Sashe 12
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
cim miki? Gaskiya Inno ki yi tunani." Inno ta yi wa Yaya Inu kallon she e ta ce, "Ka karanta mini aya ko hadisin da Allah Ya haramta wa tsohuwa aure! Yanzu Inusa sunnar Annabi kake arin da ilewa?" Yaya Inu ya yi shiru don zuciya ta gama zuwar masa wuya. Saboda dama tun farko jininsa bai ha u da Malam mai Yasin ba. "Yanzu Inno da za ki ce za ki auri mutumin nan mu da ba mu san asali da tushensa ba, babu wanda muka sani na shi fa. Abu aya ne fa ya ha a mu da shi taimakon da muka yi masa a airport, sanadin kamen da aka yi masa wanda har yau babu wanda muka sani a cikin danginsa. Gaskiya ko za ki aure shi sai mun san wani daga cikin danginsa." Baba Ibrahim ya yi maganar fuska a ha "Wallahi kai ka ma yarda ta aure shi, na rantse da Allah yadda na tsani yamusasshen tsohon can idan ban sheme shi ba Allah Ya tsine mini!" Yaya Inu ya fa a jikinsa yana karkarwa. Inno ta yi karaf ta ce. "To wallahi ku shaida duk wanda na ji ko kallon banza ya yi wa Malam sai na aga masa mamunana. Kuma dama na fa a muku ne saboda na fita ha inku na 'ya'ya atoh, don kada ku ji muna kashewa da binnewa ni da shi a aki ku fara yi mana an zargi. Duk da dai dama na fa a masa auren auko buta za mu yi." Inno ta sake kallonsu aya bayan aya ta cigaba. "To ku ban da abinku ace yau uwarku ta mutu da aure a kanta ba ya fi daraja a wurinku ba? Allah na tuba duk ha urin da na yi da ubanku tsawon shekaru bai wadatar ba? Wallahi da shi ne ma ba zai auki shekarun da na auka bai yi aure ba, a toh a yanzu na samu wanda zai ba ni walwala da kulawa gwargwadon farincikina. Da ku aura mini aure da kar ku aura duk aya, saboda yanzu zan tafi wurin Malam Liman ya zama waliyina shi kuma Malam Ladan ya yi wa Malam walicci ashafa mana fatiha." Shiru ta ji sun yi ba tare da sun tanka mata ba, ta kalle su rai a ace ta ce duka su fice mata daga aki. Nan take duk suka fice, Baba Ibrahim zai fita ya waigo ya ce. "Idan Allah Ya kai mu zan auki jininki da na Malam in sai na yo muku gwajin da ake yi kafin aure." Ha a Inno ta ri e ta ce. "Kai Iro ka fita a idona na rufe, uban me zan yi da wani gwaji ni da zan yi auren auko buta." Baba Ibrahim ya fita don ya lura Inno a fusace take, sai dai ya ci alwashin zai shawo kanta ya yi musu gwajin koda ba za ta ha ura da auren ba. Malam mai Yasin da yake ra e abayan katanga yana jin duk abin da suke fa a ya saki murmushi a fili ya ce. "Ashe na kusa arje amarci tun da na tsinci dami a kala. Na ci mai kyau na sha mai kyau, nan gaba kuma na kwashi ganima son raina." Ya aga kansa yana kallon tan amemen gidan gandun ya ce. "In Shaa Allahu har wannan gidan sai na mallaka, da ni kuke zancan dan ubanku." Yana jin motsin tafiya ya yi sauri ya fa akinsa ya saki labule. Tun da Laraba ta dawo gida ta ci alwashin idan sama da asa ce za ta ha e ba za ta sake zuwa makaranta ba. Kuma ko da gari ya waye, sai ta yi shirin makaranta kamar wacce za ta je da gaske, amma sai ta nufi cikin gari ta shiga yawace-yawacenta. Ta jima tana tunanin hanyar da za ta ullo wa Mai garu da su Malam Sule, a kan cin zarafin da suka yi mata amma har lokacin ba ta samu mafita ba. Sai da ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta kamo hanya ta fallo da gudu, a bisa tsautsayi za ta tsallaka wata hanya shi kuma wani matashi ya shawo kwana da motarsa ya an make ta. Laraba tana ganin haka ta sake bajewa a asa tana numfarfashi, a gigice matashin ya fito daga motar jikinsa sanye da uniform in NYSC. Laraba ta yallere ido a kaikaice bayan ta hango fitowarsa ta sake runtse ido tana ihu. "Wayyo Allah! afata da kaina za su alle. Wayyo Allah." Ganin yadda matashin ya gigice ya sa Laraba ta sake narkewa. "I'am very sorry dear!" Ya furta a gigice yana ago afar Laraba da ya ga ta dafa ta. Laraba ta yi shiru tana bin zara-zaran dogayen yatsun hannunsa, don dama ba ta fahimci abin da ya ce ba. "Lets go to hospital..." "Wayyooooo jama'a ya karya ni." Furucin Laraba ya sake katse shi. "Ki yi ha uri please mu je hospital, a ga me ya faru da ke." Kallon da Laraba take wurga masa da dara-daran idanunta ya sa tsoro ya kama shi, a ransa yake raya ko dai aljana ya bige? Yana nan tsugunne ya ji ta bushe da dariya. Ta sake zaro masa ido ta ce. "Kai an gaya maka gadon gidanmu suna zuwa asibiti? Mu za ka nuna wa boko?" Cikin Mahmud ya ka a, gabansa yana fa uwa ya ce. "Ku yi ha uri me kuke so." Laraba ba ta tanka masa ba, ta nuna masa wata katuwar bishiyar kuka da ke gefe. Ganin haka ya sa shi zaro ido, sai kuma ta nuna masa hanyar fadar Mai gari. Shiru ya yi don bai gane abin da take nufi ba, ta are masa kallo tun daga sama har asa ta ga bai yi kama da an garinsu ko ma otan garinsu ba ta ce. "Mu gadon gidanmu ba a iya biyansu da ku i ko kadara, idan har aka cutar da su. Sai dai a tambaye su abin da suke muradi a yi musu." Bakinsa yana rawa ya ce. "Don Allah fa i abin da kike so ko mene ne zan yi miki." Laraba ta ja afa da rarrafe ta ce, "Matso kaji don kada aljani Karbu ya ji ka." Yadda Mahmud ya matso da sauri kamar zai fa o kanta ya sa dariya ta kusa wace mata. Ta maze a ta fara yi masa ra a a kunne, da sauri ya zaro mata ido. Laraba ta gya a masa kai sannan ta ce. "Wallahi idan ba ka aikata son raina ba sai na saka aljani batoyi ya babbake ka, kuma na sa ya bi har gidan iyayenka ya one su urmus. Sannan ya ha a maka ba in sharri a garin nan, gara tun wuri ka tafi zan biyo ka ta cikin iska duk abin da za ka yi ina ganinka. Idan ka fa a ba daidai ba na hukunta ka ba." Kamar Mahmud zai yi kuka ya nufi hanyar fadar Mai gari da Laraba ta kwatanta masa, su Mai gari tun daga nesa suka fara hango shi don haka suka zuba masa idanu suna kallo. Mahmud yana zuwa ya taka har tsakiyar shimfi ar Mai gari ya fara bin su da kallo kamar yadda Laraba ta tsara masa, yana yi yana waige don kar ya yi ba daidai ba ta sa a one shi. Gaba aya a tsorace suke don sun yi tsammanin soja ne, San ira ne ya yi arfin hali ya ce. "Samari daga ina haka? Wa ya ba ku izinin taka shimfi ar ranka shi da e..." San ira bai gama magana ba, Mahmud ya auke fuskarsa da mari. Saboda tsoro har ji ya yi marin yana yi masa yaji-yaji a fuska. Lokaci aya suka shiga taitayinsu, cikin Mai gari ya shiga ka awa gumi yana keto masa. Malam Bukar ya yun ura zai tashi ya tafi, Mahmud ya buga masa tsawa. "Ni da kuka ganni ba mutum ba ne, na zo muku da wannan surar ne domin ku bil'adama ne. Idan na kwashe ku na tafi da ku a can ne za ku yaba wa aya za inta. An turo ni ne daga hukumar kare ha in aljanu, domin na zo na bi diddigin cin zarafin da aka yi wa 'yar cikinmu wato aljanun da ke jikin Laraba." Mahmud yana gama fa ar haka mutane wurin suka shiga rige-rigen gudu, Mai gari tsalle ya yi ya haye bayan San ira kamar wani an biri. Saboda tashin hankali San ira bai yi wata-wata ba ya damfara Mai gari a asa, ya na e babar rigarsa ya take afarsa ya bar wurin a guje. Mai gari yana shirin guduwa, taku aya Mahmud ya yi ya cafko rigarsa. Duk yadda ya so ya wacewa ya kasa, ga shi yawancin mutanen wurin sun gudu sun bar shi. Sai kawai ya ta are ya fashe da marayan kuka, ta asa kuma gudawa ta wace masa tana zuba. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam : *GIDAN LIKITOCI*