← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 66

Sashe 31

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya sa ke mun hannu yana sauƙe numfashi kaman wanda yayi gudu, ya juya yana kallon Ummi cike da shagwaɓa yace, "haba mana Ummi!! nifa wallahi bazan cutar da ita ba, kawai ki gane Ummi sonta fah na keyi over", bayan ya saka hannu yana wani dafa ƙirjin shi kaman wanda yake jin wani ciwo a wurin.

Hararan shi cikin so da ƙauna Ummi tayi, sannan ta buɗe mishi hannu alaman ya taho gareta, da sauri yaje ta rungume shi ta wani bubbuga mishi bayan shi kaman wani yaro ƙarami, murya ƙasa-ƙasa ta ke rarrashin shi, "haba fav kasan fa Humairah amana ce a wurin mu, yayah karon farko zaka fara riƙe mata hannu kana jawota jikin ka? Kuma kasan akwai wanda sukayi alƙawarin aure kuma ya maida mu kaman iyayen shi, ae bai kamata mu baka daman ka so ta ba, saboda bazai ji daɗi ba kuma bazai yadda damu ba a gaba, kayi haƙuri farin cikina Allah zai baka wacce tafi Humairah insha Allahu".

bamu jira munji mai zai ce ba Amaal ta jawo hannuna da sauri muka wuce ɗakinta, muna shiga ta fara masifa kaman zata mare ni, "haba Hummy ki zama very careful da ɗan'uwa na domin kada ki bari yaje ya ɗauke hankalinki akan Dr, don wallahi Dr bazai taɓa yafe miki ba, kuma nima zaki sakani jin kunyan shi, don wallahi tsab Faisal zai gama da zuciyar ki acikin kwanaki kaɗan", ta faɗa tana hararana.

Murmushi nayi ina duban ta, a hankali na zauna a kusa da ita na saka hannu na riƙo nata hannun nace, "nikan Amaal kibar tunanin akwai abinda zai ɗauke hankali na akan Dr, ni ina yiwa Dr son da ban taɓa tunanin wata mace tana yiwa wani ɗa namiji ba, kai ko tunanin wani zai ɗauke hankali na akan Dr bana yi, saboda haka ki kwantar da hankali ki besty nah", na faɗa ina bin ta da murmushi.

"Hmmm bazaki fahimta bane, wallahi bros Faisal tsab zai É—auke hankalin ki domin yasan yadda zai nuna miki kulawan da baxaki iya tunawa da wani ba bayan shi, nifa É—an'uwa nane kuma nasan halinshi akan abinda yaga yana so, don ko abu yake so a mishi yasan yadda zai É—auke hankalin su Ummi da Abbu su mishi babu shiri, kedai ki maida hankali kawai, bana son kina bashi haÉ—in kai ko yazo inda kike kinji", ta faÉ—a tana duban cikin ido na.

"Ashe baki sona da alkhairi ko ƴar'uwata? wato kin fi son farin ciki wani bari akaina ko Amaal? toh bana so ki zugata kibarta tayi amfani danata baiwan ta zaɓi wanda yayi mata bawai sai kin mata shishshigi ba", Faisal ya faɗa ya na tahowa inda muke shima ya zauna a kusa dani, sannan ya dawo da hankalin shi kaina.

Yana murmushi ya saka hannun shi ya riƙo nawa, ido na nayi saurin buɗe su a kanshi, amma sai na kasa ce mishi uffan domin yadda naga ya runtse idon shi bayan ya riƙe dukkan hannuna yana ta matsa mun yatsuna a hankali a hanakali, da sauri na dubi Amaal da ta buɗe baki tana kallon ɗan'uwanta.

"Mine kice mun wani abu mana da daddaɗan muryanki hankalina ya kwanta", yana wani langwaɓe mun kaman mai yaron da yake shirin shan nono, murmushi nayi na ɗaga idona ina kallon shi, a hankali na buɗe bakina nace.

_Toh ina team Dr, ku fito kada Faisal ya ƙwace muku Hummy, don jikina ya fara sanyi da al'amarin Faisal, amma bari mujira muji yyh zata kaya a tsakanin su_

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/24, 04:59] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_jin kanta ta ke ta musamman saboda farincikin dake ratsata gata ga Sadauki idanuwan ta raɗau tana kallon kowa. Sadauki ya kasa tantance yanayin da ya ke ciki don bai taɓa shiga irinsa ba. farin-ciki ne ko kuma tausayi? ko dai zuciyar sa ke yaudarar sa akanta?_

_yanzun ma farfesun kifin ta ke ta tsaƙura tana ci tana tunanin ko a wanne hali yanzu ya ke ciki ? kar dai yana cen tare da ƴan iskan mata ? ko kuma yana cen yana shan giya ba, ajjiye hannunta ta yi ta fasa cin kifin hankalin ta amatuƙar tashe. tana son shi, ko ayaya zata iya rayuwa da shi ko da abinda yake aikata wa ya fi haka muni._
_"Jasra kin amince da hakan? kina so na ?" ɗaga kai ta yi tana zabga murmushi. "a a, magana za ki yi." Sadauki ya ce yana jin wani irin ƙwarin gwiwa. "na amince." kasa tsayuwa Madaki ya yi maganarta ta dakar masa zuciya. hakan ya sa ya jinginar da jikinsa da ya ke jinsa tamkar ƙwarangwal saboda tsananin shafal da ya ke jin kansa._
_"kin ga mutumin ki ya zo ko ? yana cen kullum yana tare da mata a gidajen giya kin san garin nan komai na zunubi suna aikata shi, ban san inda ya sauka ba saboda yana tsoron kar na je naga matan da yake mu'amala da su......"._

*ZAIBA! ZAIBA!! ZAIBA!!!* na ƙara ce maku *ZAIBA* ku neme shi ku karanta kar da ku bari a baku labari, rashin karanta shi kuma zai sanya ka yi takaicin hakan.

*SHAFI NA 25📑*

*__________📖* "me kake so kaji? Bayan kasan kai ɗin yaya nane, akwai abinda ya fi shi girma ne a wurina"? na faɗa bayan na xare hannu na daga na shi ina binshi da kyakkyawan murmushi a fuskana.

Juyar da kanshi yayi alaman yayi fushi, "gaskiya ni bazan taɓa amincewa da wannan hukuncin ba, kawai da ne kike ƙanwata da ban ganki ba, amma yanzu nima zuciyata ta amince da miƙa miki ragamar rayuwata, saidai kawai idan baki sona ki fito fili yau ki gaya mun, don bana barin ɗakin nan sai naji abinda ke zuciyar ki game da ni", ya faɗa yana ƙara ɗaura hannun shi saman kafaɗa na, ya kuma ƙura mun idon shi masu masifan haske da kyau akaina.

A hankali na sauƙe a jiyar zuciya, sannan na ɗago ido na na dubi Amaal alamar neman a gajinta,... Tsaki taja ta harare ni, "common my friend ki gaya mishi gaskiyan yadda ya ke a mine ɗinki, kawai kina da wanda kukayi alƙawarin aure da shi, wanda sanadin soyayyan da kike mishi ne muka sako shi a rayuwar ki don ya kawo mana a gaji bawai shima ya dawo yace yana sonki ba", ta faɗa tana wani abu kaman zata zo ta yanka mun mari.

"Don Allah kibar shirmen da kike yi a wurin, idan ba zaki iya zama a wurin ba ki fita ki bamu wuri, so kam zata soni, me zatayi da mutumin da ya kusa haifanta, kuma bai damu da miƙa mata soyayyan shi gaba ɗaya zuwa gareta ba", yana gama hantarar Amaal ya juyo kaina cikin sassauta murya, "plzz mine kiji dani mana".

Ɗaga mishi kaina nayi ba tare da na furta komai ba, sai dai murmushin da bai bar kan fuskana ba nakeyi, "nikan mine ki buɗe baki kimun magana kada zuciyata ta fashe, wallahi ina miki son da zai iya halakani a yau ɗaya, plz kice wani abu mana dear", ya faɗa yana damƙe kafaɗa na da ɗan ƙarfi sosai.

"Na amince muyi soyayyah amma bance maka zan aure ka ba, domin nayi alƙawarin auren Dr", na faɗa ina juyar da idona kan Amaal.

Mtssss taja tsaki ta kalleni cikin ƙanƙance ido, "wallahi sis babu ruwa na nikan baza ki sakani jin kunyan Dr ba, kuma ke kaɗanki kiyi shirin amsan tuhuma a wurin shi, kada ma ki yadda ki sako ni a ciki, amma kin ban mamaki Hummy, ashe akwai wani sauran ɗa namiji da zai ɗau hankalin bayan idon Dr"? Ta faɗa tana bin mu da kallon banza daga ni har Faisal ɗin.

"Get out my friend, ki fita a É—akin nan ki bamu wuri, ke wacce iriyar Æ´ar'uwa ce wanda bata kishin nata É—an'uwan sai wani daban da a sama kika sanshi, kuma kije É—in itama bazata nemi taimakonki ba, shi ma ya sani wannan flower mai kyaun ae bazai zama ta shi bace shi kaÉ—ai, dole muma mu so ta, Allah ya bawa mai rabo sa'a kawai, fita kibani wuri kafin na tashi nazo inda kike yau kiyi kwana hospital".

Kuka Amaal ta fara yi, wanda daga gani na ɓacin raine, tana duban shi tace, "bros don tsabar son kai irin naka na rashin gaskiya shi ne kake fatan ka tashi ka dake ni har nayi kwanan hospital? Wallahi sai na faɗawa Abbu abinda kake shirin yi na rashin amana", sannan ta ƙarasa bakin ƙofan ta riƙe tana kallona tace, "ke kuma idan baki rabu da shi ba sai na gayawa Dr kuma yanzu ma zanje na haɗaki da Ummi, kuma babu ruwa na da ke, bana son ƙawa da ke tunda baki riƙe amana" ta juya ta fita cikin ɓacin rai.

"Bros toh kayi haƙuri mu bar wannan maganan, kaga ran Ameel ɗita ya ɓaci, ina tsoron taje ta gayawa Dr Hussain zaiji haushi na, don Allah kayi haƙuri".

Yana wani murmushin da ba kai ciki ba yace, "bafa zan taɓa haƙuri ba, domin sonki shi ne rayuwata, kina son ganin bana a raye ne"?

Juya kaina nayi alaman a'a, "toh ki bar ni a yadda nake so, mai rabo ya samu cikin mu" ya faÉ—a yana tashi tsaye.

Hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ƙura mun ido bakin shi ɗauke da murmushi, nima ƙura mishi idon nayi domim wani irin kyau Faisal yake mun, ga shi da wani ƙwalisa kaman shi kaɗaine namiji a saudi, murmushi na sakeyi da naga yadda yake wani bina da kallo kaman zai lashe ni, ina kallon yadda yakeyi yasa naji kunya na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsuna.
Chapter 31 · 0% Book details