← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 66

Sashe 6

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin abinda yayi kawai sai na fashe da kuka ina buga ƙafa na a ƙasa ina faɗin,
"nikam wallahi nasan yayi daɗi Dr'n mu, kullum Daddy yaci abinci na sai yace duk duniya nafi kowa iya girki, kai kuma tun dana shigo baka yaba kwalliya na ba, baka kuma yaba abinci na ba, bayan Daddy yace ina da kyau kuma na iya gayu sosai, idan ya tashi aurar dani sai an yi layi ya zaɓa mun miji".

na faɗa ina ƙara fashewa da kuka.

"To ki bari hawaye ya ƙara sa ɓata miki mummunan kwalliyan kin, dama ba kyau ki kayi ba".
naji muryan shi yana gaya mun ba tare da ya kalli inda nake ba.

"Dr'n mu banyi kyau ba ne?".
na tashi tsaye ina juyawa a gaban shi ina ƙara gaya mishi bai ganni bane da kyau.

Bai sake kallo na ba yace, "zauna kici abincin ki kada yayi sanyi, duk ranan da kika koyi gaisuwa zan gaya miki kinyi kyau ko ba kiyi ba".
ya faɗa yana cigaba da cin ƙosan shi da kunu.

"Dr'n mu ina kwana".
na faɗa ina zunɓuro baki na gaba.

Gyaɗa kanshi yayi ba tare daya amsa mun ba, amma ya mun alaman ya amsa, saboda haka jawo plet nayi na zuba ƙosan na saka yajin a gefe na fara ci nima, ya rigani gamawa, bai ce mun komai ba, ya ƙara jawo flask ɗin ya ƙara kunun kusan rabin cup ɗin sannan ya ɗauka ya miƙe tsaye ya koma cikin parlon, kunna T.V yayi sannan ya nemi wuri ya zauna yana kallon news yana kuma kurɓan kunun shi, maida hankalina nayi kan abinci na har nagama ci, ina gamawa na tashi ina maida cup da plets ɗin da muka ci ƙosan cikin basket ɗina.

"Aisha ki bar mun flask É—in kunun".
ya faÉ—a idon shi yana kan T.V É—in, nima bance komai ba na mayar da flask É—in na ajiye, sannan na É—auko basket É—in na taho inda yake, ina kallon shi nace.

"Dr zan tafi me kake so a lunch?".

Idon shi masu tsananin kyau a cikin glass ɗin shi ya ƙura mun, ganin haka ya saka ni saurin ɗauke nawa idon ina ƙara maida fuskana alaman zanyi kuka, don ni bana so nayi abu ba'a yaba mun ba, wanda kullum hakan shi yake haɗa ni faɗa da ƴan gidan mu, amma Daddy komai nayi sai ya yaba mun, shi yasa nake jin daɗin yi mishi komai.

"Jeki É—auko mun books É—in ki kizo".
ya maida idon shi kan kallon da ya keyi bayan ya gama faÉ—in abinda zai ce.

Buga ƙafa na nayi a ƙasa ina ƙananun gunaguni,
"nikam har yanzu baka ce mun abincin yayi daÉ—i ba, tunda baka ce nayi kyau ba ai ya kamata kace abincin yayi daÉ—i, tunda nasan dai ni É—in mai kyau ce, tunda Daddy yace duk family'n mu babu mai kyau na".
na faÉ—a ina murguÉ—a mishi baki na don ganin ya juyo yana gani na.

Harara na yayi sannan yace,
"zaki wuce da shirmen ki kije ki É—auko mun books É—in ki ko sai na kira Daddy'n shi na gaya mishi baki son karatu"?.

"Toh ai baka da number'n Daddy, ta ina zaka gaya mishi".
Kallo na ya ke yi can sai naji ya karanto mun number Daddy.

Baki na buÉ—e ina kallon shi da mamaki, "dama ka san Daddy ne?".

"Wuce ki bani wuri ko na kira shi".

Da sauri na É—auki cup É—in da ya gama shan kunun nayi hanyar waje, ina fita yayi murmushin shi kaÉ—an yana girgiza kan shi, a hankali yace,

"Rigimammiya, komai nata irin na Aishan'n mu, nasan dai Ummi na bata sake haihuwa ba, da nace wannan Æ´ar Ummi ce, domin Aisha kowa yaganta sai yace babu abinda ta bari na Ummi, yadda nida Hassan babu abinda muka bari na Abban mu, sai dai banbancin hali da mukayi da Hassan".

da sauri ya kawar da tunanin a zuciyar shi, domin baya so ya dinga tunawa da su a rayuwar shi, fatan shi yadda yabar su har abada ya zama har cikin zuciyar shi ya manta da su, wanda duk yadda yayi a wannan tsawon shekarun da yayi babu su ya kasa, sai dai idan sun faÉ—o mishi a rai yayi sauri ya kawar da su.

Dai-dai lokacin da yaji Abban shi ya faɗo mishi a rai na furucin da yake yawan yi kullum a kan shi, ni kuma na dawo, ina kallon yadda ya ƙurawa ƙasan parlon ido kaman yana ƙirge, nima yasa nabi wurin da kallo, banga komai ba sai zanen flower carpet ɗin shi da yake tsakiyan parlon kawai nabi da ido, da sauri na ƙaraso wurin shi dai-dai fuskan shi nace.

"Dr'n mu yanayin ka irin na mutane masu haƙuri da nutsuwa wallahi, kuma baka da hayani amma ni kuma gaskiya ina da surutu kaman wanda naci.....".
Sai kuma na rufe baki na ina dariya.

Da sauri ya ɗago idon shi da suka yi ja ya ƙura mun ido, ina dariya na sake cewa,
"Dr'n mu idon ka kaman na zaki, dama *ALIYU* aka saka maka".
na faÉ—a ina binshi da murmushi.

Da ƙarfi ya runtse idon shi, kuma da ƙarfi ya furta, "Ya Allah".

sannan ya buÉ—e idon shi ya É—ora a kaina yana mai da numfashi kaman wanda yayi tsere, a zuciyar shi kuma yana maimaita,
_innalillahi wa'inna ilahir raji'un_, ya fara tuna wata rana haka Aisha ta taɓa gaya mishi lokacin suna zaune a parlon Abba ana karya wa sai ga Hassan ya shigo da fuska a ɗaure yana duban Hussain yace,

"Bros wani irin wulaƙanci ne an kirani a waya ba zaka ɗauka kace ina wanka ba, irin haka sai mai kiran yace ina wulaƙanci ne".

ya faɗa ya na ture mun ƙafa na da nashi ƙafan don neman ayi faɗa, ni kuma a rayuwa na tsani ka hau kaina da masifa kaman kai ka haife ni, don duk shiru na da haƙuri na bana iya ɗaukan raini da wulaƙanci, shi yasa kafin kaji baki na a abu sai komai ya ɓaci, cikin ɗaure fuska da nuna bana son raini na ɗago zan mishi masifa, kawai sai naji Abba ya dafa kafaɗa na yana ɗan bubbugawa yana cewa.

"Ubana Aliyu tabbas kai mai haƙuri ne da nutsuwa kaman mai sunan ka, kada ka yadda ka dinga biyewa ɗan'uwan ka ana jin kan ku, domin shi haƙuri baiwa ne wanda ba kowa yake da shi ba, tabbasa *ALIYU* da mai suna *ALIYU* basu son raini, amma sun kasa masu haƙuri da kuma nuna soyayya wa ɗan'uwan su mai tsafta, shi baka ga sayyadina Aliyu yadda yake son ɗan'uwan shi (Annabin rahma S.A.W ba?) to kayi koyi da shi kaji *ZAKI NA*".

Babu ɓata lokaci Ummi ta amsa da cewa,
"gaskiya Abban su baka yi mun kara yadda nake maka, nima fa Hassan yaci sunan nawa mahaifin *ABUBAKAR* Kuma kasan yadda shima Sayyadina *ABUBAKAR* ya kasance babban amini kuma masoyin manzon Allah (S.A.W), kuma koda ya kasance shi Hassan mai neman faɗa ne da ɗan'uwan sa ai zaka na min kara saboda dai Baba na mai haƙuri ne da kuma kawar da kai, don dai shi Hassan ya ɗauko halin ƙanwa tace *HAUWA* domin ita ce mai yawan neman tsokana da son ayi rikici".

ta faɗa wanda gaba ɗaya parlon muka kwashe da dariya saboda tunawa da halin Aunty Hauwa, wanda babu inda Hassan ya bar halinta kaman ita ta haife shi wurin neman tsokana da kuma masifa, don kullum ta zo gidan mu sai sun kacaɓe da Ummi duk kuwa da haƙurin Ummi, sai dai duk gidan su Ummi babu mai son ƴan'uwa da zumunci irin nata, ga kuma faɗan gaskiya, wanda idan ka ganta sai ka rantse mutum ɗaya ne ita da Ummi tsabar kaman nin su, sai dai banbancin shekaru, tunda mutane biyu ne a tsakanin su.

Ina dariya na kalli Ummi nace, "hmmm Ummi wallahi neman faɗan sune da yawan surutun su kaɗai iri ɗaya da Hassan, amma ita Aunty Hauwa ai nine na ɗauko son faɗin gaskiyar ta da halinta na son zumunci, amma shi wannan ai idan na gaya miki halin shi sai kin wuntsila shi ƙauyen ningi, kince sam wannan ba halinki na dattaku irin na mutanen garin *MISAU* yake da shi ba".

na faÉ—a ina kallon Hassan da yake harara na, dariya na fara mishi ina cewa, "ko na faÉ—a ne my heart?".

"Munafur ci kenan zaka koma, don nasan duk inda mai shiru yake, randa ya falle to munafurci zai haÉ—a, kuma ni nasan Ummi na da Abba na sun yadda da ni kawai nema kake su fi sonka a kaina shiya sa zaka mun sharri".
ya faÉ—a yana jinginuwa da jikin Ummin mu.

Abba dariya yayi yace, "kaga shalelen Ummi'n shi, daɗinta ma ga Aisha nan, dole kayi haƙuri da cinyar Ummi".

A lokacin Hassan hararan Aisha yayi, ita kuma ta murguÉ—a mishi baki, wanda kullum na rasa mai yasa basu zama inuwa É—aya, amma ni bana da lokacin tanka musu.

"Dr'mu ka kula ni mana".
na mishi magana cikin shagwaɓa, don tunda yayi mun tsawa ya razanani sai kuma ya koma yayi shiru idon shi a runtse, wanda daga dukkan alamu tunani ya tafi.

Ƙura mun ido yayi duk alaman hawaye ya cika idon shi, a hankali ya miƙo mun hannu muryan shi can ƙasa yace,

"Aishan mu taho wurina ki bani labarin Hussain da Ummi na da Abba na, yanzu ciwon Ummi na yana tashi? Ko kuma tunda komai ya riga ya faru zuciyar ta bazata sake barinta ta samu lafiya ba, zo kusa da ni Aisha na, ni kaÉ—ai nake son ki sama da irin wanda Ummi ta ke miki".

Tsoro naji ya lulluɓe ni domin hawaye ne masu gudun gaske suke biyo fuskan Dr mu, wanda duk sai naji na rasa abinda yake mun daɗi, da sauri ina jijjiga kaina alaman ba haka bane, nima hawaye yana zuba mun amma nawa na ganin abinda nake girmamawa yana hawaye shi ya dame ni nace.

"Dr'n mu bani bace fa Aisha'n, ni fa Hummaira ake gaya mun, Dr'n mu wacece Aishan? Matar ka ce? Ƴar'uwar kace? Wacece ita ne Dr na?".
na faɗa lokacin da sautin kuka na ya ƙaru.
Chapter 6 · 0% Book details