Sashe 2
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dafa kafaɗa na tayi muka tsaya dai-dai lokacin da ta tsayar mana da taxi, BAILEN, CARRER DE ta faɗawa mai taxi ɗin sunan unguwan da take, nima na gaya mishi inda nake, saboda ni nafita kusa da school ɗin, haka muka shiga har inda nake na sauƙa ita kuma ta wuce.
Ina ƙarasowa gidan da nake wanda gida huɗu ne a compound ɗin gidan, wanda yake kusa danawa ban taɓa ganin an buɗe gidan ba, sai biyun da suke gaban namu suma wasu students ne a ciki amma dukan su maza ne, ina ƙarasowa wanda muke haɗe da shi naga yau alaman akwai mutane a gidan don ina zuwa kusa da wurin naji ƙamshin kaman ana soya ƙwai, har cikin zuciyata naji daɗi domin ina tunanin ko macece a gidan nima na samu wacce zatana tayani hira wani lokacin.
Naso ace naga wanda take gidan amma har na shiga gida na ban ga kowa ba, ina shiga direct toilet na shige na ɗan watsa ruwa, riga dai-dai gwiwa na nasaka domin na samu sakewa na ɗan taɓa karatu, ina shiga kitchen naji nayi missing Daddy da yanzu har ya dafa mana abinci, amma yanzu gashi yunwa na keji kuma ina jin lalacin dafa komai, KunKumi na na riƙe ina hararan kitchen ɗin kaman shi ya haɗa ni da yunwan, zuwa can na juya na koma parlon na zauna akan dinning ina ta tunani.
Kaman an zabure ni na miƙe na shige kitchen ɗin da sauri, egg guda uku na ɗauko na fasa na fara soyawa saboda na tuna ita ma neighbor nah ma shi naji tana soyawa, ni kaɗai na fara murmushi a zuciyata ina cewa Allah kasa macece a gidan.
Bayan na gama na dawo parlor na sauƙa akan ƙwaina gefe ɗaya kuma na haɗa cornflakes ina sha, ko cin rabi banyi ba naji ana nocking ƙofa na, dariya naji ya ɗan suɓuce mun a fuskana, a zuciyata nace hala neighbor na taji na dawo shine ta zo duba ni, sai kawai nayi tsalle na miƙe, ko duba kayan jikina banyi ba saboda murna da ɗaukin zuwa ganin neighbor.
Ina buɗe ƙofan sai naji da ƙaran buɗe ƙofan da bugawan zuciyata sunyi a lokaci ɗaya, da ƙarfi na rike ƙofan don kada na faɗi, idona kuma a zare kaman zasu zazzago ƙasa, kuma alokaci ɗaya naji na kasa rufe bakina dana buɗe zanyi magana.
Haka zalika shima a gefen shi ba ƙaramin faɗuwar gaba da gigita yayi ba, domin bai taɓa tsammanin ganina ba, domin yayi tunanin namiji ne a gidan don last week kaman namiji yagani ya fito ya daɗe tsaye a ƙofan gidan, shi kuma tun ranan Allah bai nufa ya dawo gidan ba sai yau.
Sake juya idon shi yayi yana Ƙara zuba mata ido kuma zuciyar shi tana harbawa kaman zata faɗo ƙasa, kaddai wannan yarinyar da yaji muryanta sak ina na *AISHA* ce a gaban shi, yarinyar da tunda yaji muryanta ɗaxu faɗuwar gaba yaƙi barin shi da wani irin mummunan tsoro a zuciyar shi, duk da ɗazu bai kalli fuskarta sosai ba, kawai muryanta da tsarin maganan ta babu maraba dana Aishan.
saidai zuwa yanzu duk ta kunce mishi notinan kanshi daya ga hattah zaro idonta da ɗan bakinta data buɗe kaman na Aisha, kai shi idan ba karya yake so yayi wa zuciyar shi ba sai yaga hatta fuskan kaman na Aisha aka maka mata, sannnan kuma tsayin ta ma kaman na Aishan ne, ba zuciyar shi ba yau yana ji hatta huhunshi ma kaɗawa suke yi, yau wani irin gamu yayi? Shiyasa tunda tayi mishi magana yaƙi yabar kanshi ya dubi fuskanta ɗazu.
"Dr mu kai...ne...a..nan...wurin?" Lokaci É—aya ta samu kanta dayin in'inan da bata san ko tana yi ba ko yanzu ne ya zo mata.
Shi dai bai ce mata komai ba sai kaÉ—uwan da zuciyar shi ta sake yi don jin yadda tace mi shi wai, "Dr mu".
innalillahi ya furta a zuciyar shi, kaddai Aisha ce tazo har inda yake? Wato duniyan ƙaramar wuri ne ko? Duk inda kaje sai an tarar da kai? A hankali ya buɗe baki yana kallonta yace," *AISHA*"
Zaro ido Humairah tayi da sauri tana duban shi cikin mamaki, sannan tace, "lahhh kaima Aisha kake son ƙirana da shi? Kasan kakana ne kawai suke ce mun Aisha, Daddy yace mun duk ranan da yace mun Aisha sai ya wuni bashi da lafiya, dama kasanni ne? Shiyasa ɗazu dana baka haƙuri sai kaima kamun uzuri a rayuwa ko? Don kasan laifin da mutum zai yi a farko yaka mata ana mishi uzuri, idan ya sake kuma sai ace gangancine ko kuma da son ran shi yayi, ta ƙarisa maganan tana mishi murmushi, wanda lokaci ɗaya yaji faɗuwar gaban shi ya ƙaru, wanda baisan ya dafa jikin bangon gidan da ƙarfi ya furta.
"Aisha ya ya kike bina kuma a rayuwa ta, meye ya saura kuma? Bana ce......".
sai kuma ya rufe bakin shi da hannun shi da ƙarfi, ya kifa kan shi a kan hannun shi ɗayan daya dafa bangon yana mai runtse idon shi, a hankali yana bawa kanshi haƙuri yana gayawa kan shi ba zai taɓa yiwuwa Aisha ta zauna yadda take kaman daba, bayan yanzu rabon shi da ita ya kai 18yrs, wannan da take gaban shi kuma bazata wuce 16yrs zuwa 17yrs ba. Ya kamata zuwa yanzu ace Aisha ta kai 35yrs, tunda shi dai yanzu yana 39 zuwa 40yrs.
Sake É—ago idon shi yayi yana kallonta wanda ita ma zuwa lokacin ta fara tsorata da yanayin da taga ya shiga, tana bin shi da kallo cikin damuwa tace, "Dr mu baka da lafiya ne? Na baka paracetamol?".
Juyawa yayi da sauri yayi hanyan gidan shi, duk illahirin jikin shi kuma yana rawa, wannan wani irin kamane tayi da Aisha hatta yanayin yarintar su da shagwaɓar su iri ɗaya ne, idan bai manta ba babu hali da ya zaina yayi shiru za kaji Aisha tana cewa,
"na kawo maka paracetamol? Wato É—abi'un suma É—aya ne, to ko dai ita ce? A haka har ya wuce gidan shi ya rufe kanshi, sannan ya runtse idon shi bayan ya faÉ—a kan gadon shi.
Humairah tana tsaye har saida ta daina ganin shi tukun ta koma nata parlon ta zauna, sai da ta daÉ—e idonta yana kallon abincin tana tunanin meye ya samu mutumin nan? Can taji kan ta ba zai É—auki tunanin ba kawai sai ta share ta cigaba da cin abincinta.
Har ranan friday Humaira bata sake ganin Dr ba a cikin compound ɗin su, ko alaman ana zama a gidan ba taga anayi ba, kawai sai tayi tunanin ko yana tafiya wurin familyn shine, don bata jin motsin mata ko yara a gidan, can kuma ta saka hannun ta da riƙe haɓanta kaman mai tunani zuwa can sai tayi dariya tace yes hakane ma tunanina dai-dai ne, wato matar shi da yaran shi suna wani gida, may be matar shi tana aiki a wani wurin ne shiya sa ya barta da yaran shi, shi kuma nan yafi kusa mishi da school ɗin da yake aiki, wataran ya zauna anan wataran ya koma wurinta, sai tayi tsalle ta jinjinawa kanta tana dariya irin tunaninta dai-dai yake.
Ranan friday suna da Dr Hussain a 8:00 to 9:30, tun 7:30 suka shiga class, don duk Æ´an class É—in suna tsoron Dr Hussain, suna zama class reps ya tashi yace,
"duk ku kashe wayoyin ku gudun abinda ya faru ran monday".
kaman ance na bar wayana a kashe sai duk aka juya ana kallona, murguÉ—a musu baki nayi na juyar da kaina gefe, dai-dai lokacin da ya shigo class É—in, sai kaji kaman babu sauran wasu halittu masu numfashi a class É—in duk an É—auke wuta.
Yafi minti uku a tsaye yana duban books ɗin da suke hannun shi, ba tare da ya dubi kowa ba, can ya rufe ya fara musu lectures yana yi yana ɗan zaga class ɗin, wanda bai taɓa musu haka ba sai ranan, yana zuwa dai-dai inda Humairah take zaune ya tsaya ya cigaba da bayanin shi yana tsaye a wurin, can ya miƙa mata hannu alaman ta bashi abu.
Duk sai taji ta ruɗe ta waiwaya ta dubi class ɗin taga kowa ita yake kallo, haka shima Dr idon shi yana kanta ya ƙura mata su, batare daya daina bayanin da yake mata ba, a hankali ta nuna mishi bata fahimci mai yake nufi ba, abinda bai taɓa yiba yayi shine ya saka hannu ya buɗe handbag ɗinta ya ɗauko wayanta ya duba yaga a kashe yake, amma duk da haka bai maida mata ba, sai kawai ya jefa a aljihun shi, ya wuce gaban class ɗin inda yake tsayuwa da.
A haka yayi musu lecture har ya gama ya fita, kuma ko tunanin ya miƙa mata wayan bai yi ba kawai fitan shi yayi, ita ma ba tayi wani yunƙurin tashi ba ballantana ta nemi ya bata.
yana fita Amal ta dube ta tace, "Hummy yaya baki karɓi phone ɗinki ba"?
Juya ido tayi cikin yanga da yabi jikinta tace, "idan yana so zai bani ai, ba lallai sai na bishi ba".
Amal ta sake cewa, "yaufa friday ne Hummy, kinga sai monday ne fa ya dawo class É—innan, zaki iya zama babu wayan?".
"idan bai bani ba yaya zanyi Amal?".
Kowa class É—in da abinda yake faÉ—i, can uwar rawan kai ta taso jiki na rawa ta zo wurin su ta zauna tana cewa,
"Humairah yaya me yake faruwa ne?".
Humairah ta juya idon ta kaman mai jin bacci tace,
"me yasa kuke damun kan ku ne?".
Sai ta juya tana buɗe book ɗin da yake gaban ta ba tare data ce komai ba, ganin ba zata ce komai ba sai kowa ya ƙunshe guntun gulman shi yayi shiru, har wanda yake ɗaukan su Eng ltr ya shigo.
Har na kai yamma banga alaman Dr a compound ɗin gidan mu ba, duk damuwata yau friday kada Daddy ya ƙirani yaji wayan a kashe ko kuma a hannun wani, nasan Daddy ba zai ji daɗi ba.