Sashe 28
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA SHA "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ke! Wane irin iskanci kike yi haka? Ba za ki cika ni ba, sai na sa a miki." Yaya Inu ya yi kalamansa yana kokawa da 'Yar gwal amma fir ta i sakinsa, ta adandane shi sosai kamar mayen arfe. "Ke yarinya, ba ki da mutumci ashe ban sani ba, ba za ki sakar mini yaro ba." Inno ma ta yi maganar tana arasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar etarsa, saboda dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa. Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya arfinsa da niyyar ya war o ta asa, sai ta ma ale shi am a madadin 'Yar gwal ta fa o sai wata wawiyar tusa ce ta wacewa Yaya Inu. "Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?" Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki aya kuwa? Kamar muna asar kafirai za ki adandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ago tana bin sa da wani irin kallo, sai kawai suka ji ta saki jiki ta fa i yaraf a asa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana ka e riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka. "Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?" Furucin Baba anladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, anladi ya ago ya dubi Yaya Inu ya ce. "Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." anladi ya arasa maganar yana aukar 'Yar gwal ya shige aki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce. "Inusa yaushe an'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?" Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin iri- iri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne anladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba." Daga cikin akin anladi ya ce. "Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini age, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke yashi na raya?" 'Ha a na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tir ashi, wannan anladin ai ya gama tashin kaina.' Mai Yasin ya raya a ransa. Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta. "Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta aci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa." Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga aki. "Inno azu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..." "Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta auko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?" Inno ta katse shi tun bai arasa magana ba. "Don Allah Inno ki bari na dire maganata." Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta ora daga inda ta tsaya. "An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban ta a haihuwar zabiya ba." A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce. "Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama sa on Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka auki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana mi ewa, har za ta shige uwar akinta ta waigo ta ce. "Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai ora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya ha e masa. Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce. "A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna bu atar ayan bayan aya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya an muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud uri da ido ya ce. "Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?" Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi da e, sai dai idan mai kama da ni ka sani. " Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, aya daga cikin aliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar asa (NYSC)." A fili Mai gari ya fa a fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar asa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana ha e rai ya ce. "Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta asar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a asata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce. "Ku dube ni nan, bautar asa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke mi afa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku. "Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi da e. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya arasa maganar yana mi a masa takardar. Gaban Mai gari ya fa i, da ya ga ya mi a masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya ri e takardar yana an matse idanu ya fara karantawa. "Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko wa annan jajirtattu kuma hazi aliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar asa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tu uru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ago yana muzurai, daga can asa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce. "Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani orafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntu a ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya sa a masa. Idan da hali ma ya ci tararsa." Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka auki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Ha a gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce. "Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura alibi NYSC wato bautar asa, ana nufin ya hidimtawa asa ta hanyar bun asata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani arin horo ne, da alibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi da e, idan na fa i ba daidai ba." Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ace ya nuna Shazali ya ce. "A kananna e shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba ne?" "Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya fa a fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka fa a..." Da sauri Mai gari ya katse Mahmud. "Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da