Sashe 63
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA UKU Jin yadda jikin Uwani yake karkarwa ya sa Jafar ya kwantar da ita a jikinsa ya sa hannu ya fara bubbuga bayanta, nan take idanunsa suka yi jawur saboda acin rai. Ya dubi mutumin murya a dashe ya furta. "Ka san wa ka ta a kuwa? Ka san wanne irin kuskure kake yun urin aikatawa. Wallahi sai na nuna maka bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Jafar ya arasa maganar yana yun urin cire Uwani daga jikinsa, cikin kuka Uwani ta furta. "Tsoro nake ji Ya Jafar don Allah kada ka sake tafiya." Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya ri e hannunta suka fara tafiya rai a ace, ganin haka ya sa Alhajin ya zuba a guje ya fa akinsa ya datse ofa. akinsu suka wuce sai da Jafar ya sa key ya bu e suka shiga, ya kai ta kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. "Ki jira ji yanzu zan dawo." Fuska da hawaye Uwani ta furta. "Ya Jafar kada ka tafi ya shigo mini." Sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya an hura mata iska ya furta. "Ba abin da zai faru da ke yanzu zan dawo kin ji." A hankali Uwani ta gya a masa kai sannan ya fice. akin Alhajin ya koma ya yi bugun duniya ya i bu ewa, shi kuwa Alhaji tumbin ku i jin ana buga ofar akin abokinsa da arfi, ya sa ya ara wa tashi ofar key sannan ya wuce ban aki a guje jiki na rawa ya uya. Ganin ba shi da niyyar bu ewa ya sa Jafar ya zaro waya ya danna lambar DPO in unguwar Zoo road, da yake abokinsa ne. Nan take ya sanar da shi abin da ya faru tsakanin Uwani da Alhajin. Sannan Jafar ya sauka asa ya sanar da ma'aikatan reception abin da yake faruwa da kuma akin da Alhajin yake ciki. Wata mata da ke gefe nan take ta furta. "Kai malam Allah Ya yi maka albarka. Wallahi ni ma jiya da dare na an fita unguwa na dawo haka wani ya dinga mini an kira, da na shiga aki har buga mini ofa ya yi ila ma shi ne." Jafar ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Daga yau ai ba zai ara ba." "A toh ai wasu mutanen gani suke idan suka ga mutum ya kama hotel kowa ma an iska ne, Allah Ya kyauta." Ba a auki lokaci ba sai ga motar 'yan sanda ta araso, lokacin da suka je bakin ofar Alhaji sai da yar ya bu e musu ofa. Har asa ya tsugunna yana ba wa Jafar ha uri amma fir ya i sauraronsa, yaran D.P.O bayan sun saka masa ankwa Jafar ya ce su wuce da shi zai zo daga baya. A wurin da ya bar Uwani a nan ya koma ya same ta, fuskarta ta kumbura saboda kuka. Tana ganinsa ta yi zumbur! Ta mi e tsaye. Bai kula ta ba ya koma can gefen gado ya zauna ya dafe kansa, wani irin aci yake ji a ma oshinsa ya ago murya can asa ya ce. "Ya aka yi mutumin nan ya biyo ki ke da na bar ki a aki?" Zuciyar Uwani aya ta fara masa jawabi. "Ni fa kasan afata ba ta saba zaman wuri aya ba, gajiya na yi da zama shi ne na fita can asa na sha iska. Da na dawo sai na rasa akin nan, bisa tsautsayi na fa akin wani an iska..." Uwani ta kwashe komai ta gaya masa amma ba ta gaya masa irin azabar da ta yi wa Alhaji tumbin ku i ba, ta dai ce masa Allah ne ya wato ta bayan ta fito wannan Alhajin ya biyo ta. Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin acin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da wa annan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da fa a tamkar zai rife ta da duka daga arshe ya fa a toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ace yake ya furta. "Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta auka ta fa a ban aki kafin ta fito ha r Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya an kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba. Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ofa yana fa "Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ofar haka ya yi ta mur awa ta i bu uwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta an waiga ta ce. "Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" La was Jafar ya yi ya zauna a asa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya." Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya." "Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan." ewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta su uce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga akin, Uwani ta saka kayanta sannan ta ha a ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka. Ba su auki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya arasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki. Lokacin da su Uwani suka arasa gida mommy ta rako awarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana fa "Ya aka yi Jafar?" Jafar ya an sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma. awata wai kar dai ra e-ra in da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya fa i, ta an basar tana iro murmushin ya e ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta ro e shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san a na kowa ne awata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wula antaccen kallo ta furta. "Ban da ta arewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawa e." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ari biyar suna sa su a aki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da arshe da ta jefi Uwani da su ba aramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A an tsawace Mami ta ce. "Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da wallah. Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce. "Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai ago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta. "To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na kar o magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce. "Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira. Mami na shiga sashensu ta ha o wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata fa a. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin. Cikin wankin da Mami ta ha o wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin da in rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin