← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 69

Sashe 18

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA TAKWAS Duk maganar da Inno take yi babu aya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa da ya ji tana ibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana bugawa ya dubi Inno ya ce. "Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?" Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi yana in sayar da shi, mutumin arshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi." Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce. "Na jima ban ci gashin nama da ya yi da i kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne ka ai zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..." Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi ha e da fa "Malam lafiya kuwa?" Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba kafin a yanka." Mai Yasin yana gama fa ar haka ya sake arkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya fa a, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta ta a tsammanin zai fa i haka ba. "Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na auki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai gaba aya ba." Mai Yasin yana ha a ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai auke da manufar za mu ha u da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar aramin yaro ya sake arkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya cika akin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya mi e yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana yun urin ta e masa afarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai tanka musu ba. Zazzafan zazza i ne ya rufe shi don haka ya shige akinsa ya ja bargo ya rufa, domin kusan a asa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka. Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa." Daga can angaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?" Baba Ibrahim ya ji da i yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi ha in kai a game da bu atar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ofar sannan ya ce. "A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna." Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin akin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce. "Inno lafiya? Me ya samu Malam?" Inno ta an canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi uri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba. "Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa." Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma an'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya. "Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai." Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce. "AlhamduLillah! Ha a ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa ha uwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!" Baba Ibrahim ya ago ya an dube su sannan ya cigaba da cewa. "Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da aya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba." Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya ha e rai, Inno ta dube shi she e ta ce. "Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa fa a, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka kar o kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune alau?" Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa alau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba. "Wallahi Inno ba ni da wata ala a da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika auke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne an'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu wayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma wa annan wayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu auke da matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression) sai uwa-uba cutar anjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake ha ura da auren. Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari." Baba Ibrahim ya fa a cikin tattausan lafazi. "Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan anjamu? Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana arin raba sunnar Annabi ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai aton da ya sake ta a mini hannu? Ta shi ka fice mini tun raina bai aci ba." Inno ta fa a a zafafe tana nuna masa hanyar fita. "Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki, ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya aukarta ta hanyoyi da dama kamar amfani da reza aya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta masu aski, askar wanzamai, wu a, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar inki. Duk ana iya auka da su matu ar dai jinin mai auke ita zai ta a abubuwan da na lissafa, wanda ba shi da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa, kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su ha u wurin aure da wa anda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba, haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin awainiya." Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS. AA sune masu cikakkiyar wayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai an rauni a cikin wayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu auke da amosanin jini wato sikila. Saboda raunin ita wannan wayar halittar ya kai ma ura. Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin soyayya ta yi arfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin aure, idan an duba genotype din sune kamar haka: Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar,
Chapter 18 · 0% Book details