Sashe 36
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a akina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu." "Wace ce ita?" Ta wurga masa tambaya. "Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta." A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi da e ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan she aniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwa e mata ba ki ya fashe. "Kada ki sake danga ta mini Laraba da shai anu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan aci." Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga akin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu. Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da an Bishir suka sake komawa police station. "Alhaji na yi mamaki warai da na ji an ce case in naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira. Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina auke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba har sai an bi mini ha ina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu." Malam Shehu ya yi fi i-fi i cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na fa a, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan ga a. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni." Bala wanzan ya zaburo yana fa in, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu." Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana fa "Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani." "Ni dai tun da nake ban ta a yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana auke da cutar anjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni." Sergent in ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira. Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yalla ai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini azafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon anjamau. Har wasu suna cewa urajenta sun fito mini." uri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ora da cewar. "Dr kai ne likita, saboda Allah ina ha in cutar farankama da anjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ibana ake yi? Ni lafiyata alau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba." Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce. "A'a gaskiya babu ha i ma tsakanin cutar anjamau (HIV) da cutar farankama/ arambau (CHIKENPOX). Tun da ita cutar anjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin an'adam. Ta yadda za ta ba wa wayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun ha a da: arkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazza in da ya i jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon ma oshi, yawaitar fitowar uraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai aukar lokaci ba tare da ya ji magani ba." Cikin Alhaji Idi Naira ya ka a sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa. "To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar." Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba. "Amma ita cutar farankama/ arambau (CHIKENPOX), wayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya aukarta ta hanyar sha ar numfashin mai auke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazza i mai zafi, firgita, jajayen uraje masu urar ruwa, da matsanancin ayi. Mafita aya ce a kiyaye ha a mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da kar ar rigakafi." Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu ala a tsakanin cutar anjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gaba aya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin." Cikin Alhaji Idi Naira ya uri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya ha e fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata alau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana aro- aro a fuskar Alhaji Idi Naira. Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun ri o Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti. "Subhanallah! Hansatu lafiya?" Yaya Inu ya furta a razane. "Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo." "Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?" Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro." A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can in rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma da i ya ji saboda ya san arshen zance a ce ya kawo wani abin. Fadil ne ya auke su a motarsa ya wuce da su asibitin wararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye akin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi aurin aurensa. "Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba a ba ne." "Mene ne idan ba a ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka aurin aurena da Zuly zan tafi." Ba in ciki ya sa walla ta zubo wa Hansatu a ufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?" "Hansatu kada ki ata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a aura ne kawai yake ba ni warin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki a ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe akinsa sannan ya fice. Yana kai kansa zai fita a ofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su San ira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce. "Barka da fitowa!" Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa. "Ranka ya da e ya haka kuma?" Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara." San ira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin dag a cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi. "Ranka shi da e ni fa ka saka ni a duhu, wa annan in na mene ne?" Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman arin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai ba in jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar afar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce. "Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma aura mini aure za a yi!" Cike da shau i Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?" Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sau a mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya arasa. Hakan kuwa aka yi, Mai