← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryan Ummi mukaji tana ƙiran Amaal ta zo ta buɗe mata ƙofan, da sauri Amaal ta sauƙa taje ta buɗe ƙofan, wanda nima dole na natashi na zauna ina kallon bakin ƙofan da Ummi zata shigo, riƙo hannun Amaal tayi suka shigo cikin ɗakin a tare, har gefe na Ummi tazo ta zauna, kuma har lokacin idona duka suna zube akan ta, ko ƙiftawa banayi na ƙura mata su don ganin yadda sukayi ja sosai, alaman bayan tafiyan mu taci kuka ba kaɗan ba.

Hankalina gaba ɗaya naji ya tashi, lokacin da Ummi ta saka hannunta ta riƙo nawa kawai sai ta fara kuka mai ratsa zuciya, ganin haka ya saka ni ƙarasawa jikinta na rungumeta, ina kuka nace, "Ummi na mai ya sameki kuma"?.

"Humairah gobe mahaifinki zaizo, inajin tausayin shi bakaɗan ba, kuma inajin tausayinki, zai ga kaman da gangan muka bar ɗan mu zai keta miki daraja, wallahi Humairah ba halin Faisal bane, narasa dalilin da ya saka shi aro wannan ɗaɓi'an, kiyi haƙuri Hummy kada zumuncin mu ya ɓaci, don Allah kiyi haƙuri"? Ta ƙarasa tana mai matuƙar zubar da hawaye.

Jikina a sanyaye na fara share mata hawayen idon ta, "Ummi don Allah kidaina kuka, insha Allahu har abada zumuncin mu yana nan, ni ae ke uwace a gare ni, kuma Faisal yayah nane, kawai yanzu ma sharrin shaiɗan ne ya shige shi, amma insha Allahu zakiga Daddy nah ya fahimci komai, kuma zumuncin mu yana nan Ummi, sai ma abinda ya ƙaro", na ƙara ina kuma jikinta na kwanta ina kukan, wanda Amaal daga inda ta ke a takure itama ta ke nata kukan.

Wannan ranan dai kam mutanen gidan gaba É—aya basuyi bacci mai daÉ—i ba, duk zuciyar kowa babu daÉ—i har asuba tayi.

Wunin ranan gaba ɗaya Dr kin zuwa gidan yayi,dana gajji da rashin shi na ƙira shi amma sai ya nuna mun kanshi ne yake mishi ciwo, amma zuwa dare zai zo.

Haka dai muka wuni sukuku a gidan, kai hattah Faisal ɗin ma sai dana dawo ina tausaya mishi, sbd duk yadda akayi ya shigo gidan ƙi yayi, da aka matsa mishi yazo ayi breakfast sai ce wa yayi ya tashi da azumi, haka kowa ya zauna ranshi da zuciyan shi a dagule.

Daddy sai washegari da asuba jirginsu ya sauƙa, da yake ta sowan dare sukayi, jiki a sanyaye Abbu yaje taryenshi tare da driver, mu kuma aka barmu da haɗa breakfast, na lura Ummi gaba ɗaya a rashin walwala ta ke, ganin haka ya saka na matsa kusa da ita, a hankali na saka hannu na a kafaɗanta cikin hankali na ce mata, "Ummi don Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi ni babu abinda zai raba mu fah, wannan abin mu ɗauke shi a Ƙaddara ne da yazo mana, don Allah Ummi ki kwantar da hankalinki, nasani kina damuwa ko Daddy na zai ƙullace ku ko? Toh ina mai tabbatar miki babu abinda zai faru, don Daddy na mai fahimta ne", ajiyan zuciya
Ummi tayi ta juyo tana duba na cike da damuwa, "Humairah wallahi bana son kuga kaman mun bar Faisal bamu ɗauki wani mataki akai ba, kuma ina tsoron hala Daddyn ki yaƙi tarayyan ku da Amaal, gaskiya Faisal bai kyauta mana ba ko kaɗan", ta ƙaresa faɗi kaman zatayi kuka.

Ƙara shigowan motan su Abbu ne ya saka mu saurin sauƙowa downstairs nida Amaal, da sauri nayi hanyan waje domin taryan Daddy, ina ganin shi da gudu na ƙarasa na faɗa jikin shi, lokaci ɗaya naji hawaye yazo mun, amma don bana son hankalin Daddy ya ƙara tashi sai nayi dabaran dana mayar da shi, ina rungume da shi na ɗaga kaina kawai sai naga Dr na a bayan Daddy yana duba na da murmushi.

Abbu ne yayi gyaran murya da nufin mu karasa parlor, Daddy yana rungume dani a gefen shi muka ƙarasa parlon, gaba ɗaya idon Dr yana kaina kaman zai jawo ni jikinshi.

Haka muka ƙarasa kowa ya nemi wuri ya zauna, Ummi ta fito fuskanta ɗauke da murmushi.

_*JAMA'A DON ALLAH KUMUN HAƘURI WALLAHI YAU MUNA TA BIKI NE, PAGE ƊIN BABU YAWA*_

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/10, 16:43] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 31📑*

*__________📖* Tunda muka zauna nake kwance gefen jikin Daddy nah, amma gaba ɗaya hankali da idon Daddy yana kan Dr Hussain, sai kallon shi yakeyi yana tunanin ina ya taɓa ganin mai irin kamannin shi, haka dai ya haƙura da kallon aka shiga gaisawa.

Abbu sunyi tarya wa Daddy na girmamawa, dole Abbu ya saka Faisal ya zo ya gaida Daddy, Abbu yana kallon Daddy yace, "Alhaji Mohd ko zakaje ka É—an huta ne kafin zuwa dare muyi abinda ya tara mu? don maganan gaskiya ka É—auko gajjiya yakamata ka É—an huta".

"No babu komai Alhaji, idan babu matsalah ya kamata mu tattauna abinda ya kamata", Daddy ya faÉ—a hannunshi É—aya ya na dafe dakai na, amma yawanci idon shi yana kan Dr, wanda gaba É—aya Dr yakasa sakewa.

Cikin mutsuwa Abbu ya lallaɓa Daddy, babu yadda ya iya haka ya haƙura akabar zaman sai anyi sallan ishaa.

Ana idar da sallan ishaa Daddy da Dr Hussain suka iso gidan, da yake Dr yaja Daddy sun tafi hotel ɗin da ya sauƙa, anan sukayi dinner sannan aka taho cikin main parlon gidan aka zazzauna.

Dubawa Abbu yayi yaga babu Faisal, da hanzari ya ɗauki wayan shi ya ƙira shi, babu ɓata lokacin ya shigo duk jikin shi a sanyaye, gefen ƙafan Abbu yaje ya zauna.

Addu'a Abbu yayi ya buÉ—e taron da addu'a, sannan ya karanto wa Daddy duk abinda ya faru daga farkon neman mu da Dr har zuwa case É—inmu da Faisal, da kuma niyyan da Dr yayi na bada labarin shi sai dai yagaywa Daddy, daga nan ya fara neman gafaran Daddy na abinda Faisal yaso aikatawa.

Murmushi Daddy yayi ya dubi Abbu yace, "haba Abbu yanzu don wannan tsautsayin da ya faru ne zai saka kayi fushi da Faisal? Ni ae banga laifin Faisal ba sai naku iyayen shi, abinda yasa kuma ɗaya ne, a wannan rayuwa da muke ciki dole ne fah ka hana yaranka maza zuwa sashin yaranka mata, haka zalika suma ƴaƴan mu mata su daina zuwa gefen yayun su mazaa, koda kowa kai musu saƙo ne, domin masifun da yanzu suka mana yawa a duniyar mu, hadda sakacin mu iyaye, wallahi Alhaji zaka sha mamaki idan kaga yadda fyaɗe yayi yawa a wannan lokacin, kuma abin munin sai kaga mahaifi ne yayiwa ɗiyar shi, ko kuma yayah yayi da ƙanwar shi, ko ƙaninka yayi da ɗiyarka ko ƙanin matar ka, munyi sake da barin yaranmu suna chuɗanya kaman jinsun su ɗaya, haka kuma irin suturun da ƴaƴanmu mata suke sakawa a cikin gida, duk yana contributing lalacewan yaran namu, saboda haka mu iyaye mu gyara kafin mu koma kan ƴaƴanmu".

Daddy ya dawo da kallon shi kan Faisal da yake ta share hawaye yace, "Faisal Amaal da Humairah dukkan su ƙannen kane, tunda Allah ya kiyaye babu abinda ya faru, toh Alhamdulillah, sai dai nace maka don Allah ka ƙara saka tsoron Allah a ranka, kaga nan gaban iyayen kane kayi niyyan aikata haka, toh ina kuma babu idon iyayenka?" Daddy ya daɗe yana mishi nasiha sannan ya neme kowa ma ya yafewa juna kuma muyi ƙoƙarin kula da zumuncin mu, sannan nima da Amaal ya mana namu faɗan akan mudinga kula da shigan da zamu dingayi, daga nan ya dawo da duban shi kan Dr Hussain yana murmushi yace.

"Dr Allah bai sa mun taɓa haɗuwa da kai face to face ba sai yau, duk zumuncin mu through phone muke yi, ashe kuma suruki zaka zama mun ban sani ba", ya ƙarasa faɗi yana murmushi mai kaman dariya, wanda ya nuna tsananin farin cikin Daddy a fuskar shi, kowa da yake cikin parlon saida ya ɗan dara, nidai ban iya darawa ba sai ma ɓoye fuskana da nayi a jikin Daddy, shi kuma Dr ya sake sauƙe idon sho ƙasa.

"Toh Dr Hussain muna saurarenka" cewar Abbu da yake bin Dr da murmushi.

Ƙara tanƙwashe ƙafan shi yayi a ƙasa yana murmushi, kan shi ya ɗago ya kura mun ido yana duba na.

"Alhaji Gambo Aliyu, shi ne mahaifin mu, wanda ya kasance haifeffen garin misau ɗaya daga cikin ƙaramar hukumar Bauchi, misau shi ne asalin garin su mahaifina, sun kasance su uku ne a cikin mahaifansu, yana da yayu guda biyu dukkansu mata, twins ne wato hassana da hussaina, mahaifinmu shi ne Gambon su, wanda sun bashi yakai shekara biyar, bayan an haife sune da shekara biyu suka yi ciwon ƙyanda, idan anan Hassanan Allah yayi mata rasuwa, bayan an haifi mahaifinmu ne suka kasance su biyu kenan a hannun iyayen su, mahaifinsu ɗan kasuwa ne a wancan lokacin, yana kasuwancin shi har zuwa garin jos.

Mahaifina yayi karatu har zuwa matakin digiri, wanda yayi a garin jos inda mahaifinshi yake zuwa kasuwanci, a hannun aminin shi ya da suke kasuwanci da shi ɗan garin Narabi dake jos ya barshi yayi karatu, inda mahaifin mu suka shaƙu da ɗan Baban Narabi mai suna Umar, wanda dukkansu sun kasance masu ilimi sosai.

Goggo Hussaina tayi aurenta a garin misau, amma har zuwa girmanta Allah bai bata haihuwa ba, sai daga baya mijinta ya ƙara aure, inda abokiyar zamantan ta haifi yara kusan huɗu, kuma dukkan su zaka ɗauka Goggo Hussaina ce ta haife su, don tsabar kulawan da ta keyi da su, abin babu wuya Abban mu suna final year a digiri ɗin su Allah yayi rasuwa wa mahaifin su, inda suka shiga cikin tsananin tashin hankali, amma da yake basu da yawa sai Baban Narabi ya ɗauki ɗawainiyar karatun Abba har suka gama.

Abba na lagos aka tura shi service, shi kuma Baba Umar kaduna, haka suka tafi suna kewan junan su.
Chapter 37 · 0% Book details