← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 66

Sashe 15

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BuÉ—e ido ya yi yana kallo na fuskar shi É—auke da murmushi,

"anya idan na tashi ƙara aure zan samu mai irin yanayin ki kuwa? Ina son macen da zata buɗe mun gaskiyar zuciyar ta a kaina, ina buƙatan macen da ni kaɗai zata na ganin nafi kowa ni namiji a rayuwar ta".
ya faÉ—a idon shi cikin nawa.

Matso da kujera na na yi kusa da na shi, murya a hankali nace, "Dr Khadija bata gaya maka ne? Kuma zaka iya ƙara aure bayan kace tafi kowa yi maka kyau?".

"Kyawun ta baya ruÉ—i na, saboda ni soyayyar mace na tsakani da Allah na ke so, kuma irin halayen...".
sai kuma ya yi shiru bai ƙarasa faɗin abinda zai faɗa ba.

"Me ka ke so kace mun Dr? To ni nace maka kana da kyau mai kyau, nima ka ce ina da shi mana, kasan nafi son na auri mijin da zaice mun Hummy kina da kyau, Hummy gayun ki yana burge ni, kai Hummy yau kin mun kyawun da ba bu macen da taɓa yin irin na ki".
na faÉ—a ina kwaikwayon irin muryan da mijin zai dinga faÉ—i.

Kallo na ya ke yi fuskar shi cike da farin ciki, shima matso da kanshi ya yi kusa da nawa a hankali yace, "kyautan me ki ke so na miki yau?".

Duban shi nayi fuska a yamutse na ce,
"kyau ta kaman ya ya? Ni da na ce ka ce mun ina da kyau ka ƙi, sai kuma kace mun kyautan me na ke so kamun? Ni bana so kawai kace ina da kyau, kuma ga shi baka ce kaya na sun mun kyau ba".
Na faÉ—a ina hararan shi, wanda fuskar mun ta yi kusa dana juna.

Lumshe idon shi ya yi sannan ya sake buÉ—e su a kaina, a hankali yace, "kazar mayun nan ba kiji ta ce yau yakamata na miki kyauta ba? Saboda kin sakani ina ta farin ciki".

"Rabu da ita ai ni ba ka sakani farin cikin ba, saboda haka bana son kyautan komai, sai ranan da kace kai Hummy kin yi kyau, to zan gaya maka irin kyautan da na ke so".

"Ko ki gaya mun abin da na kike so ko kuma yau Dr'n ki ya yi ta miki kuka har sai kin faÉ—a mishi ya baki".
Ya faÉ—a kaman zai yi kuka yadda na ke yi.

Dariya na ke yi mai sauti ina kallon shi ya zunɓuro bakin shi irin yadda na ke mishi rigima,
"Dr ashe kaima ka iya sakalci? To kada kayi kuka Babyn baby, zan gaya maka abinda na ke so".

Tsayawa ya yi da abinda ya ke yi ya ƙura mun ido fuskan shi gaba ɗaya ya canja lokaci guda, a hankali ya furta, "Babyn baby" sai kuma ya runtse ido yana tuna ranan da Aisha tana kallon shi a gefen Ummi ya nata sakalci ta ce, "to sannu Babyn baby, don ka kusa ka ɗauki babyn ka amma kana sakalci kaman baby".
sa ke buÉ—e idon shi ya yi yana duba na a hankali ya ce, "tashi mu tafi gida Aisha Humaira".

Muna shiga mota na kalle shi na ce, "Babyn baby baka gaya mun dalilin da yasa baka gaya wa kazar mayu ni sister ka ba ne".

Juyowa ya yi ya dube ni, sannan ya maida kanshi kan tuƙin da ya ke yi yace,

_*KU KASANCE AKO YAUSHE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA, TSAKANIN DR HUSSAIN DA HUMAIRA, SANNAN KUMA KU SAMU SANIN WACECE AISHA?*_

*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
       ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

_*SADAUKARWAR PAGE ÆŠIN NA KUNE, HAFSAT ISAH PZ & HAUWA MUSTAPHA JAJERE A (Gaskiya Fans H) KUYI YANDA KU KE SO DA SHI, INA JIN DAÆŠIN YANDA KU KE SON WANNAN NOVEL ÆŠIN, SABODA HAKA MA BESTY NAH (Miss Xerks) TA CE NA GAISHE KU BOHOT-BOT... Kuji daÉ—in karatu lafiya.*_

*SHAFI NA 12📑*

*__________📖* Daga Abbu har Ummi sun ji daɗin karrama su da na yi musu, bayan munga ma dinner ta re da su, Abbu ya maida hankalin shi kan kallon News da ake yi na ƙasan, ni da Ummi kuma kaman wanda mu ka shekara muna tare, sai hira muke yi na rayuwar Amal da irin wahalar da ta ke sha.

"Ummi to me zai hana Amal ta dawo wuri na mu zauna tare? Saboda yanayin ciwon ta ina ga bai dace ta zauna ita É—aya ba, saboda wataran ina ga baza ta iya samun sararin yiwa Dr waya ba, ko me ki ke gani Ummi?".

Na faɗa ina matsawa jikin ta, tsabar samun wuri irin nawa, dama asali ni mai son naga ana nuna mun kulawa ne, domin duk ranan da kaka ta tazo gidan mu ko naje wurin ta, sai Daddy yayi ta mana shari'a, zata yi ta mitan ina tumurmusan ta, amma ina primary 6 Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya jiƙan ta da rahma.

Abbu ne ya juyo ya ƙurawa Ummi ido don jin mai za ta ce, amma sai Ummi naga ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai tunani, har tsawon wani lokaci sai ta ɗago tace,

"Humaira ba wai naƙi shawaran ki bane, iyayen ki ina ga ba lallai ne su yadda ba, and secondly kuma ciwon Amal ba ita kaɗai ba, duk wanda ya raɓe ta ma sai ya sha wahalar jinya, keda aka kawo ki karatu, ai bai kamata mubar ki da jinyan Amal ba".
Ummi ta faÉ—a tana share guntun hawayen da ya biyo idon ta.

"Ummi Daddy na ba shi da matsala bazai hana ba, shima kullum sai yace tausayi na ya keyi na zama na ni kaɗai, kawai babu yadda ya iya ne, ciwon Amal kuma kawai nawa idan ya tashi ne na ƙira Dr ya tafi da ita asibiti, tun da asibitin su ba zama akeyi a wurin ba, ba kai musu abinci akeyi ba, komai acan ake musu, kinga ai babu wani matsala, bana son ta zauna ita ɗaya ne".

Abbu ya yi gyaran murya yace, "Humaira bani number shi mahaifin kin, nima nayi tunani irin naki tun da muka shigo gidan nan, idan Allah yasa ya amince ni zan fi samun kwanciyar hankali ma".
ya faɗa yana miƙo mun wayar shi.

Da sauri na amshi wayar tsabar murna jiki na har rawa ya ke tayi, number Daddy na juye mishi, na miƙo mishi ina ta murmushi.

Bai daɗe wayan yana ringing ba naji muryan Daddy yana sallama, alamar ya ɗauki wayan, Abbu ne ya fara gaishe shi, sannan ya mishi bayanin shi ne mahaifin Amal ƙawar Humairah, Allah sarki Daddy daga muryan shi za kaji yaji daɗin ƙiran da Abbu ya mishi, tambayar jikin Amal ɗin yayi, Abbu cikin farin ciki da jin daɗin an nuna kula akan ƴar ta shi ya amsa da sauƙi, sannan Abbu ya gayawa Daddy manufar ƙiran shi da ya yi.

Daddy ma ya nuna jin daɗin shi in da ya ke cewa Abbu ai daman kulum zama na ni kaɗai tausayi na ya ke ji, don ma ya bada amana na wurin Dr Hussain ne ya samu ɗan sauƙin tunanin abun, amma ai bakamar yadda zasu zauna su biyu ba, don kuwa zata daina jin kaɗaici, kuma za suyi karatu tare.

Daddy yace mishi kuma zai yi bayani wa Dr Hussain ya saka musu ido sosai a rayuwar su da kuma karatun su, duk da kullum alkhairin mu yake gaya mishi, shima Abbun yace insha Allahu kafin ya tafi zai sake samun Dr Hussain É—in, haka suka yi sallama kaman wanda su ka daÉ—e da sanin juna.

Kallon mu Abbu yayi yana murmushi, ya jawo flask yana zuba shayi mai cike da kayan ƙamshi, irin su citta da su kanamfari,

"wato Humaira ina ga a wurin mahaifin ki ki ka gaji karamci, mutumin nan bai san wacece Amal ba da kuma iyayen Amal amma ya amince ku zauna tare, domin shi É—in É—an halak ne".
sannan ya mana bayanin duk yadda su kayi da Daddyn, kowan mu sai farin ciki ya ke yi.

Ina kallon Ummi nace, "Ummi gobe zanje na kwaso kayan Amal É—ita, ina dawowa a school".

Ummi tana mun dariya ta ce, "ki bari mana a sallame ta sai kuje tare, Ke kam ai gobe school ya kamata kije ki nutsu ki maida hankali a abinda za'a muku, É—ebo kayan kuma sai kubar shi sai weekend ko".

ÆŠaga kai nayi ina murmushi, sannan na É—auki wayana da ake kirana, ganin sunan Dr Hussain sai ya sakani tashi na wuce bedroom É—ina.

Kan bed É—in na hau na kwanta sannan na É—auki wayan da ya sa ke shigowa a karo na biyu, manna shi kawai nayi a kunne na ba tare da nace uffan ba, sautin murmushin shi naji, sannan naji yace,
"Babyn baby muna faÉ—a ne?".

Turo baki na yi kaman yana kallo na, yadda kasan jikar kulu idan sun haura da amininta Hussain 80k, na yi magana ƙasa-ƙasa nace, "to ba kai bane ba".

"To kuma ba ke bace ba".
ya faÉ—a yana kwaikwayon murya na.

Dariya nayi a ɓoye ina rufe baki na, ya sa ke cewa,
"kawai sai kice mata na kaman kwandon wanke-wanke, bayan irin kyawun ta da na ke gani bana tuna ita É—in gajeruwa ce, amma yau kinsa na fara tunawa ashe fa da kaÉ—an tafi kwandon wanke-wanke".

Ina dariya na ce, "Dr'n mu zaka daina son ta kenan?".

"Idan na daina son ta wacece zan so? Ko zaki sama mun wata?".

Rufe ido na yi ina jin daÉ—in da ban san meye dalilin shi ba,
"To kace mun bata da kyau, kuma ka dai na son ta".

"Tun da ki ka ce mun kaman kwando ta ke, sai na daina son ta, kuma na daina ganin kyawun ta".
ya faÉ—a shima yana jin daÉ—i da wani nutsuwa a ranshi daga in da ya ke.
Chapter 15 · 0% Book details