← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 69

Sashe 49

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHIDA Dada ta zuba musu ido ganin yanayin da Uwani take ciki ya sa ta aminta da kalaman an'uwanta, ta san dai ba zai ta a yi musu arya ba. Runtse idonsa Jafar ya yi yana fesar da iska mai zafi, ya bu e idanunsa da suka rine jawur kamar gauta ya sauke su a kan malam Na Madina. A fusace ya arasa gabansa ya cukwikwiyo babbar rigarsa ya ri e shi wuri aya rai a ace ya furta. "Wallahi ba don ina duba tsufanka ba, da yau sai na bambamce maka tsakanin zuma da ma aci." Jafar ya sake shi sannan ya wuce akinsa, saboda tsoro tuni malam Na Madina ya yi mutuwar tsaye. Dada ta bi bayan Jafar da kallon tsoro baki a sake. "Yaya an ya Jafaruna ne ba aljanu ne a kansa ba..." Kuka ya katse maganar da Dada take yi. "Sharrin waya ce Kulu, na sha fa a miki wannan aikin amarar ba zai haifar da samun a mai ido a cikin zuri'armu ba. Yanzu wa gari ya waya? A ce Jafaru bai san Kano garin Musulunci ba ne? Ya auka rayuwar da yake yi a Legas ita zai yi a gidan nan. Kin ga dai abin da ya faru a gabanki. Da fa dukana zai yi, kaico rashin haihuwa ne ya ja mini haka." Na Madina ya fashe da kuka, Uwani da ke gefe ko a jikinta ta shige aki ta ci gaba da sauya kaya. Don ita hakan da ya faru ma da i ta ji, ko ba komai ta san Jafar da zuciya ba lallai ya sake shiga sashen Dada ba sai bayan kwana biyu, ballantana ya hora ta a kan laifin da ta yi masa. Tana gama sauya kaya ta fice a nan harabar gidan ta ga Lawan da matarsa Fanteka, 'ya'yan ta ibo ta yi hanyar keji da su uwar ta rufa musu baya. Sai da ta dawo ta ga Lawan yana tsince-tsince a wurin akuyoyinta. "Kai dai Lawan ka cika an kishiya ri on mai ha uri, wallahi da kiwon ka aka ba ni da ka ja mini zagi a ce na bar ka da yunwa." Uwani ta yi maganar tana arin kama shi, Lawan ya yi tsalle zai dira a kan katangar gidan Baba Isuhu da yar ta kama shi tana sakin murmushi. Kai tsaye sashen Dada ta wuce tana shiga ta ci karo da Jafar ya fito auke da jaka a kafa "Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Yaya ka ga yaron nan saboda ya san tsiyar da ya shuka fita zai yi ya bar mu, ni dai wallahi Sa'idu ya cuce ni duk wannan abin da yake faruwa Sa'idu ne sila." Jafar bai bi ta kan su Dada ba ya fice daga gidan har yana hanka e Uwani. "Kulu Allah Ya ba mu alheri, wallahi Jafaru ba zai yi mana turun jeka ka mutu ba. Ya shuka bishiyar tsiya mu da ba mu ji ba, ba mu gani ba mu girbe masa." Malam na Madina ya sake jan jaka ganin haka ya sa Dada ta ce. "Ka jira ni yanzu zan kira Inusa dole ya tara mini 'yan'uwansa a gidan." Dada ta yi maganar tana fa awa aki domin auko wayarta. "Inusa a yanzu ba sai gobe ba ka tara mini 'yan'uwanka, wallahi idan ba haka ba zan bar muku gidanku na shiga duniya. Kuma ku yi gaggawar kiran Jafaru ku ce ya dawo don zaman nasu ne, shi da Uwani ne suka ulla tsiyar da bakina ba zai iya furtawa ba." Daga haka Dada ba ta sake cewa uffan ba ta kashe wayarta, da kashe wayar babu jimawa Baba Yunusa ya sake kiranta, Dada na auka ta ce. "Yunusa wai wa muke yi wa Sallah da azumi?" Daga can angaren Baba Yunusa ya ce. "Allah." Dada ta sake ha e fuska kamar yana ganinta ta ce. "Da ma saboda na fita ha inka a matsayinka na babba shi ya sa na kira na sanar da kai, wallahi idan ba ka ha o mini kan 'yan uwanka ba sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba." Dada za ta katse da sauri Baba Yunusa ya ce. "Shi kenan Dada ga mu nan zuwa yanzu In shaa Allah." Ta amsa masa sannan ta katse wayar, sai da ta lallami Na Madina sannan ya mayar sa akwatinsa. Falon tsit ya yi da ka kalli fuskokinsu ka san kowanne yana cikin damuwa, Baba Yunusa ne ya yi arfin halin cewa. "Dada gaba aya ga mu mun hallara." Jafar tun da ya sunkuyar da kai asa zuciyarsa ke tururi, Uwani na ra e a gefe sai raba ido take kamar osan sadaka. Ganin haka ya sa jikinsu ya sake yin sanyi, don sun tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa. Sai da Na Madina ya kalli Jafar da Uwani sai ya sake fashewa da kuka, ganin haka ya sake raunata zuciyar Dada ta ja gefen mayafi ta fara sharce hawaye sannan ta fara magana. "Gaba ayanku na tabbata idan za ku yi mini shaidar Allah da Annabi, za ku yarda da abin da zan fa a." Suka amsa mata cikin ha in baki. Dada ta ci gaba da ce wa. "Wallahi anin mahaifinku Sa'idu ya cuce ni cutar ta har abada, amma ya je ba ni ya yi wa ba zumuncin Allah ya yi wa kuma ranar gobe iyama sai igiyar zumunci ta zarge shi. Ni dai ba zan shiga tsakaninsa da Ubangiji ba amma sai mun tsaya a gaban Ubangiji ni da shi." Sororo gaba aya suka yi hankali a tashe suna kallonta. Baba Yunusa ya ce. "Dada me yake faruwa haka ne Baba Sa'idu fa? Baba Sa'idu da ya zame mana bango madafa kuma majingina, mutumin da ya maye gurbin mahaifinmu..." "Inusa wa ya samar maka aikin Sojan nan? Kuma wa ya samarwa an'uwanka Mamman aikin ansanda, shi kuma wancan Rosofti?" Dada ta Katse shi. "Duka Baba Sa'idu ne ya samar mana Dada wani abu ne ya faru?" Ya tambaye ta a sanyaye. "Aikin amarar ba shi ya kai Jafaru Lagas ba?" Duka suka amsa mata, jin furucin Dada ya sa Jafar ya ago a fusace. Dada ta cigaba da fa "Silar haka ai ga shi muna shirin samun Iron Alto na biyu a cikin gidan nan." Jin kalaman Dada ya sa gaba aya suka auki salati hankali a tashe. Baba Isuhu ya wurga wa Jafaru wani mugun kallo cike da yama, yana ri e da ha a hannunsa aya kuma na ri e da mai sunan Malam. Sai da akin ya lafa da hayaniyar da ake yi sannan Na Madina ya ce, "Wallahi ba tun yau ba shi ya sa magana ta a kullin yaran nan a aurar da su, amma da yake nasara ya hure muku kunne sai ku ce yara sai sun yi karatu. Yanzu dubi garsamemen ato kamar Jafaru a ce bai yi auren fari ba, ni wallahi ina kamarsa da Allah Ya ba ni haihuwa da na yi 'ya'ya uku. To yanzu me ya fi wannan haushi? Wa ya sani ma a Lagas in ko 'ya'yan edarai ne suka suke bu e masa idanu, yake wartar aya bayan aya yana sakayewa a gefe. Ga shi nan yanzu ai ya gagara ha uri ya ja Uwani akin Kulu suna watsa wa sunnar Ma'aiki asa a ido." Kamar ha in baki gaba aya mutanen akin suka furta. "Innalillahi Wa'inna ilahirraji'un." Duk budurin da ake yi ko a jikin Uwani ita babbar damuwarta ba ta wuce ta samu ta tsira daga horon Jafar ba, don ta san yadda ransa ya aci idan ta shiga hannunsa sai Allah. Ran Jafar ya kai matu ololuwar aci don haka a zuciye ya buga tsaki ha e da mi ewa zai fice daga akin. "Wallahi matu ar Jafaru ya fita daga akin nan Mamman sai ka bi anka, tun da ni da an'uwana ba mu isa da shi ba." Dada ta yi furucin rai a ace. "Koma ka zauna Jafar." Mahaifinsa ya furta murya a dashe saboda acin rai. "Daddy wai ba ka ji me wa annan mutanen suke fa a ba ne? Wannan wanne irin abu ne. A ce a rasa azafin da za a yi mini sai na zina, kuma na rasa da wa zan yi sai Uwani yarinyar da azanta ta samu gurbin zama a ilahirin jikinta..." Na Madina ya katse Jafar sakamakon rarrafowar da ya yi, ya dafa afarsa. Kwanciya na Madina ya yi a gabansa sannan ya fashe da kuka. "Don Allah kada wanda ya hana Jafaru ya rufe ni da duka, dama azu ka so dukana to ka saka bindiga ka tashi kaina a kan wa annan magangun da kake fa a mana ni da 'yar uwata." Na madina ya furta wallah na zuba, idan ka ga yadda yake rusar kuka sai ka rantse da Allah wani abin aka yi masa. "Ba na son sakarci ka koma ka zauna Jafar." Mahaifin Jafar ya buga masa tsawa. Sai da ya ha iyi yawu mai aci sannan ya koma ya zauna yana wurga wa su Na Madina harara, ya sunkuyar da kai asa cikin acin rai. Baba Inusa da kansa ya arasa ya tashi Na madina ya koma mazauninsa sannan shi ma ya koma ya zauna. Baba Rufa'i ya gyara zama, sannan ya fara magana. "Dada duk mun ji abin abin da yake faruwa amma don Allah ku gafarce ni a maganar da zan fa a." "Kayya Rufa'i muke wa Ubangiji laifi ma ya yafe mana, ballantana an'adam abin banza." Cewar Dada. "A iya sanin tarbiyyar da yaran nan suke da ita ba mu ta a tsammanin haka za ta ta a faruwa ba, sai dai kuma a ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Dada ta jinjina kai jin kalaman Baba Rufa'i yana shirin ci gaba da magana ta katse shi. "Ai albasa ce ba ta yi halin ruwa ba Rufa'i, wai a rasa wurin da za a yaye wa sunna labulen albarka sai a akina. Kaico ni Kulu." Sai da Dada ta yi shiru
Chapter 49 · 0% Book details