← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 69

Sashe 30

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sayi magani." Mutumin tun da ya yi tsaye yake arewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya fa i. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa. "Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa." Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya arasa maganar yana mi a masa wata roba arama ya ora da cewa. "Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta arato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan umi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa." Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro ku i ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa. "Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka wa annan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya wa anda suka san kansu ka saya..." A she e Yaya Inu ya katse shi. "Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin dan o? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsu e jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar ku ina nake saya babu wani ato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina." Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace. Yana zuwa akinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya fa a masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A angare aya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya auki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya fa a ban aki a guje har yana ari da kwanuka. irjinsa ne ya buga da arfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa. Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya. Littafin ku i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam : *GIDAN LIKITOCI*
Chapter 30 · 0% Book details