Sashe 43
Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama da Addagana da su kawu auwalu da uncle baba da Aunty ummi da ÆŠanta wanda baifi 5month ba mai sunan Bappah, ana ce mishi Affan, duk sun zo mana lagos, daÉ—i muke ji kaman babu gobe, haka akayi ta pictures ana raha, da dare ranan Aunty hauwa tace ita a gidan mu zata kwana, domin ganin Æ´an uwa duk sun haÉ—u, haka Baba umar ya amince mata, akan tayi kwana biyu idan su Mama da Adda sun tafi zaizo ya É—auke ta, abin daÉ—in kuma aranan ya bawa Aunty hauwa da Aunty suwaiba kyautar mota, Aunty hauwa ta É—auki Ash, Aunty Suwaiba kuma ta É—auki black, duk muka haÉ—u muka taya su, murna, baby Aishan mu kuma ya bata kyautan gidan gonan shi da yake garin Narabi, sannan ya buÉ—e mata account ya saka 5million a ciki.
Duk wannan kyaututtukan a gaban Abban mu akayi shi, bayan an ƙira baban narabi an sanar mishi, Baban Narabi yana dariya yace, "Toh godiya muke Baban mu, domin wannan kyauta da kayiwa uwargida na wani da ita kayiwa, domin zan cigaba da riƙe mata har sai ta girma, idan mai sonta ya fito sai muyi shaɗi da shi, wanda yaci gasan ya aureta ya riƙe mata, don nasan ni zan cinye gasan", ya faɗa yana dariya, duk su Abba ma dariyan sukayi domin a handsfree Baba Umar ya saka.
Aunty Suwaiba tana dariya bayan ankashe wayan tace lallai muƙi wayon Baban Narabi, wannan golden girl ɗin ƴar mun ae sai mun darje mazan duniyan nan kafin mu yarda mu bata mijin, ina zata kai Baban namu alokacin"? Kowa dariya yayi ana kallon Aisha da ta ɗale kan cinyan Babanya sai ja mishi gashin gemun shi ɗan kaɗan da ya ajiye ta keyi, shi kuma sai bin ta da dariya yakeyi.
Chan kuma ta koma tana jan gashin kanshi sai gwalamniyan surutu ta je mishi yana ta dariya, yana duban ta da murmushi a fuskarshi, batare da ya dubi idon kowa ba yace, "Gambo" Abba ya ɗaga kai yana duban shi batare da ya amsa ba, Baba Umar yayi murmushi yana kan wasa da jelan gashin Aisha yace, "Gambo duk duniyan nan idan ka cire Baban narabi da uwata da ta daɗe da rasuwa, toh Allah bai taɓa sakamun son abu ba aduniyan nan irin Aisha Humairah, ina sonta har ban san irin shi ba, wataran idan suna bacci da uwar sai na tashi basu sani ba, na ɗauketa nayita kuka, domin ina jin ajikina kaman bazata samu gatan mahaifi ba, kaman bazan daɗe tare da ita ba, sai inajin tausayinta hala ko ita kaɗaice rabo na? Ko bazata samu ɗan'uwa ba? Hala ita kaɗai zata kasance abinda zan haifa, amma idan na tuna tana da kai tana da Ummi, tana da Hassan da hussain, sai na samu nutsuwa a zuciyata, domin nasan bazata taɓa maraici ba a duniya, bazata taɓa kukan rashin ƴan'uwa ba, domin Hassan da Hussain sun ishe ta rayuwa, ga kuma Affan ta samu ƙanin ta abokin wasan ta, yadda Hauwa da Baba ƙarami sukeyi haka ita ma zata samu nata ƴan'uwan", ya faɗa fuskan shi da murmushi yana share hawayen idon shi kuma.
Jikin kowa yayi sanyi gaba ɗaya a parlourn, a hankali Aunty suwaiba ta saka hannu ta ɗauki Aisha tana share hawayen idon ta tace, "narasa mai yasa kake yawan irin wannan zan tukun kwanan nan, nifa har kasa ina jin tausayin kaina da kuma hauwa da wannan yarinyar da Allah ya bamu kyautanta, duk da ka ƙwace mana ita ka kyuatar, amma bamuyi fushi ba, muna fatan baɗi hauwa ta haifa mana ƴan biyu, ta bani ɗaya ta riƙe ɗaya, bayan wani shekara ta kawo mana ƴan uku, lokacin kuma ni zan ɗauke su dukkan su, amma idan kana wannan furucin sai kasa jikina yana sanyi, faɗuwar gaba na yana yawaita, tsoro yana kamani, ina ji ajikina kodai bani da rabon riƙe ɗan ka a hannuna ne har na koma ga ubangiji"? Ta faɗa tana share hawayenta.
Juyar da kai Aunty hauwa tayi tana kuka a hankali, murya yana rawa tace, "nidai ka daina faɗar mun da gaba na hero, muna nan tare har tsufan mu insha Allahu, ke kuma suwaiba ki daina mun fatan haihuwa dayawa, kema insha Allahu baɗi zaki haifa mana ƴan biyun, kidai na fitar da rai daga alkhairin Allah, kuma ni nama fasa kwanan ku tashi mutafi gida kawai, idan yaso mubar musu Aishan a gidan su ni nama yaye ta daga yau," ta faɗa tana miƙewa.
Baba umar yana dariya yace, "wallahu baki isa cire mun uwata a nono tana shekara ɗaya ba, ke hauwa kifita a idona fah", ya faɗa yana dariya, sannan ya dubi Ummi da ta sunkuyar da kanta tuntuni yana dariya yace, "Babbar ya uwa, wallahi kada kibari koda wasa Haiwa ta cire mun uwa a nono, kuma ko wani irin tashin hankali ne zai sameta toh ta maida hankalinta akan uwata", ya faɗa yana miƙa hannu wa Abba da yakasa cewa uffan sai kallon kowa yake yi kawai.
Aunty suwaiba ita ma miƙewa tayi tana dariyan hauwa tace, "ke kululwa yaifa babu inda zaki bimu, kima je ki gyara wurin kwanciyar da kyau yau a gidan nan, kibar ni yau nabi mijina, ke kuma bayanzu ba, ki zauna ciki ƴan'uwanki kusha hira, ki kula mun da sanyin idona kuma da kyau, ki bata non tasha ta ƙoshi bayan kin mata wanka ta huta gajjiyan yau", sannan ta ɗago Aisha ta sake duban Ummi tace, "Ummi naso ace idan ɗiyata ta girma na haɗa ta aure da Hassan ko Hussain, amma kuma Babanta yace su ɗin ƴan'uwanta ne, ke kuma uwace, toh na haƙura ina yiwa hasken zuciyata addu'an Allah ya bata miji nagari jarumin gaske, wanda zai sota da amana, saboda bana son Aisha tasan ba Ummi bace ta haifeta, kuma bana son ta san su Hassan ba ƴan'uwanta ciki ɗaya bane, saboda haka Ummi da Abba mun bar ku da ɗawainiya Allah ya baku ikon riƙewa, ke kuma Hauwa kiyi haƙuri da rayuwa ki rungumi kowani irin ƙaddara da hannu bibbiyu a rayuwar ki, ki yafe mun rashin fahimtar ki danayi a baya, kuma insha Allahu zaki haifo mana wasu yaran masu irin kyaun ki da sakalcin ki da wannan rikici da yangan," ta kara faɗa tana guge hawayen ta tana dariyan Aunty hauwa da ta tashi ta rungumeta tana kuka, daga baya ita ma Aunty suwaiban kukan ta fara.
Ganin haka sai Baba umar yazo ya jawo hannun Aunty hauwa yana dariya yace, "bari muyi waje na rarrashi kayata kafin ku fito," ya jata sukayi waje, parlourn kuma duk anyi tsit, sai sautin muryan kukan Aunty suwaiba ,Ummi da uncle Baba da Aunty Ummi da wata ƙanwar Baba Umar da tazo daga jos kawai akeji, wanda ita ma a wurin su Aunty hauwan zata kwana, sai da suka bawa Baba Umar da Aunty hauwa good 30minutes tukun suka bi bayan su, lokacin nida Hassan duk mun yasu a parlourn munyi bacci, ɗayan gefen ma Affan yayi bacci acan ɗaki wurin su Mama wanda basu san me akeyi ba a parlourn, amma Aisha idon ta biyu tana rungume jikin Aunty suwaiba, a haka suka fita waje inda su Aunty hauwa suke zaune a mota ita da Baba Umar yana ta aikin rarrashinta.
Kiss Baba Umar yayiwa Aisha bayan ya miƙa ta wa Aunty hauwa, sannan ita kuma ya ɗan lakuce kumatun ta yana murmushi yace, "bye bye my heart"! Aunty suwaiba tana tsokanan ta tace, "hauwa yau kam na miki wayo na tafi da miji na, zamuje muyita shan soyayyah babu ke, yau har rawan da kika taɓa mishi ina kallon ki ban kuƙa ki ba zanje na mishi", ta faɗa tana dariyan Aunty hauwa da ta ke hararan ta da wasa, a haka suka shiga mota suka tafi suna ta ɗaga mana hannu.
Dama su Aunty suwaiba basu bar gidan mu ba sai wajen 12:00pm na dare, toh Ummi suna dawuwa aka tattare gift É—in da muka samu aka kai É—akin mu, sannan kowa yayi wanka yayi shirin kwanciya, wanda Aunty hauwa ko Aisha batayi wa wanka ba, sai share hawayenta ta keyi, Ummi ce ta É—auki Aisha tayi mata wanka ta bata cerelac ta sha, ta tafi da ita É—akinta wurin Abba, suna nan har wajen 2:00 ita da Abba basuyi bacci ba, Abba sai juyi yakeyi, chan sai Ummi ta dube shi tace, "me ya hanaka bacci ne"?
Murmushi yayi yace, "ke mai ya hanaki baccin"? Ajiyan zuciya Ummi tayi ta dubi Aisha da ta ke ta kallon sillin ido ta nuna mishi ita tace, "ga wanda ta hanani bacci, domin nafi so tayi bacci tukun", juyawa yayi ya kalli Aisha, a hankali ya jawo ta kusa da shi yace, "auta na me ya hanaki bacci"? Aisha ta kalle shi kaman ta gane mai yace, tana gwalamniyanta tace, "Dada" wato tana nufin Daddy, yadda take ƙiran Baba Umar da shi.
Abba zai bata amsa sai yaji ƙaran wayan shi, da sauri ya tashi ya ɗauka ya kai kan kunnen shi, bayan ya amsa Ummi taji yana amsawa da "ehh nine, akwai wani matsalah ne officer"? ya faɗa jikin shi duk rawa yakeyi, da sauri ya miƙe jiki na rawa ya ce, "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN" , sannan da ƙarfi yace, "Officer kuna wani asibitin ne"?