← Book details Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 66

Sashe 1

Kaddara Ta Riga Fata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
    *SHAWWAL/JUNE.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*

*SADAUKARWA WA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 1📑*

*__________📖* BARCELONA

Duk yadda naso nayi bacci abin ya gagara, tsabar farin ciki tun lokacin sallan Asuba bai yiba na shiga toilet nayi wanka na ɗauro alwala, ina fitowa a parlon na kalli ɗakin yadda aka ƙawata mun shi, nika ɗai na naji na sake fashewa da dariya, murya a bayyane na furta.

"Wayyo Daddy nah, ni a rayuwa mai zan maka na nuna maka irin farin cikin da ka sakani a rayuwata"? Na faɗa ina maida hannu na da kyau ina ƙara kankame towel ɗina.

Sallaya na shimfiɗa nayi raka'atul fajir, na cigaba da jan carbi inata istighfari, har naji wayata tana sanar dani lokacin sallan Asubah tayi, don tunda zan kwanta Daddy ya karɓi wayana ya saka mun alerm.

Tashi nayi nayi sallan Asubah sannan na zauna ina askhar, fuskana ɗauke da murmushi, ina gamawa na ɗauko qur'ani na na fara bitan karatu na, har saida gari ya fara haske tukun na miƙe na tafi gaban mirrow.

Wata Red dogin riga na nasaka, wanda yayi bala'in fito da kyau na da ƙuruciyata, wanda banfi 16yrs ba, don banfi 5month da cikawa ba, dai-dai lokacin naji muryan Daddy yana ƙirana dai-dai da buga ƙofan da yakeyi.

Da sauri naje na buɗe ƙofan ina dariya na ɗan sunkuyo dai-dai fuskan Daddy ina faɗin, "Good morning my dad," zaro ido Daddy yayi cikin mamaki yana kallona, a hankali yasa hannu akan haɓan shi yana cewa, "sweet heart har kin shiryah"? Dariya na fara yi ina kallon Daddy nace, "ae nayi 2hrs da shiryawa Daddy", sannnan na fito daga ɗakin na saka hannu na riƙe na Daddy mukayi hanyan parlon, inda cikin rawan kaina kaman zan koma cikin shi nace, "Daddy kasan daɗin dana ji kuwa? Daddy kullum zan ta maka addu'a Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira", na faɗa ina duban fuskan Daddy da yake ta murmushi.

Muna zama a kan dinning ya dube ni hannun shi riƙe da nawa yace, "sweet heart ni abinda nake so ɗaya zuwa biyu ne a wurinki, na farko ki maida hankali akan abinda ya kawoki kinji?, na biyu kuma ki riƙe mutuncin kanki saboda Allah kinji HUMMAIRAH nah".

Jikinta duk yayi sanyi ta ƙurawa Babanta ido, kaman bazata yi magana ba, can kuma sai tace insha Allahi Daddy bazaka same ni da aikata wani mummunan abu ba, kodan ma....." sai kuma ta sunkuyar da kanta tana zubar da hawaye.

Daddy runtse ido yayi kaman shima zai zubar da hawaye, yana girgiza kanshi, can ya dube yace, "komai zakiyi sweet heart kiyi shi saboda Allah bawai don kina gudun maganan mutane ba, shi zai ki gyara rayuwar ko ko babu idon kowa, kisaka wa ranki Allah yana kallonki kinji".

Muna gama shan tea, Daddy ya sakani na fito muka fita har bakin titi, wanda tunda muka fito kallon unguwan da muke nakeyi, wanda yayi matuƙar ɗaukan hankalina, kaman Daddy ya san tunanin da nakeyi ya ƙara damƙe hannu na yace, "BOCABELLA, PASSATGE. sunan street ɗin da kike kenan sweet heart, ya miki kyau"?

Murmushin da yake kan fuskana ne ya ƙara ƙaruwa, na damƙe hannun Daddy da ƙarfi kaman zanyi tsalle nace, "Daddy na gode wallahi wurin ya mun kyau, kuma insha Allah na maka alƙawari da first class zan dawo maka, bazan taɓa sakaka kaji kunya ba", na faɗa ina ƙara saurin tafiya ta yadda naga Daddy ma yanayi.

Muna isowa kan titin saiga taxi ya tsaya, Daddy ne yace mishi *UNIVERSITY OF BARCELONA* da sauri na buÉ—e na shiga na zauna, munkai kusan 30mnt kafin muka isa school É—in, jikina har wani rawa yake yi tsabar yadda naga school É—in ya mun kyau.

Da sauri na kalli Daddy ina ɗan murmushi nace, "Daddy schooƙ ɗin yayi kyau" shima murmushin kawai yayi ƴa tare mana wani bus da naga yana shiga cikin school ɗon da student, wani gini mai kyau naga mun tsaya, nidai kawai bin Daddy nake har muka shiga wani office mai girman gaske, wani bature ɗan luti mai katon tunbi nagani a zaune cikin wannan makeken office ɗin, fuskan shi ɗauke da murna da farin ciki ya taso ya miƙawa Daddy hannu suka gaisa, sannan ya miƙo mun hannu don mu gaisa, amma cikin murmushin da yaƙi barin fuskana, na haɗa hannu na guri ɗaya na matse su a cinyana ina ɗan jujjuya jikina, na amsa mishi gaisiwan shi batare dana miƙa hannu ba, shima dariyan ya ɗanyi yana buga kafaɗan Daddy cikin turancin shi mai daɗin sauraro ya ke cewa Daddy, "Nice doughter ɗin shin"?.

Wuri Daddy ya zauna inda baturen ya nuna mishi, nima gefen Daddy na zauna kaman zan koma cikin shi, haka sukayi ta hira a ƙarshe naga ya ɗaga waya ya ƙira wata yarinya, tana shigowa nagan ta kaman zata ɓalle don rama, har inda yake ta ƙarisa ta gaishe shi, daga nan ya mata bayanin department ɗinmu ɗaya da ita, kuma nima doughter shine, saboda haka ta tafi dani har class ɗin da muke lectures.

Hannu ta miƙo mun cikin sakin fuska, ban ɓata lokaci ba na miƙa mata muka gaisa inda tana riƙe da hannu na tace, "my name is *VICKY*, ina binta da murmushi nace mata, " *AISHA HUMMAIRAH*" cikin murmushi ta sake cewa, "nice name".

Daddy sai binmu da murmushi yakeyi har muka fita, inda kafin mu fita na zo na rungume Daddy nace, "Daddy zaka jirani ne"?

yana É—an dariya ya É—aura hannun shi a kafaÉ—a na yace, "zan koma gida akwai abinda zanyi, kina tashi ki nemi taxi ki bashi wannan card É—in har gidan zasu kawo ki ko sweet heart", ya faÉ—a yana bina da kallo har muka fita.

Muna kan hanya vicky take ta bani labarin yadda last week suka fara lectures, da kuma yadda tayi mamakin tana ganewa, domin ita tun a secondry babu abin da take so irin *ACCOUNTING* Nima murmushi nake binta da shi saboda yadda nake son course É—in, kuma buri na kenan naga na karanta Accounting, don burina naga na zama chartart acoountant wata rana, har class muka isa vicky sai labarin daÉ—in course É—in take bani, amma muna dai-dai da zamu shiga class É—in take gaya mun wahalar wani course wai shi *FINANCIAL ACCOUNTING* amma ita tanaga tsoron lecturer suke ji shiyasa suke ganin kaman da wahala.

Kallonta nayi cikin mamaki nace, "yana baku matsalah ne lecturer"? É—an ya mutsa fuskanta tayi tana girgiza kanta tace, "no kawai baya dariya ne, kuma yana É—aukan attendance, kawai dai baya dariya ko kaÉ—an".

Haka muka shiga class É—in, abin mamaki sai naga bamu fi mu 15 ba, cikin mamaki na dubi vicky nake tambaye ta "ina sauran Æ´an class É—in"? Tana murmushi tace mun mu 15 ne dama, amma kusan class uku ne ko wanne 15, sai lokacin exam zamu haÉ—u dasu a hall É—aya.

Muna zama bamu 5mnt ba sai ga wani lecturer ya shigo, kana ganin shi kaga ɗan gayu, gashi bayida wani tsayi amma sai wani bouncing yake yi, ƙasa-ƙasa vicky tace mun, "mr solomon, yana ɗaukan mu *COST ACCOUNTING* Ina jijjiga kai batare da na dube ta ba na maida hankalina kanshi, abin sha'awa duk da yau na fara shiga class ɗin amma na fahimci lectures ɗin mutumin yadda baku tsammani, inda yamana wani topic *BUDGET CONTROL* gaskiya na gane lecturers ɗin sosai, haka mikayi lectures huɗu a ranan, a ƙarshe mace ce ta shigo ta mana *TAXATION* india ce amma taji turanci na fitar hankali.

har gate muka zo da vicky, inda na samu taxi har gida ya kawo ni, gaskiya na daÉ—e ina sha'awar kasar spain, inda yau Allah ya kawo ni É—aya daga cikin state É—inta, da farin ciki na shigo gidan, daga É—aki Daddy ya fito yana ware mun hannu, da gudu naje na faÉ—a jikinshi.

*Masoya novel ɗina wannan karon kumun uzuri ba zan dinga typing kullum ba, haka pages ɗina ba za suna yawa ba, nagode da ƙaunarku*

*HAKA ZALIKA MRS ZERKS BAKI BAZAI IYA FURTA KALMAR GODIYA ZUWA GAREKI BA, NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFI BESTY NAH, ALLAH YA BAR ƘAUNA*

*©AUNTY NICE•* ✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
     *1441H/2020M.*
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         ```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:[email protected]
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 3📑*

*__________📖* Girgizamata kai kawai nayi alamun babu wani dangantaka a tsakanin mu, wuri ta nema kusa dani ta zauna ƙasa-ƙasa tana gaya mun wai yanzu taji wani ɗan class ɗin mu yana cewa a tarihin Dr Hussain bai taɓa fita a class ya dawo ba, sunyi mamaki da sukaga ya dawo, shiyasa suke tunanin ko yasan ni ne.

A hankali na dubeta sannan nace, "Vicky ban san shi ba, a school É—in nan na fara ganin shi, kuma shima ina tunanin bai sanni ba, don na lura ko kallon fuskana bai yi ba, kawai may be yaga laifina na farko ne, shiyasa yamun uzuri".

na faÉ—a ina kallon ta, ita ma girgiza kai tayi alamun magana na haka yake.

Bayan mun dawo break ne muka yi lecture É—aya sannan muka ta shi, Amal ta dube ni lokacin muna fita a school É—in tace,

"Hummy yaushe zamuje muyi shooping ne? Don gaskiya akwai abubuwan da nake son na ƙara"......kaman bazan yi magana ba saboda tunanin daya cika zuciya ta, har ta manta dani sai kuma na samu bakina da furta,

"Mu bari ranan saturday sai muje wani mall dana gani kusa da inda nake, naga wurin yana da kyau da girma, ina ga zamu samu duk abinda muke buƙata a wurin".
Chapter 1 · 0% Book details