← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 66

Sashe 38

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan 1yr suka gama suka dawo jos, babu ɓata lokaci Baban Narabi ya tsaya kai da ƙafa har saida ya nema musu aiki, inda Abba ya samu aiki da Central Bank, shi kuma Baba Umar ya samu aiki da Custome.

Zuwa wani lokaci komai ya fara musu daidai, sun fara fin ƙarfin komai, sai Abba ya fara neman auren wata yarinya a garin misau, ana shirin auren su Allah yayi mata rasuwa, gaba ɗaya Abba ya shiga cikin wani irin tashin hankali, har sai da yafara kasa aikin shi, ganin haka mahaifiyar shi Umman Misau ta nemi shawaran Goggo Hussaina akan ko zasu bashi auren babbar ƴarsu da yanzu ta gama secondry school a wannan shekaran mai suna *FATIMA* babu ɓata lokaci Goggo Hussaina ta amince kuma ta bar maganan zata je tayi shawara da iyayen yarinyar, basu wani ja ba dukkansu suka amince inda mijin Goggo Hussaina Alhaji Abubakar dama ya kasanceai matuƙar haƙuri magana ma nan baza kaji shi yana yi ba, malamin gidan gona ne, idan baya wurin aiki toh kullum yana ƙofan masallacin unguwar su da yake manne da gidan shi yana zaune, jama'a da dama suna mutunta shi da halinshi na dattaku, itama mahaifiyar Fatima wato Aishatu itama ba mai magana bace, ta kasance bafulatanan garin gabɗori, duk wanda yasan garin misau ya san gabɗori garin wasu farare kyawawan fulani ne a wurin, gashi ta kasance mai haƙuri da kawaici, ana ƙiranta da suna Addagana, tun ranan da malam Abubakar ya aureta babu wanda zai ce ya taɓa jin tsakaninta da mijinta ko abokiyar zamanta Goggo Hussaina, kuma ta ɗauki iyayen Goggo Hussaina kaman nata iyayen, domin ita ta kasance marainiya ce, babu uwa babu uba, kuma ƴan uwanta sun mata riƙon wahala, toh da ta samu Gogho Hussaina irin mutanen nan ne masu amana da maida ɗan wani nasu, sai ta rungumeta suka zama kaman ƴan'uwa ba kishiyoyi ba, suma iyayen Goggo Hussaina sai suka riƙeta kamar ƴa.

Lokacin da ta haifi Fatima bata cika shekara ba ta samu cikin ɗanta na biyu, dole Goggo Hussaina ta karɓi riƙon Fati ya dawo hannunta, bayan Addagana ta haihu, an samu Muhd Auwal, ko shekara baiyiba sai ga wani cikin a jikin Addagana, haka Goggo Hussaina ta sake karɓan shi ta haɗa da fatima ta riƙe shi, yana da shekara ɗaya da ƴan watanni Adda gana ta haihi ɗanta namiji inda Malam Abubakar yayi kara ya saka sunan mahaifin su goggo hussaina wato malam musa, amma suna ƙiran shi da Baba, Addagana wanannan karon bata sake haihuba, don tayi ɓari kusan sau biyu kuma ta haihu kusan sau uku suna komawa, ba ita ta sake haihuwa ba har saida Fatima ta kai shekara goma sha uku, Auwal yana da shekara gima sha biyu, Baba kuma yana da shekara goma da rabi, sai lokacin ta haifi *HAUWA*

Fatima da hauwa sun kasance suna tsananin kama da mahaifiyar su, domin kana ganin farinsu da gashin su babu abinda suka bari na Addagana, Auwal kuma da Baba duk mahaifinsu suka É—auka, duk da suma farare ne amma basu yi kyaun su Fatima ba.

Fatima da ƙannenta sun kasance yara masu tarbiya da nutsuwa, domin Goggo Husaina babu abinda ta bari daga tarbiyan su, ta riƙe su kaman ita ta haife su, babi wani mugunta a tarbiyanta, sai kuma yaran suke sonta kaman itace mahaifiyar su, Baba ne kawai wani lokacin sai ya koma ɗakin Addagana, idan sun ɓata kuma ya tattaro ya dawo ɗakin goggo hussaina, kowa zaka ga yana mishi dariya, akan yarasa wurin zama guda ɗaya.

Lokacin da aka gayawa Abban mu maganan auren shi da Fatima bai wani ja ba ya amince, amma ita Fatima sai da tayi ƙorafin ita fa kawun tane kawu Gambo, amma da taga ran Yayah zai ɓaci sai ta amince, da yake haka suke ƙiran Goggo
Hussaina, don duk sunbi bakin Addagana ne.

Ba'a É—auki lokaci ba akayi auren Abba da Ummi nah, aka kaita garin bauchi inda Abba na yake aiki, sun zauna a wani unguwa wai shi dutsin tanshi, gida ne É—an madaidaici ma É—akuna biyu, sai kitchen da wani É—an store, babu laifi gidan ya dace da sabbin ma'aurata.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/11, 11:08] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 32📑*

*__________📖* Abba na da Ummi na suna cika shekara uku da aure Allah ya basu mu, inda aka same mu nida ɗan'uwa na Hassan, daga lokacin Allah yayita buɗi wa Abban mu, inda aka maida shi branch ɗinsu na lagos, babu ɓata lokaci muka tattara tare da Aunty Hauwa muka koma chan, ita kuma tana taimaka wa Ummin mu da wasu ƴan aikace aikace, inada a lokacin tana tayata har renon mu don bamu fi six month ba, ita kuma Aunty hauwa tana 14yrs kuma zata shiga ss 2 a lokacin, haka Abba ya sama mata wani private school kusa damu ta shiga.

Muna cika 2yrs Aunty hauwa ta gama rubuta waec É—inta, murna kaman zatayi yayah, haka muka É—unguma muka taho Misau mukayi hutu.

A wannan hutun ne Baba Umar yayi aure da wata yarinya ƴar tilden fulani, ƙanwar matar abokin shi ce mai suna suwaiba, shi kuma a wannan lokacin yana katsina da zama.

Result ɗin su Aunty hauwa na fitowa Ummi suka yi shawara da Abba akan a sama mata school of nursing bauchi, haka Abba yayita fafutukan nema har Allah ya yarda da rabonta a ciki, tafiyan ta ummi taji babu daɗi, domin Aunty Hauwa akwai kazar-kazar ɗin aiki, saidai akwai yawan faɗa, wanda kullum akace ta ɗauki Hassan sai ta zungure shi tayita mitan ya cika yawan kuka, amma idan Ummi zatayi aiki tafi so ta bata riƙon shi, don aikin zai fi tafiya mat, domin ni duk inda akayi dani haka nakeyi bana da rikici inji Ummin mu, shi yasa ita bata damu ta ɗaga hankalinta akaina ba, sai dai kullum rikicin Hassan ke rikota su dukkan su gidan.

Aunty hauwa tana 2yrs a school of nursing, taxo mana hutu lokacin muna 4yrs, a lokacin kuma Baba Umar an dawo da su Lagos, ranan da tazo Abban mu tare da Baba Umar suka je ɗaukota a airpot, tunda Baba Umar ya ganta hankalin shi yayi mugun tashi, sai tambayan Abba ya keyi "yaushe Hauwa ta girma haka? Kaga fa yadda ta koma kaman Fatima sak, har ma tafi Fatima tsayi da fari wallahi", ya faɗa yana duban Abba da ya ƙura mishi ido.

Murmushi Abba yayi mishi yana duban Aunty Hauwa ta mirror yadda duk ta kasa sakewa sai wani kunya ta keji kaman ta nutse a ƙasa, yana ɗan dariya yace, "haba Umar duba dai da kyau ka gani, ta ina Hauwa ta kai Fatima kyau? Tsayi kuma don ita yanzu yarinyace batayi jiki ba, amma Fatima nah tafi komai, wannan da wani hancinta da baikai na matata kyau ba", ya ƙarasa yana dariya domin ganin yadda Aunty Hauwa tayi saurin ɗago idon ta tana kallon shi da mamaki, chan kuma ta saka hannunta ta shafa hancin ta, muryah cike da shagwaɓa tace, "yayah da Bappan mu sunce nafi Adda Fatima kyau, wataran Addagana ma tace nafi kowa kyau a gidan, kuma ka tambaya yayah kaji", ta faɗa kaman zatayi kuka.

"kwantar da hankalin ki Princess babu ta inda Fatima ta fiki kyau, kawai haushi ya keji don matar da zan aura tafi tashi matar kyau, kada ki wani ɓata hawayenki zan karɓa miki ba sai kin ɓata yawun bakin ki ba", ya faɗa yana kai duka wa Abban mu, wanda shi kuma sai dariyan su yake tayi yana chigaba da driving ɗinshi.

Har suka iso gidan mu faɗan bai ƙareba, mu kuma nida Hassan da gudu muka zo muka rungume Aunty Hauwa, itama da murnan ta ta rungume mu, kaman zatayi yayah don daɗin ganin mu, Hassan yana duban ta yace, "Aunty Hauwa inace kinfi sona akan Hissain? tunda nine babanki ko?" ya faɗa yana shan gaba na kada na matsa kusa da Aunty Hauwa.

Tana dariya ta sunkuya ta riƙo hannun mu tace, "dukkan ku ina son ku iri ɗaya, amma kai nafi sonka saboda sunan Baba na kaci, shi kuma nafi son shi saboda shiɗin rayuwata ce, Hassan farinciki nane, Hussain kuma rayuwata ce, kaga dukkanku ina sonku, amma yanzu zan fi son wanda yafi jin magana a cikin ku", ta ƙarasa faɗi tana miƙa mana sweet wasu manya-manya dasu kowa uku-uku a hannun shi.
Chapter 38 · 0% Book details