Sashe 8
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA HU Kasancewar yaya Ado dawowarsa daga wurin aiki kenan, ya sa ya shiga rage kayan jikinsa domin ya watsa ruwa ya gabatar da sallar Isha'i. Yana daga cikin akinsa ya fara jiyo ihun Labaran, ya girgiza kansa cike da takaici, yana jin haushin yadda gidansu ya zama tamkar gidan haya saboda yadda zuciyar kowa take a kusa. Ihun da Labaran yake kurmawa ne ya janyo hankulan mutane wasu suka fito, wasu kuma suka tsaya suna le ensa daga window. Yayin da wasu kuma suka rifa masa baya, domin su ga irin wainar da zai toya. Sashen Yaya Ado ya shiga, ya tsaya daga bakin ofa yana sauke numfashi cike da zafin rai. Yaya Ado ne ya le o da kansa daga shi zai gajeren wando, ya ha e fuska ganin Yaya Ado da ragowar mutanen gidan a sashen ba tare da sun nemi izininsa ba. Saboda yaya Ado mutum ne mai tsattsauran ra'ayi, kuma yana da a'idoji don haka suke cewa karatun boko ya mayar da shi mai a idar yahudawa. "Me ya sa ka shigo mini ba tare da izinina ba?" Yaya Ado ya tambaya fuska a ha e, Labaran ya ji kamar ya watsa masa ruwan zafi mai ha e da attaruhi, saboda ganinsa da ya yi da gajeren wando ka ai ya sake harzu a shi, musamman da ya tuna Rahina ta ce kwarton yana ta shafe ta a ban aki. A hankali Labaran ya fara takawa jikinsa har karkarwa yake, hannunsa ri e da aton almashi. Ganin haka ya sake ata ran Yaya Ado, saboda a duniya ya tsani wani ya ra akinsa saboda muhimman takardunsa da ba ya son wani ya ta a masa. A harzu e ya tunkari Labaran ya ce. "Kai Labaran ba magana nake yi maka ba?" Mutanen wurin carko-carko suka yi cikin mamaki suna kallon Labaran, cikin shammata Labaran ya yi kukan kura ya yi kan yaya Ado yana aga almashin sama, kamar yadda sojoji suke yi a filim ya i ya ce. "Zuwa na yi na halaka asurgumin fasi i da wannan almakashin." Yana gama magana ya kai hannu yana arin fisgar gajeren wandon Yaya Ado. Nan take suka shiga kiciniya, Yaya Ado yana arin kare kansa shi kuma Labaran arfi da yaji yake ihu da kururuwar sai ya guntule shi. Ganin haka ya ata ran yaya Ado, ya fusata ya aga Labaran ya damfara shi da asa. Labaran bai daddara ba ya sake mi ewa duk da ya ji zafin buguwar ya ce. "Wallahi yau ko kashe ni za ka yi sai dai mu kashe juna, ko banza na san zan mutu a fagen shahadar kare mutumcin matata." Yana rufe baki sai kawai ya saka hannu ya zugo gajeren wandon asa. Matan da suke wurin suka saki ihu suna fita waje a guje, yayin da Baba Ibrahim da Baba Sale suka yi kansu Labaran da gudu ganin da gaske yana shirin aikata abin da yake fa Fitar Hansatu ya yi daidai da parking in motar Fadil, da gudu da arasa wurinsa cikin kururuwa ta ce. "Likita don Allah ku taimako wallahi kisa za a yi, Ado ne da Labaran." Cikin izza ya sauke ba in gilashin idonsa, ya zuge gilas in motar cikin golden voice insa ya ce. "Lafiya?" Ya tambaya saboda bai ji abin da ta fa a ba, sakamakon gilashin motar da ke rufe. "Ado da Labaran ne za su kashe kansu har da makami, don Allah ku zo ku kawo auki." Hansatu ta sake maimaitawa a hargitse, ganin yanayin da take ciki na firgici ya sake tabbatar masa da abin da take fa . Ya saka hannu ya dafe goshinsa cikin takaici, saboda a kullum danasanin sakancewar zamansa a wannan gidan gandun yake yi. Bai tanka mata ba, ya ajiye lapcoat insa ya bu e murfin motar ya fito. amshin turarensa ya bugi hancin Hansatu, ita dai haka kawai rayuwar Fadil take birge ta don haka ma ta ci alwashin aura masa Badariyya, idan ta ara zama budurwa tun da dama namiji ai mijin mace hu u ne. Kuma matar Fadil ko ka an ba za ta nuna wa Badariyya komai ba, sai kyau da iyayin da take ta ama da ita likita ce. "Suna ina?" Fadil ya katse mata tunanin da take yi. Da hannu ta nuna masa mangaren Yaya Ado. Da sauri Fadil ya shiga, a daidai lokacin Malam mai Yasin da Inno su ma suka arasa. A lokacin yaya Ado ya samu nasarar ara aga Labaran ya buga da asa, hakan ne ya sake aga hankalin Inno sai ta fashe da kuka, da yar aka samu aka ri e Labaran, shi ma yaya Ado aka ri e shi kowannensu sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Malam ya kwantar da murya kamar bai san abin da ya faru ba, ya shiga tambayarsu abin da ya ha a su. Rai a ace yaya Ado ya ce. "Kun san dai a cikin gidan nan ba sabgar kowa nake shiga ba, saboda ba na aukar raini ba zan auki cin zarafi ba. Yanzu saboda Allah shekara nawa na ba wa Labara? ko Sale da yake bi na, ya isa ya zo ya yi mini iskancin daLaraban ya yi mini ballanta shi anina na biyu? Wallahi ko da wasa ka sake kwatanta mini abin da ka yi sai na ba ka mamaki sakarai bawan mace." Daga haka yaya Ado ya fisge hannunsa ya shige akinsa. Tun ba su ji ta bakin Labaran ba suka fara ba shi laifi a zuciyarsu, saboda kowa ya san yaya Ado shi ka ai yake gudanar da rayuwarsa bai cika shiga shirgin kowa ba bayan gaisuwa. Don haka ma ake zargi da ra e-ra in ko aljana ce ta aure shi, tun da ga annensa nan har biyu sun da e da aure amma shi shiru. "Kafin ku ji abin da ya faru don Allah zan tambaye ka Likita!" Labaran ya yi maganar yana kallon Fadil. Gya a masa kai ya yi alamar yana sauraronsa Labaran ya ce. "Idan yanzu na saka almashin nan na guntule yaya Ado, akai wani dashe da za a yi masa a likitance?" Takaici da kunya suka hana Fadil yin magana, kamar dai ba zai magana ba sai kuma da ile ya ce. "A'a" Labaran ya ha iyi yawu mai aci yana jin kishin Rahina yana nukurkusarsa ya ce, "Yaya Ado ne ya shiga ban aki ya lalube mini masoyiya tana wanka, saboda ya ga dare ya yi kuma wallahi idan duk garin nan gatansa ne sai na gama da shafinsa." Labaran yana gama fa ar haka ya shamace su ya fisge ya fa akin Yaya Ado cikin araji yana fa "Gafara ga maza nan bisa kanka." Ganin haka ya sa su ma ragowar mazan da ke tsaye suka rufe masa gaya. Da yar suka samu suka sake yage Labaran, sai da aka kai ruwa rana sannan aka ba wa Labaran ha uri ya ha ura. Dalilin da ya sa Labaran ya ha ura, saboda Baba Inu da Baba Ibrahim sun tabbatar da yaya Ado a kan idonsu ya shiga sashensa, kuma suna tsaye Labaran ya zo yana cewa an shiga ban akin da Rahina take wanka. "To kuwa idan haka ne akwai kwarto a cikin gidan nan, kuma ni da ma daga cikin ilimin da Allah Ya ba ni akwai na gane kwartaye. Kuma ni dama tuna zuwa ban yarda Ado zai aikata hakan ba. Za mu zuba aiki cikin an ilimin da Allah Ya ba mu, Allah Ya sa mu dace." Malama mai Yasin ya yi maganar da wata irin murya, kamar irin waliyan bayin Allahn nan. Gaba aya suka amsa masa sannan kowa ya watse. Washegari Tun da asuba bayan da Inno ta tashi Laraba yin Sallar Asuba, ta tabbatar mata da ba za ta je makaranta ba, saboda irin cin zarafin da Mai gari ya yi mata a gaban mutane da yaran gari. Don haka har kimanin arfe tara na safe tana kwace a kan gado tana bacci, daga ita sai rigar atamfa da an kanfai a jikinta. Zanin ya zame ya fa i gefen gado, yayin da ankwalinta ya fa asa. Sallama auke a bakinsa ya shiga akin Inno, Inno tana ganinsa ta ha e rai fara mita sama-sama. "Haka kawai a dinga tayar mini da zaune tsaye, ina dalili a ce duk bayan kwana uku sai an auna jinin mutum. Ni dai tun farko Burema ya cuce ni da ya sayo abin nan ya ce ka dinga auna jinina." Fadil ya zaune a gefenta bayan ya gaishe ta ya ce. "Ba ni hannunki!" Inno ta watsa masa harara ta ce, "Kai Boka ni fa na gaji da wannan aurin hannun. Kaf zuri'armu babu mai ciwon hawan jini, sai da ubanka ya aba mini." Fadil ya sake ha e fuska ya ce. "Inno sauri nake fa." Ya arasa maganar yana ri o hanunta, Inno ba don ta so ba Fadil ya gama gwada mata hannu. Kasancewar ta ta a fama da ciwon hawan jini, yana shirin fita ya hango Laraba a kan gado tana sharar bacci. "Yarinyar can me ya hana ta zuwa makaranta?" Inno ta ata fuska don ta san yanzu sai ya tilasta mata zuwa. "Tun asuba ta ce mini jikinta yana ciwo ba za ta je ba, ka san jiya zanen zabuwa Mai gari ya yi mata. Ni ma kuma da ma ko ba ta fa a ba, ba zan bari ta je makaranta da anyan jiki ba." Fadila bai tankawa Inno ba ya arasa ya bu e firjinta, ya auko ruwa mai sanyi ya arasa ya kwara a kan Labara. A hargitse ta tashi cikin masifa ta ce. "Uban waye ya zuba mini..." Maganarta ce ta ma ale ganin Fadila tsaye a kanta, ya na e hannuwa a irji fuska babu walwala. Ta shiga murtsuka fuska tana kawar da kanta fege.