← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 66

Sashe 60

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hussain kaine sanyi idanuna, wannan key na gidana da yake sir kashim road ne na baka shi duniya da lahira, dama na gayawa duk wanda ya kamata su sani, nabawa Ummin ka ɗayan key ɗin wanda tace zuwa gobe zasije suyi jere wa Aisha, wannan kuma nakane, Hussain Allah yayiwa rayuwarka albarka, Allah yasa duk inda kasanya ƙafanka kashiga kaga haske da rufin asiri a rayuwarka, Hussain yadda ka faranta mun ina roƙon Allah yabaka yaran da zasu maka sama da yadda kamun, Hussain duk wani abu da kamun daga ranan haihuwarka har zuwa yanzu har zuwa ƙarshen rayuwarka na yafe maka shi duniya da lahira", duk sai naji kaman nafasa ƙudirina, amma ina bazan iya rayuwa da matar da ɗan'uwa na ya kusance taba, har abada bazan samu nutsuwa da ita ba, rasa abinda zanyi nayi, kawai sai naje na rungume shi na fashe da kuka, abin mamaki duk dauriya da ƙarfin halin Abba, amma sai kawai naji shi yana kuka kaman mace, wanda nayi imani da Allah tunda abin nan ya faru bai samu ya cire abin a ranshi ba sai yau, saboda haka barin shi nayi yayi iya son ranshi, wurin ƙarfe tara na mishi sallama nace zan duba Ummi ne, da ƙyar Abba ya barni nabar parlourn kaman wanda yasan abunda yake mine ɗina.

A zaune a bakin gadonta na sameta tana zuba wasu Æ´an kunnaye a cikin kid É—inta, ganina ya saka tayi murmushi, nima maida mata martanin murmushin nayi, a hankali na karasa inda take, hannu na saka na matsar da kid É—in na zauna a gefenta, ita ma hannu ta saka ta maida kaina kan kafaÉ—anta.

"Ummi nah!" na faɗa bayan na kwantar da kaina da kyau a jikinta, "Autana!" itama ta faɗa tana shafa kaina, da sauri na ɗago da kaina muka ƙurawa juna ido, daga nan mukayi dariya wa junan mu, domin idan taso raha takance mun yayan auta, yau kuma ta ƙirani da autan, wato ta tabbatar yanzu ni autan tane.

Murya a hankali nace, "Ummi na ina sonki, kuma bana son na dinga ganin tears a fuskar ki, ummi bana son na dinga ganin wani ya ɓata miki rai ballantana ni da kaina, Ummi duk abinda na miki daga ranan da kika haifeni ki yafe mun".

Shafa kaina ta dinga yi a hankali, chan kuma sai naji muryanta tana cewa, "Alhussain, wallahi tun daga haihuwarka har ka koma ga mahalicci na yafe maka duniya da lahira, ina roƙan Allah ya haska rayuwarku kaida ɗan'uwanka, Allah ya kare mun gabanku da bayanku, duk inda kuke a duniya Allah ya tsare mun ku", shiru tayi na wani ɗan lokacin sannan ta cigaba da cewa.

"Hussain damuwa ɗayane, me hauwa zataji a zuciyarya? Na hanata xama da ƴarta, na hanata nunawa ƴarta ita ta haifeta, a ƙarshe kuma ga abinda ɗana yayiwa ƴarta, shin haiwa zata iya mantawa da wannan al'amari kuwa? Kullum sai nayi kukan abinda ya faru, ga tsananin kunyar Aisha da nakeji, domin bansan da wani ido Aisha zata dinga dubana da shiba, gashi tun ranan har zuwa yau ta kasa dogon magana da ni, iyakarta gaisuwa shima ba kullum ba Hussain", Ummi ta ƙarasa faɗi tana kuka.

Hakan Nayita kwantar wa Ummi nah da hankali kuma na mata alƙawarin zan fahimtar da Aisha komai, amma nafi son Ummin ta kwantar da hankalinta tukun, haka mukayi ta hira har nagaya mata kyautar da Abba ya bani na gida, amma murmushi tayi tace ya gaya mata, hannu na saka a aljihuna na fito da key ɗin na miƙa mata nace ta riƙe mun idan zanje gidan zanzo na karɓi key ɗin, babu wani tunanin komai ta karɓi key ɗin, wurin 11:00 na dare mukayi sallama da ita na fita a ɗakin.

Ɗakin Aisha na wuce, inda na sameta suna shirin kwanciya ita da Mama da Umma, bayan mun gaisa dasu nacewa Aishan tazo parlourn ta same ni, na zauna banfi minti 2 ba ta fito da zunbulelen hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta gaisheni, sai naji wani tausayinta kaman na fashe da kuka, a lokacin naji haushin Hassan ya mamaye zuciyata, ban san lokacin da na furta "Allah ya isa tsakanina da kai Hassan", da sauri Aisha ta ɗago idonta ta dubeni, sannan tayi ƙasa da kanta tace Yayah kana kishi a kaina ne? Kana sonane yayah?" duban ta nayi a zuciyata nace wato Aisha har gobe babu abinda ta keso sama da na furta mata ina sonta ko? Murmushi nayi na dubeta a hankali nace, "meye riban idan nace ina sonki bayan wani ya rigani furta yana sonki"?.

Murmushi tayi tace, "Yayah aiko raina ne yake shirin fita babu abinda zan so irin naji kalmar ka kace, "Aisha ina sonki, toh bansan da wani farin ciki zan koma ga mahaliccina ba, domin nayi imani da Allah ko ajiye mu gida ɗaya akayi da kai bazaka taɓa aikata mun irin cin amanan da Hassan yayi mun ba", ta ƙarasa faɗi tana share hawayenta.

"Aisha ina sonki! Ina sonki!! Ina sonki!!! Amma kinsaka jikina yana sanyi da ke saboda naga kaman kina fushi da Ummi na, wanda gaba ɗaya kin saka ta daina walwala damu irin nada, Aishan mu banji daɗi ba", na ƙarasa ina jijjiga kaina.

Matsuwa tayi da rarrafe har kusa da ƙafana fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Yayah nah ko yau Allah ya ɗauki raina burina ya cika, mutumin da na rayu da son shi ya furta mun yana sona sau uku, nagode yayah nah! Nagode yayah nah!! Ummi kuma wallahi tausayinta ne yake saka ni kasa sakewa da ita, saboda Ummi ta nuna mun so sama da abinda ta haifa, amma ɗanta yazo ya cutar dani, shiyasa kullum na dubeta sai naga damuwan abun a kwance a fuskarta, ni kuma sai naji banji daɗiba, kuma ina samun rashin nutsuwa idan na ganta a haka, yayahn mu kuma ni bana so ace Aunty hauwa ce mamana, nafi son Ummin," ta faɗa tana turo bakinta gaba zatayi kuka.

Murmushi nayi ina dubanta nace, "tou idan da ba Aunty hauwa bace ta taimaka ta haife ki tou yayah kike tunanin zan furta miki ina sonki"? BuÉ—e baki tayi tana kare hannunta akai, dariya tayi tace, "nafi son Ummi ta haife ni, ku kuma Auntyn Hauwan".

Dariya nayi nace, "tou mun yarda daga yau kece Æ´ar Ummi mu kuma Aunty hauwa, saboda haka tashi muje muyiwa Ummi albishir ko zata samu yau tayi bacci mai daÉ—i".

Sallama mukayi muka buÉ—e É—akin Ummin, lokacin ta fito daga toilet daga gani alwalah ta É—auro, da gudu Aisha taje ta rungumeta tana dariyanta irin na da tace, "Ummi mun yarda nida yayah na, daga yau kice kika haifeni ni kaÉ—aina, su kuma Aunty hauwa ce maman su, kinga an raba ko Ummi? Kuma kullum ni kaÉ—ai zakiyi taso".

Murmushi Ummi tayi tana duba na kaman tazo ta goyani ta keji, a hankali tace, "Allah yayi muku albarka, tabbas na yadda ki kaÉ—aice Æ´ata, kai kuma hussain kaxama surukina saboda haka fita kabawa uwa da Æ´arta wuri zasuyi shawara", dariya dukkansu sukayi wanda nima sai da suka sakani nayi bayan hawaye ya cika mun ido, ina dubansu da yadda suka manne da junan su, sai naji kaman kada na tafi na barsu, domin nasan yanzu abu mafi tashin hankali da zasu shiga shine rashina kusa da su, amma kuwa bazan iya buÉ—e baki nace bazan iya auren Aisha ba, saboda Hassan, kuma bazan iya auren ta ina tunanin Hassan ne yafara kusantar ta kafin ni ba, haka na É—aga musu hannu alaman bye-bye, na juya zan fita.

"Yayah mu!" naji muryan Aisha a hankali ta ƙirani, a hankali na share hawayena na juyo ina duban su, "Yayan mu yau a ɗakin Ummina zan kwana, saboda haka kada kamana sammakon zuwa da sassafe, kabar mu sai mun neme ka", ta ƙarasa tana rungume Ummi, ni kuma kasa ce mata komai nayi tsabar tausayinta, murmushi kawai nayi na juya na fita.

Ƙiran sallah asuba ya tashe ni, da wuri naja jaka na wanda kaya na basu da yawa a ciki, saidai dukkan credentials ɗina suna ciki, ɗakin Hassan na buɗe na ganshi a dunƙule yana jin sanyin Ac, rage AC nayi na dube shi na share hawayena, sannan naja ƙofan na fita, ina zuwa ƙofar gate naga bangies mai achaɓa, hawa nayi mukayi gaba dashi.

*BARCELONA*
Shine inda ya mun na taho, saboda nan ne inda na tabbatar su Abba baza suyi tunanin zuwa na ba, duk da lettern dana bawa bangies nace yabawa Abba nah, nagaya mishi dalilin tafiyana, kuma na basu tabbacin kada ma su fara nema na, don nayi nisa kada su wahalar da kansu.

Yana zuwa nan ya ɗago da idon shi da sukayi jaa ya ƙura man shi, nima share hawayena nayi ina duban Daddy da naga shima hawaye yake tayi babu ƙaƙƙautawa, a zuciyana ina jin tausayin Dr nah babu adadi, duk da chan ƙasar zuciyata inajin zafin Aishan tunda ya taɓa furta mata kalmar so, wato ya taɓa son wata kafin ni kenan.

Daga nan Dr Hussain ya cigaba da bawa su Daddy labarin haɗuwar shi dani a school da irin alƙawarin da mukayi wa junan mu, ya basu labarin har zuwa tahowa na saudi.

"Ikon Allah Daddy ya furta da ƙarfi yana duban Dr yace, *ƘADDARA TA RIGA FATA* shine labarin ka kam Dr, toh yanzu ma jikina yana bani akwai aure kuwa tsakaninka da Hummy? Gaskiya ina tantama Dr" Daddy ya faɗa yana share wani hawayen.

Da sauri Abbu ya ɗago yana duban Daddy yace, "kasan shine? Kuma kasan wani alaƙa ne tsakanin shi da Hummyn"? Duk a firgice Abbu ya jeho da tambayoyin wa Daddy.

Shima Dr a razane yake duban Daddyn, yana kuma jira yaji me Daddyn zaice.

"Kunsan danganta kar dake tsakanin Hummy da Aisha da kuma Hassan ne"?

_TOH MAKARANTA KARATUN ƘADDARA TA TIGA FATA KU KASANCE DANI A SHAFI NA GABA DOMIN JIN ME ZATA KASAN CE, MEYE KUMA DANGANTA KAR HUMMY DA HASSAN DA KUMA AISHA, NIDAI BAZAN FASA SANAR DAKU DUNAN BOOK ƊIN BA, *ƘADDARA TA RIGA FATA*_
Chapter 60 · 0% Book details