta yi alaman a'a bata son komai, bance mata komai ba na ci gaba da daddana mata ƙafan, har sai da naga bacci ya ɗauke ta, sannan na miƙe naje kitchen na ɗaura faten dankali, sannan na gyara ganye alayyahu mai yawa na ajiye a gefe.
Ina fitowa parlor na ƙura mata ido, ganin bacci ya ɗauke ta babu yadda zanyi na ta she ta ta yi sallah ina tsoron ciwon na ta, ga shi kuma lokacin sallan magrib ya gaba to, haka na wuce ɗaki na ɗauro alwala nayi sallah, bayan na idar da azkhar na wuce kitchen na zuba wadataccen ganye na, sannan na ɗauko apple guda huɗu na wanke su, na yanka na zuba a blander nayi blanding ɗin su, saboda ina ji ana cewa yana amfani a jikin masu ciwon sickler, a fridge na ajiye sannan na sauke abincin na juye a cikin cooler na kai su kan dinning.
Ina fitowa da komai na dawo gefen ta na zauna na ƙura mata ido, har lokacin sallan isha ta yi ba ta ta shi ba, bayan na idar da sallah ne na fito nazo na same ta tana zaune dirshan a ƙasa ta mimmiƙe ƙafan ta a ƙasa tana ta ya mutsa fuskan ta.
Da sauri na ƙaraso in da take ina duban ta nace, "ya fara miki ciwo ne? Ko zaki iya ta shi ki yi sallah?".
Bata ce mun komai ba ta miƙo mun hannu alaman na taimaka mata ta tashi, da sauri na saka hannu na miƙa mata, ta na tashi muka wuce har toilet ɗin ɗaki na, sannan na barta ta shiga ta ɗauro alwala, tana fitowa na shimfiɗa mata sallaya, abin tausayi a zaune tayi sallan kaman za tayi kuka har ta idar.