Sashe 13
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA SHIDA Wani irin yami ne ya kama Mahmud jin yadda Mai gari yake ta sakin gudawa babu autawa, ya an waiga bayansa cike da tsoro don su kansu da ace ba a tsorace suke ba, da sai sun fahimci tsoron da yake kwance a saman fuskar Mahmud. Mai gari hawaye da majina da suka gama wanke masa fuska ya dubi Mahmud ya ce. "Da wanne suna zan kira ka ranka shi da e, kuma cikin jinsinku ana iya kiranku da wannan sunan? Ka dubi Allah, ka dubi Muhammadur Rasulillahi ka yi mini rai ka yafe mini." Mahmud ya tsuke fuska ya ce. "Kada ka sake yi mini magiya, domin ni ma umarni na kar a daga sama, a madadin hukumar kare jinsin aljanu ta asa, sun wakilto ni na zo na tafi da kai da ta adiran mutanenka zuwa fadar majalisar inkin duniya ta aljanu. Amma tun da sun gudu da kai za mu tafi." Jin haka ya sake aga hankalin mai gari sai kawai ya sake fashewa da kuka, don ba shi da wata mafita da ta wuce haka. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya shiga yi wa Mahmud magiya, Mahmud ya tuna yadda suka yi da Laraba ya dube shi ya ce. "Za mu yi maka afuwa amma da shara i, shara in kuwa za ka ebo zabin gidanka guda hu u ka yanka su a kan waccan bishiyar." Mahmuda ya nuna masa wata bishiyar tunfafiya, San ira da ke la e a bayan katanga ya zaro idanu duk da ba da shi ake ba. Mai gari ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya ce. "Zabin banza ranka shi da e, wallahi ko rago ka ce yanka shi zan yi." Ganin zai yi gaba Mahmud ya ce, "Ba mu gama ba ai, shi wannan jinin da zai sauka a kan bishiyar tunfafiya shi zai goge laifin da ka yi a ofishin shugaban ungiyarmu. Saboda ka san haka nan ma aljanu zubar da jini suke yi, gangar jikin kuma ka taho mini da buhu zan kai a kwankwantsa namansu, a madadin naman jikinka da za a yi kwatsa-kwatsa da shi." Mai gari ya shiga gya a kai kamar na adangare. Ya alla wa San ira kira ya ba shi umarnin da ya je gida ya ebo zabi guda hu u. San ira ya yi wuf ya sake uya, don haka aka rasa wanda zai kawo wa Mai gari zabin da zai fanshi kansa sai Sahabi ne ya yi ta maza ya je gidan ya ebo. Kamar yadda Mahmud ya ba shi umarni, haka Mai gari ya arasa bakin bishiyar tumfafiyar ya fara yanka zabbin aya bayan aya har ya yanke su duka. Bayan Mahmud ya kar i zabbin ya cewa Mai gari. "Abu na arshe da zan fa a maka shi ne, ka kiyaye acin ran Laraba. Wallahi tun wuri ka ha a mutanen garin nan su nemi yafiyarta." Mahmud ya sake daidaita ba in gilashin idonsa ya cigaba. "Idan ba haka ba sai mun tsotse romon kanka, kuma daga yau duk abin da kuka ga Laraba ta yi to ba yin kanta ba ne. Duk wanda ya yi gangancin sake ta a ta zai mutu nan take, ko kuma mu auke shi mu yi ta azabtar da shi." Mahmud ya gama magana ya juya kansa a asa ya cigaba da tafiya, Mai gari yana ganin haka ya fice a guje ya nufi gida afar wandonsa ta yi sharkaf da gudawa. Ga mamakin Mahmud yana zuwa ya tarar Laraba ba ta nan, a tsorace ya ajiye an buhun zabbin ya yi sauri ya fa a motarsa ya fisge ta da gudu ya bar cikin dajin. Tun da Laraba ta hango shi ya tunkaro ta, take yata dariya tana da saman bishiyar dalbejiya har Mahmud ya ja motarsa ya yi gaba. Dirowa ta yi ta bu e buhun tana dariya har da ri e ciki, sai kuma ta yi shiru tana tunanin yadda za ta yi da zabi har guda hu u. Mai daban-daban ne ya fa o mata a rai, wani mai nama da yake can tsallaken auyensu, wanda ya jima da cewa yana sonta. Da sauri ta suri buhun kamar marar gaskiya ta shiga bi ta cikin gonaki ya har ta isa wurinsa. "Larabayyo 'yar Larabatuwa! Yanzu Laraba sai ki dinga guduna, saboda Allah mene ne aibuna?" Mai daban-daban ya furta mata cike da so. Laraba ta maze ta ce, "Mai daban-daban ka san shi so makaho ne, to kwanaki shi ya lullu e mini idanu a kan wani mutumi amma yanzu ba ya gabana kai nake so!" Wani irin da i ya mamaye shi don haka ya ce. "Kai amma na ji da i Laraba, wallahi yau da yar zan iya yin bacci yanzu fa i duk abin da kike so a wurin nan a yanka miki." Laraba ta yatsina fuska ta ce, "Eh wancan balangun za ta yanko mini ko yanka sha biyar ne, amma kafin nan ga zabin Inno nan ta ce a kawo ka gyara ka gasa mata." Jikin mai daban-daban har karkarwa yake, ya fara yankawa Laraba nama. Ya kalli wani yaronsa ya buga masa tsawa a kan ya kar i buhun hannun Laraba ya je ya gyara su. Bayan ya mi a wa Laraba balangun ta ce. "Na gode sosai masoyina mai daban-daban, yanzu wa annan zabin idan ka gama gasa su ka ajiye da daddare zan zo na kar a." Mai daban-daban ya amsa mata yana washe baki. Laraba har ta yi gaba ta waiga ta sake jan kunnensa, a kan kada ya aika zabin gidansu za ta dawo ta kar a da kanta. Mahmud bai yi tafiya mai nisa ba, isa bakin wani babban symbol in sabulun wanka da ke gefen titi. Ya ciro waya ya kira abokinsa Muddasir, wanda suka yi da shi za su ha u a adaidai wurin da ya kwatanto masa. Bugu biyu wayar ta yi ya auka. Daga can angaren ya ce. "Ga ni nan ina hango ka na kusa arasowa!" Daga haka Muddasir ya katse. Cikin asa da minti aya mai adaidaita sahu ya sauke shi. Sai da Mudassir ya biya shi ku insa ya arasa wurin motar Mahmud ya ce, "Mutumina ashe ka gane kwatancen!" Cike da damuwa Mahmud ya ce, "Allah ka yi mana tsari da auye, yanzu saboda Allah a nan za mu yi service?" Mudassir ya yi murmushi yana zama a sit in gaba ya ce. "Kai kukan da i kake yi, da muka samu aka canza mana school zuwa ta garin Gangaren dutse? Da ace an bar mu a garin Rafin gurgu fa? Yanzu ba ga su Haidar can ba suna fama." Mahmud ya saki guntun tsaki ya ce, "Yanzu ina za mu bi mu arasa garin Gangaren dutsen?" Mudassir ya nuna masa hanyar shiga garinsu Laraba, gabansa ne ya fa i amma sai ya basar don ba ya san ya sanar da Mudassir abin da ya faru da shi ya yi masa dariya. Ganin sun tunkari hanyar garinsu Laraba ya sa Mahmud ya ce, "Wai ina ne garin? Mun kusa zuwa ko da saura. Mudassir ya ce, "Mun kusa zuwa, da ka mi e za mu bi ta kan doguwar hanyar can har ofar gidan mai gari, ka san dole sai mun gabatar da kanmu a wurinsa tun da zama ne ya kawo mu. A hargitse Mahmud ya taka burki cikinsa yana ka awa, Mai garin da ya gama sakawa zawo a wando ne za su je wurinsa su gabatar da kanku? "Lafiya Mahmud?" Mahmud da gumi ya gama rufe shi kamar zai yi kuka ya ce. "Wallahi ba lau ba Mudassir." Ya arasa maganar yana yin parking in motar a gefen hanya, sai kawai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. Cike da shau i Mai Yasin yake kallon Inno jin amsar da ta ba shi, dangane da sanar da iyalanta a kan maganar aurensu. farinciki fal zuciyarsa ya ce. "Allah mai ha a jinin mumini da mumini, Allah ka ai ya san alkairin da yake oye da silar ha uwarmu a Saudiyya. Haka kawai na ji kin sake kwanta mini Inno, a gaskiya marigayi ya dace da mace." Inno ta saki murmushin jin da i kanta a asa, ita dai nutsuwar Malam da da an kalamansa wa and ta rasa a baya suna birge ta. Har a cikin zuciyarta tana jin ina ma tun tana budurwa, Allah Ya aiko mata shi cikin rayuwarta, da babu yadda za a yi ta yi rayuwa da tsohon mijinta da ko ka an bai iya soyayya da tarairaiyar mace ba. Mai Yasin ya saci kallonta da gefen ido ya ce. "Innota ko ba kya jin da in yabon da nake yi miki? Ko da za ki ji babu da i sai dai ki ji, amma Allah Ya sani aunarki ta jima da amfaruwa a cikin zuciyata." Inno ta ago ta dube shi ta ce. "Haba Malam, ai duk macen da ta yi dace da kai a matsayi mace ta more a gidan duniya da Lahira." 'An zo wurin, dama nan nake ta jiran mu araso.' Malam ya raya a cikin ransa, yana murmushi mai auke da manufa a ransa. Ya ance murya cikin yaudara da karuwanci ya ce. "Wallahi tun da na wayi gari jikin nan yake son dawo mini Inno, ga bakina salam babu da i kamar yawun mage. Nace ko zan samu koda kaza ko naman kasuwa?" Inno ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin yadda Mai Yasin ba ya gajiya da mur ushe cinyoyin kaza, amma da ta tuna a kullum ya ci kazar ya kuma shar i romonta ara samun lafiya yake sai ta ce. "To Malam ka ga dai yaran nan azu kusan baram-baram muka rabu da su dutse a hannun riga, kuma dama mai arin sayo maka Iro ne. Yanzu dai ban san cikinsu wa zan