← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 69

Sashe 50

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sannan ya ora. "Kai Jafar ina maka kallon mai hankali ya aika yi haka ta faru?" Kai tsaye Jafar ya nuna su Dada murya a sha e ya ce. "Baba a tambaye su ni kaina sama ta ka na ji abin da suke fa a." "Ba ni da an uwana ka aryata ba, uwarka Saro da ubanka Mamman su ka aryata ka ji Jafaru." Dada ta furta tana wurgawa Jafar ta uwa. "Ka shiga taitayinka Jafar? Idan na kuma jin magana mara da i daga bakinka sai ranka ya yi mummunan aci, ke Uwani shin yau wannan abin ya ta a shiga tsakaninki da Jafar ne?" Baba Rufa'i ya jefa mata tambaya. Zuciyar Uwani aya ta share walla ta ce, "Wallahi ni kam azalce ta kai ni akin Ya Jafar, ashe Lawan yana la e a bayana ban san ya biyo ni akin ba." Cikin ha in baki duka suka ce, "Waye Lawan? "Mijin Fanteka ne." Uwani ta fa a cikin kuka. "Ashe ba ki da hankali Uwani? Ashe sakarcin na ki da ake fa a gaskiya ne? A ina Lawan in yake kuma an gidan uban waye a auyen nan? Da har zai shigo cikin gida ya bi ki aki." Baba Yunusa ya yi maganar rai a ace. "Ban gan shi ba Baba, duk neman da na yi ban gan shi ba ma azu, kuma wallahi ganin idona ya fito daga akin ya Jafaru. Sororo suka yi suka gagara gane kan maganar Uwani. "Shi Lawan in ne zai ata a gidan kamar wani zobe? Kin san me kike fa a kuwa Uwani?" Cewar Baba Mamman. Ganin duka ba su fahimci inda maganarta ta dosa ba ya sa Dada ta ce. "Lawan in da Uwani ke fa a ba kowa ba ne fa face zakaran da take kiwo, ko ba Lawan mai wake-wake ba Uwani?" Da sauri Uwani ta gya a kai. "Ba maganar zakara muka yi miki ba, muna magana ne akan tsakaninki da jafar." Baba Yunusa fa Jin haka ya sa Uwani ta kwashe duk abin da ya shiga tsakaninta da Jafar ta fa a musu, shiru duka suka yi Dada ta dubi Na madina ta ce. "Yaya wai haka ne abin da ta fa a? Don gaskiya shedar zir haramun ce kar Mamman ya fusata ya ce mun yi wa ansa azafi ya kaimu kotu, al ali ya yanke mana bulala tamanin mu shiga uku." Jikin Na Madina ya yi sanyi don shi kasan ya san zargin ne yake yi idanunsa ba su gani ba. "Ni dai Allah Ya sani ban kama Jafaru da Uwani turmi da ta arya ba, amma na ji wa ansu kalamai da suke yi a cikin akin Kulun. Don Allah me zai sa su ke e idan ba warware mutumcin sunna suke ba?" Sai a lokacin iyalan wurin suka fahimci gaba aya inda maganar su ta dosa. "Amma dai Yaya ka ci zarafin zuri'ata, yanzu saboda Allah wacce iyayya kake yi wa Jafaru da Uwani da za ka nemi ka ha a su da hali irin ta'adar Iron Alto, ni dai ku zama shaida ta daga yau ba zan sake ha a inuwa aya da Yaya Musa ba." Dada ta yi maganar cikin kuka, ta mayar da kallonta wurin su Jafar ta ci gaba da cewa. "Ban da arfin al awari ma me zai ha a Uwani da Jafaru? Yarinya kyakkyawa kamar Uwani a ba ta ansanda, ansandan ma kamar Jafar mai zuciyar masifa. Ni tsorona ma kada watarana Uwani ta yi masa laifi ya sa bakin bindiga ya bindige ta..." "Allah ya tsare ni, ni kuwa me zan yi da Uwani wallahi ko a afa aka aura mini ita ba zan ja ba, kai ko abokina ba zan yi wa hanyar aurenta ba, haka kawai a ce na yi sanadin auren azama kamar Uwani." Jafar ya fa a a azance kamar zai yi amai. "Idan kai ba ka so ba ai tuni al wari ya ba ka aurenta Jafaru, shafa Fatiha ka ai ya rage muku. Amma fa wallahi fa i kanka tsaye Jafaru azantar uwani tun da na zo duniya ban ta a ganin azama irinta ba." Jin tonan asirin da Dada take mata ya sa Uwani tura ba ki gaba. "Rigar mama wannan Uwani ba ta san ta canza ba sai dai idan na tilastata ta sauya, ban da ma Allah Ya kawo mu zamani yaushe yarinya za ta fara saka rigar mama a gaban iyayenta? To haka take zama da tsamin hammata, rannan ina kwance a saman kaina na ji tsami ya cika min hanci wallahi ina dubawa na ga ashe an diras da kanfanta ne a ajiye. Ni ina tsoron ma kar a aurar da Uwani ta shafa wa Jafaru kwarkwata, don wallahi ko gorin kwarkwata aka yi wa Uwani sai haka. Amma dai tun da Hajiya Saro (Mahaifiyar Jafar) ta daina azanta Uwani ma za ta daina, don bara war haka sai da na ro a wa Uwani addu'ar yayewar azantar nan a Harami." Dada ta mayar da kallonta wurin su Baba Rufa'i sannan ta cigaba. "Yanzu dai ba za mu tashi daga wurin nan ba sai mun kammala maganar yaran nan. Kun dai ga yadda Uwani ta zama budurwa ni tsorona ma kada ta fara ba on wata a gabana na shiga uku..." "Subhanallah wannan wanne irin mummunan fata ne haka Kulu? Yanzu saboda Nasara ya gama wanke wa su Mamman hannu a ka sai su bar yaran nan haka?" Jafar ya saki murmushin takaici don shi gani yake duk sokiburutsun tsofaffin ne. "Don Allah ku dubi fuskar Jafaru washar yadda yake sakin murmushi, ko wannan miskilancin da yake yi fa aure yake so, kuma yanzu ya samu an soso masa wurin da yake yi masa ayi." Na Madina ya arasa maganar yana sakin murmushi. Baba Rufa'i ya yi gyaran murya sannan ya furta. "Dada dama ba mu i ta ku ba, amma gaskiya shekarun Uwani sun yi anta a aurar da ita yanzu Ina laifin ta gama sakandire ma..." "Sakandi me? Kana nufin zan zauna ina ganin Uwani a gabana har tsawon shekara biyar? Wallahi da kunci amanar zumunci, yanzu saboda kun ga asa ta lullu e idon mahaifin yarinyar nan shi ne za ku watsa mata asa a ido. Kaico mutuwa mai yankan auna. Allah Ya ji anka Umaru, ni na san da Umaru ne ba zai ta a yi wa bayanku haka ba." Shiru suka yi Baba Mamman na shirin magana Na madina ya katse shi, "Amfanin me karatun bokon zai yi mata? Aure fa shi ne sunnar Ma'aiki. Yanzu Dada ba ga su Safare nan ba kowacce tana akinta da 'ya'yanta, ina ce firamare kawai suka yi. Ko kuma mu iyayenku da ba mu yi yi bokon ba sai a ce ba mu ji da in rayuwar aure ba?" Dada ta ware hannuwa cikin gamsuwa ta ce, "Gane mini hanya Yaya, so suke yadda fitsararrun yaran can suka rasa miji ita ma ta gandame mini a gabana." "Dada domin fa mu inganta rayuwar Uwani muke son mu tsaya mata ta yi karatu kamar yadda sauran yara suka yi, amma ba don wata manufa ba. Don Allah ku fahimce mu Uwani yarinya ce, har yanzu fa ba ta cika sha biyar a duniya ba duk fa girman jiki ne." "Ni dai Baba kawai a aura mini Ofisana, kar na je Furaira ta riga ni gabatar da kanta a wurinsa. Don wallahi Furaira masifar son shi take. Ka ga ni ma sai na dinga gayu irin nasa, Allah ko su Fanteke sai sun zama 'yan gayu..." Da sauri Jafar ya katse Uwani. "Ke ba na son shashanci da rashin hankali an gaya miki ni sa'anki ne? Tun wuri dama ki nemi mijinki don ni tuni akwai wacce zan aura a Lagos..." "Lagas? Yanzu Jafaru ka rasa wacce za ka auro sai edarun Lagas, wallahi ni kam dole na je Zariya na samu Sa'idu." Dada ta fa a cike da damuwa. "Jafar wannan da an al awari ne da na ulla shi shi tun ranar da Uwani ta zo duniya, kamar yadda ka sani mahaifinta ya rasu tun tana ciki sakamkon hatsarin da ya yi. Ba ta ta a sanin fuskar mahaifinta ba sai mahaifiyarta. Tausayinta ya sa na auki al awarin aura maka ita matu ar kuka kai munzalin aure, tun da a lokacin ba ka fi shekara goma sha uku zuwa sha biyar a duniya ba. Daga kai har ita mu muke da iko a kanku babu wanda ya isa ya bijire wa umarninmu." Baba Mamman ya yi wa Jafar jawabi fuska a ha Dada ita da na Madina suka washe baki cikin farinciki ya ce, "Wallahi ka jima ba ka faranta mini rai irin na yau ba Mamman." "To yanzu dai duk ba wannan ba, abu aya zan yarda da shi. Ba zan zuba wa Uwani ido ba a yi mata aure ba har nan da shekara biyar ba. Watan Maulidin nan me zuwa ne bikin su Shukra ko?" Baba Mamman ya gya a mata kai. "Nan da watan maulidi nake son a aura musu aure idan ya so nan da wani lokaci sai a yi maganar tariya. Ko dai mutuwa na yi kafin lokacin na sauke nauyin da muka auka, ko ba haka ba Yaya?" Dada ta furta tana kallon Na Madina, cikin gamsuwa ya amsa mata. Duk yadda su Baba Mamman suka so shawo kan Dada don aga maganar fir ta i amincewa. Don haka suka ha ura suka tashi daga taron, Jafar tun ba su kai ga tashi ba ya fice fuuu daga akin. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya saki murmushi ya furta. "Ja'irin yaro wannan doron da ya yi yana yin aure zai mi e, na san yau kwanan farinciki zai yi yoo aure wasa ne." Dada ta bushe da dariya. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [11/06/2024, 13:08] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 50 · 0% Book details