← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 69

Sashe 31

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA SHA BIYU Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gaba aya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Mi ewa ta yi ta nufi hanyar ban akin tana zuwa ta ji yana fa "Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada." Sai ya sake arkewa da kuka. irjin Indo ya buga da arfi, ta an buga ofar ban akin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?" Daga can cikin ban akin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo." "Cikin ban aki fa Mai gida?" Ta tambaya da mamaki. Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta fa a ban akin gabanta yana fa uwa musamman da ta tuna bai ta a yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a akin ba ta sani ba. "Mai gida lafiya kake kuka a ban aki?" Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne. "Indo na ha u da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana." Muryar Yaya Inu ka ai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Me ya faru dai yanzu?" Yaya Inu ya zauna a kan wani an dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce. "K u je ku kori yara aki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni akina. Saboda su kansu jijiyoyin afafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba." Jin haka ya sake aga hankalin Indo, ta ja afafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke inkin mahuci ta furta. "Mai gida fa babu lafiya Hansatu." Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawa e, kowa ma fama yaka da rashin lafiya." "Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara aki mu je mu auke shi mu mayar da shi akinsa." Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu auka mu kai aki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Da sauri Hansatu ta mi e, kowacce ta shiga arin tura yaranta aki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya ha a kai da gwiwa. Abin da ya sake aga hankalin matan nasa, ganin hawaye sha e-sha e a fuskarsa yana ambaliya. "Mai gida! Wai me yake faruwa haka?" Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta sha e can ciki ya ce. "Ku yi tara-tara ku kai ni aki. " Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai iba ba, ya sa su ukun suka ha u suka aga shii suka yi aki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana sa a da warwara a cikin ranta. " azu gabanin zan shigo gida na ha u da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!" Yaya Inu ya arasa maganar yana banka e zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa. "Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?" Hansatu ta fa a a ru Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi." Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya auka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can angaren ya ce. "Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai." Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa arfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zu e?" "Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa." Kalaman mai maganin kenan da suka ara wa Yaya Inu warin giwa. Larai da ke ri e da ha a ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya." Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?" Larai ta murgu e baki gefe ta yi asa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. ila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta sa on Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..." "Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa." Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji. Kalaman su Larai ba aramin aga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune irjinsa yana bugawa ya ce. "Na rantse da girman Allah ban ta a aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi." Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron ta a ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta. Kuka Yaya Inu yake iya arfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ago mata hannu. Ba aramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba aramin tashin hankali ba ne. A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?" Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu." Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani angaren ya fara ba ta tsoro. "A'a kai ne mai fa a aji ai, tun da kai rana ta wacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya fa a." Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya ri o hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke ka ai ce ba ki guje ni ba a cikinsu." Hansatu ta yi wa Yaya Inu uri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce. "Ai wannan kalaman da kake fa a na fatar baki ne ranka shi da e, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka ta a sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida." Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lullu e shi, Hansatu ta cigaba ebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce akinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da yar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara da i yana miyagun mafarkai kala-kala. Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba aramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya ha e mata goma da ashirin ga halin da an Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye aramin asibitin gwamnati auyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa arin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya bu e idonsa. "Sannu Sale, ya jikin naka?" Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?" Ya gya a masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai
Chapter 31 · 0% Book details