← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 66

Sashe 28

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina dab da zan shiga kawai sai naji anyi wulli da ni gefe, wanda sai da nayi ƙoƙarin gaske na daka tar da kaina daga faɗuwa, juya wan da zanyi kawai sai naga Dr Khadijah ce ta wullar dani, ita kuma tayi sauri ta shige gaban motan.

Da sauri Dr Hussain ya fito daga motan ya taho inda na ke da gaggawa, hannun shi ya saka ya riƙo hannu na, hankalin shi tashe ya fara tambaya na, "Baby bakiji ciwo ba? Babu abinda ya same ki"? Ya na tambayan muryan shi da ƙarfi wanda yaja hankalin mutanen da suke wurin, kuma cikin tashin hankali ya keyi, ni kuma ganin hankalin shi ya tashi kuma duk idon mutane ya dawo kanmu, na juya na dubi Dr Khadijah, naga yadda ta buɗe baki da ido tana kallon Dr cike da mamaki, a zuciyata sai naji na raya bari na nuna mata matsayina a wurin Dr, kuka na fara nayi sauri na rungume shi ina faɗin, "Dr nah kaman hannu na data jawo zai tsinke na keji, Dr nah ciwo yake mun har bayana, ni tsoron ta nakeji Baby nah, kace ta tafi bana son ganinta", na faɗa ina ɓoye fuskana a ƙirjinsh, wai duk na nuna mishi tsoron ganin ta nakeyi.

Ranshi a matuƙar ɓace ya saka hannu ya fisgota da ƙarfin gaske daga cikin motan wanda har sai da kanta ya bugu da jikin motan, wuntsilar da ita yayi da ƙarfi har saida ta faɗi ƙasa, sannan ya dawo dani gefen shi na hagu ya rungume ni ta gefe, ya ɗaga hannun shi na dama yana nuna ta da yatsa yace, "daga yau na miki tsakani da matar da zan aura, Khadijah daga yau na miki iyaka da rayuta, wallahi na rantse miki da Allah idan wani abu ya faru da ita daga rana mai kaman ta yau hukuma za ta mana iyaka ni dake, domin, Hummy bana iya haɗata da komai a rayuwata saboda ita ɗin rayuwa tace, itaɗin haskene a gare ni, duk wani abu da ya sameta marar kyau bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda haka ki maida hankalin ki, kuma a yau zaki fuskanci waye Dr Hussain Mohd Aliyu, kuma a yau hukumar makaranta zata miki iyaka dani da iyalina, idan kuma ba a ɗauka hukuncin da yaka mata ba, toh dole na haɗaki da hukuman ƙasan ra ɗauka ƙwaƙwaran mataki akan ki, domin taɓa baby", ya saka hannu ya nuna mata ni, "kaman kin gayyato tashin masifar da tafi ƙarfin cutar cirona virus na a wurina, saboda haka ki kiyaye".

A lokacin shugaban makarantar dana department ɗin suka iso wurin, ga kuma wasu securities mata da aka ƙira suka iso, gaba ɗaya idon Dr Hussain yayi wani irin ja don tsabar masifah, ga wani rawa da jikin shi ya keyi, hannu shugaban makarantar ya saka ya ɗaga Dr Khadijah wanda gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata, sannan ya bubbuga kafaɗan Dr Hussain a hankali yace, "Dr zamu sake jan kunne wa Dr Khadijah a kashi na biyu, wanda idan bata gyara tsarin rayuwarta ba mun maka alƙawarin Makaranta za ta ɗauki hukunci mai ƙarfi gaske akanta, saboda kowa ya maka shaidah baka da abokin faɗa, kai ka bada rayuwar ka da lokacinka ne kawai akan aikin ka, babu wanda ya taɓa jin tsakanin ka da kowa, sai Khadijah da ta ke maka shishshigi, amma kayi haƙuri ka ɗauki sister ka ku tafi hospital a duba mata hannun, don bamu so iyayen yarinya suji wani abu ya samu ƴar su ta dalilin staff ɗinmu, domin zai jawo mana matsalah mai girman gaske".

Sannan ya sallami student É—in da suke tsatstsaye a wurin da sauran staffs É—insu, ya kuma umurchi Dr Khadija da ta wuce office É—in shi, sannan ya É—ubi Dr Hissain yace, "Dr kamaida su ka taho akwai zama da zamuyi da kai da Khadijah a office É—ina".

Muna isowa gate ɗin gidan mu ya juya ya dubi Amaal yace, "zaku iya shiga ciki ko na shigar daku"? Da sauri Amaal tace, "zamu iya gara kaje tun da ana nemanka da sauri a school, Dr kuma don Allah kayi haƙuri kaji".

Kallona yayi bai iya amsa abinda Amaal ta faɗa ba, a hankali naji yace, "Baby hannun yana ciwo? Zaki iya daurewa na dawo sai na kaiki hospital, ko kuma na ƙira Dr Abdallah yazo ya duba mun hannun ki"?

Sheshsheƙa na fara yi alaman zanyi kuka, nayi sauri na kwanta akan ƙirjin shi inda na ɗauki hannu na na ɗaura a daidai saitin heart ɗinshi, inajin yadda heart ɗin ya ke bugawa da sauri- da sauri na fara kuka ina cewa, "baby ni na daina jin ciwo a hannuna, kawai inajin ciwon ta ɓata mun ranka ne, baby kaji heart ɗinka yadda yake bugawa da sauri da sauri, idan wani abu ya saman mu kai wallahi bazan yafe mata ba, ni wallahi sai na faɗawa Daddy na", na faɗa ina ƙaea sautin kuka na.

Ɗago ni yayi a hankali yana duba na yace, "baby kada ki gayawa Daddy, zaiyi tunanin na gaza da baki kulawa ne, kiyi haƙuri babu abinda zai same ni insha Allahu, kawai na damu ne don bazan iya barin wani ma haluƙi yaci zarafin ki ina gani ba, kuma ina baki tabbacin baxan taɓa barin Khadijah ta sake maimaita miki ba, sai dai ta bar school ɗin nan, nidai kiyi haƙuri bari naje na dawo sai muje hospital ɗin".

"kada ka damu baby na, zan shafa maganin Amaal, dama damuwa na kai ne, kaje sai kadawo my dear, Allah ya tsare mun kai", na faÉ—a ina buÉ—e motan, haka yaja ya tafi, ni kuma na dubi Amaal muka shigo cikin gidan.

muna shigowa Amaal ta kalle ni tace, "munasira babu maganin da zan baki ki shafa, don nasan babu inda yake miki ciwo, sai tsabar sakalcin soyayyah da yake ɓuɓɓula duk wani gaɓa na jikin ki, toh yau hankalin ki ya kwanta , Dr Hussain ya nuna wa duniya babu kaman ki a zuciyar shi ƙorafi ya ƙare daga yau", ta faɗa tana buɗe mana gidan mu.

Dariya nayi na faɗin ƙasan carpet ɗin ina ta juyi a ƙasa ina cewa, "wayyo my one and only, wayyo babyn baby, wayyo my heart, wayyo honey na, yau kasa ina maka ɓulɓulan so, babu abinda ya saura sai kadawo na riƙe ka wunin yau inyi ta shagwaɓa iya son raina, kai kuma kayita jinya", na faɗa ina ƙara kwashewa da dariya.

Harara Amaal ta mun tace, "amma ke baki da imani, kibar bawan Allah nan yaji da tafiyan da zamuyi gibe mubar shi, har na tsawon 1month, kibari kuyi sallama basai kin É—aga mishi hankali ba".

Tashi nayi na zauna ina kallonta, "lallai ma Amaal, ae saina lugwaigwaita mishi zuciya, wanda idan na tafi tsanani ya daure yayi 1week bai bi baya na ba, kina ganin zan iya 1month babu shi kusa dani? Bazai taɓa yiwuwa ba, tunda Abbu suka ɗauki nauyin Hummy toh dole su haɗa dana Dr nah", na faɗa ina ƙyalƙyala dariya, ganin yadda Amaal ta bar abinda ta keyi tana kallo na.

"Hmm Hummy kice yau na yi laɓe naga yadda zaki birkita mun kan Dr"?

Dariya na sakeyi nace, "ki tsaya gulma dai kada kije ki birkita kan naki Dr, nidai babu ruwana idan kinga Dr na ya biyoni ke kuma na barki da zaman hira da Ummu".

"Hummm ni Hummy yanzu gaba ɗaya mamaki kike bani, yadda kika iya ɗauke hankalin wannan babban mutumin, babu wani fargaba yau ya yanƙwana ƙatuwar mata kaman Dr Khadijah akanki"?

_Nima Aunty Nice mamaki nakeji na yadda mutumin da bazai iya furta kalmar so ba, amma yayi mata abinda yafi ƙarfin furta kalmaɓ so ɗin ma yau a idon student da malaman su, besty ta dubeni tace "humm Aunty nice mamakin namiji kikeyi?ae ya wuce haka ma idan akan abinda yake sone, kawai yanzu ki bari mujira da wuwan shi muji yayah za ayi sallaman nan", kallonta nayi nace , "toh bari na tafi na nemo neat lady, saboda mutane suna ta neman book ɗin ta amma ni ban san ina take laɓewa ba, gara naje har gida na fito da ita taxo tayi typing dole yau_.

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/10, 14:46] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 22📑*

*__________📖* Babu ɓata lokaci muka shiga bedroom ɗinmu muka fara haɗa kayan mu, muna cikinyi akayi azahar, muna idar da sallah Dr ya ƙirani a waya yace, "Baby kije bakin gate akwai masinjan mu ya kawo muku abinci, don Allah kiyi haƙuri har yanzu bamu gama case ɗinnan ba", haƙuri na bashi sannan na mishi godiya.

Wajen gate ɗin na fito na karɓi ledan da aka mana take-away ɗin, na shigo haraban gidan muka haɗu da Peter da David, murmushi suka fara mun, Peter kuma yana harara na da wasa, domin fuskanshi ɗauke yake da murmushi, "preety wato Dr ya ɓoye mana ke ko"? Ya faɗa yana duban ƙofan gidan Dr.

Dariya David yayi yace, "ba dole ya ɓoye mata mai kyau ba, kaga laifin shi ne bros"? Nima dariya nayi ganin sun harbo jirgin mu, ina duban su nace, "baku fahimta bane Dr ba soyayyah muke yi da shi ba, yayah nane fah".

Dariya sukayi suna kallon junan su, peter yace "mun yadda ba soyayyah kukeyi ba, amma yau meye ake faÉ—a a depertment É—in mu? Ko ina ka tsaya guys sai labarin tashin hankalin da Dr yayi akan ki ake tayi, toh duk wannan ma ba soyayyah bane ko"? Zaro ido nayi na juya ina dariya nayi hanyan side É—inmu, suma dariya sukeyi suna cewa na gudu don naji zasu faÉ—i gaskiya.
Chapter 28 · 0% Book details