← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 69

Sashe 68

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ce. "Ranka shi da e ina za ka je ne? Ka shigo ka auki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta. "Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a aukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri. Da zuwan su Mami Kura ba a auki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gaba aya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta. Sannu a hankali jikin Mami yake ara samun sau i, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Al ur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gaba aya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba. Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da yar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar aki da Daddy, ita ta koma akin Daddy shi ya koma akinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga akinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lalla a ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta. Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sau i. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi. Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan aurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano. Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra aki. "Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan in da na shirya ya wargatse. Kin san dai matu ar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce. "Hanya aya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai." "Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce. "Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri. "Sata kawai za mu la a mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu ku i masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi asa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci aya suka saki dariyar samun mafita. Suna gama tattaunawa Mami ta ebo damin ku in ta dam a wa Shukra, Shukra ta oye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da awarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan in su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau aya Shukra ta ta a shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu. Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta ranga a daga cikin aki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo angarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta an saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma awata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana aya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta fa akin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka ku in a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga akin bayan Fatima ta idar da Sallah, a angaren Shukra dama kuma bu atar maje Hajji Sallah tun da bu atarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba. Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har asa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai awarta Hajiya Falmata. "Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta fa a bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga akin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar auko wayar tun da can arshen gado ta fa a. Abu aya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta ta a saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta aunarta. Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata ma udan ku in da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ace. "A gaskiya ni kam idan aka kwashe ku in nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arzi i su ige da harkar tsiya? Shi dai arawo bai ji da in halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai arar arawon nan wurin Ubangiji a akin Allah ba." Haka dai kowa da abin da ya dinga fa a, daga arshe aka ce su waye suka shiga akin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka auko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga ku i ba, Mami ta bada shawarar a duba akunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi akin Auta wasu suka wuce akin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da asan kujeru, sannan suka wuce akinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da le ashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga ku i, nan take mutane suka auki salati. Aka wuce wurin Mami da ku i, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi. Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hanka a ta gefe. Daddy ne ka ai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru. Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba aramin aci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba. Abin duniya goma da ashirin ne ya ha e wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta fa a kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce. "Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? anuwar yarinya da ke ko a ina kika san ku i da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna acin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha arauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga akin. Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan aki Auta ta je ta same ta. "Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika auki ku in nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ace Uwani ta ce. "Auta fice mini a aki kada na sauke fushina a kanki." "Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta. "Ki fice mini a aki na ce." Auta ta tsorata sosai
Chapter 68 · 0% Book details