← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 69

Sashe 66

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abinci ba sai yau, a ranta ta jinjina arfin iyayyar da take yi wa Uwani. Uwani tana kuka haka ta kar i geron ta nufi harabar gidan tana dakawa, tun ba a je ko ina ba hannunta ya fara kanta ga turmin dakan ba shi da girman kirki don a surfe ma sai da ta raba shi gida hu u sannan ta gama dake shi. Tun Uwani na cikin inuwa har rana ta same ta don sha biyun rana a lokacin ta kusa, tana nan tana daka su Shukra suka fito cikin shirinsu gwanin birgewa. Auta ce ta arasa wurinta da sauri ta ce. "Uwani me kike yi haka ne?" Uwani ta share hawayenta. Tausayin Uwani ya kama Auta, a sanyaye ta ce. "Ki yi ha uri Uwani In shaa Allah Mami za ta gane abin da take ba ta kyautawa, unguwa za mu yanzu wallahi da na taya ki." Uwani ta gya a mata kai sannan ta wuce wurin su Shukra da har sun fita bakin gate. Fitar su Shukra ba jimawa ita ma Inna ta zo ta yi wa Uwani sallamar za ta je kasuwar Garu, Mami ta aike ta yin cefane. Ita kanta Inna ta so taya Uwani sai dai tana tsoron kar ta je ta yi abin da za ta bar aikinta, don da ku in albashinta take samun na rufin asiri. Lokacin da Uwani ta gama ta gama galabaita, ga yunwa ga kuma gajiya. Can kitchen ta je ta ajiye wa Mami garin geron saboda ba ta san yadda za ta sarrafa shi ba, ta fito za ta shiga ta ofar falo ta hangi wani tafkeken jangwalagwada. Har a fili sai da Uwani ta saki murmushi, ta auko tsumma a kitchen da sauri ta arasa wurinsa ta yi A'uzubillahi sannan ta dam e shi da hannunta, a wannan karon ta ci alwashin yadda Mami ta azabtar da ita to ita ma sai ta rama. Har ta gama tsara komai koda ta kwa e mata tana gamawa Kura za ta yi wurin Dada, kuma ko kashe ta za a yi ba za ta dawo gidan ba. Cikin san a take tafiya har ta shiga falon babu motsin kowa daga can akin Mami ta fara jiyo muryarta sama-sama da alama waya take yi. Ta matsa a hankali da niyyar ta bu ofar ta zura mata adangaren ta ji Mami na fa "Haba Hajiya Karima kin gan ni fa na tu e kaya yanzu haka wanka zan shiga, don Allah ku jira ni. Kin san yadda nake bala'in son ha uwa da matar DC kuwa? Kin san fa duk in da harkar manya take ba ma sanya da ita." Uwani ta saki murmushi da ta tuna tsiyar da za ta ulla wa Mami. A kan kunnen ta Mami ta gama wayar ta fa a ban aki, sai da ta tabbatar da wankan Mami ya fara nisa sannan ta bu ofar akin a hankali ta shiga. ofar ban akin ta nufa sai ta fara mur ofar da sauri-sauri, daga ciki Mami na sa a sabulu a fuska ta ji ana mur ofar. Mamaki ne ya kamata don ta san su Shukra ba sa nan, kuma ko suna nan ba za su bu e mata ban aki tana ciki ba. "Waye a nan?"Mami ta tambaya a hassale. Uwani ta kausashe murya ta ce, "Sarki ne ya zo da kansa ba aike ba." Da mamaki Mami ta furta. "Sarki wane iri? Kai waye da har za ka tsallake ko ina ka shigo akin matar aure, kuma har ka nemi bu e ni a ban aki." "Sarautar ce haka! Kuma na aure ki daga yau, tun da na samu sukunin mai gidanki ba ya nan. Dama tun ranar da aka yi maganar auren anki Jafar ni ma na kai ku in aurenki, yanzu haka kuma na biyo ki ne domin na arje amarci." Uwani ta arasa maganar dariya na son wace mata. A hargitse Mami ta ce. "Kai malam wai waye kai ne ma? Ba ka da hankali za ka ce ka na son matar aure?" Uwani ta sake kausashe murya ta ce. "Ni dai babban burina ki ba ni ha in kai domin ni matashin saurayi ne dal, soyayya ce kawai ta sa na tsaya a kanki. Amma kada ki yi mamakin kasancewa ta wata halitar da ba irin taki ba." Uwani na gama fa ar haka ta bu ofar a hankali ta wurgar wa Mami Jangwalagwadan sannan ta janyo ofar da arfi ta rufe, da yake da key a jikin ofar nan take Uwani ta murza key in ta cire shi ta ajiye a gefen gadon Mami. Lokacin da Mami ta ji abu ya sauka a kafa arta da sauri ta hau kiciniyar wanke kumfar fuskarta. Hannunta ta kai ta shafo kafa arta bayan ta wanke fuskarta, wani irin adabarbar ta ji take jikinta ya hau karkarwa. Ta yi ta maza ta yi wurgi da shi, sai a lokacin idonta ya sauka akan tafkeken adangaren. Da yake shi ma ya galabaita nan take suka fara 'yar tsere da Mami a ban aki, duk yadda Mami ta so bu ofar sai ta gagara. Cikin Kuka Mami ta ce. "Wayyo Allah Lado, Jafar kana ina ka kawo mini auki." Uwani ta gimtse dariyarta, ta sake matsa wa jikin ofar ta ce. "A yanzu babu mai iya taimakonki domin amarci na zo ci. Kuma daga yanzu ni fa zan dinga riki a har zuwa surar mutane ina kawo miki ziyara." Uwani na gama fa ar haka ta sulale ta fice daga akin, cikin sauri ta zagaya ta wuce sashenta. Jafar ta gani ya yi ai a falo yana bacci, da alama kallo yake yi bacci ya yi awon gaba da shi don ga remote nan a gefensa. A hankali ta wuce cikin akinta ta fa a kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ugin da cikinta ke yi ne ya sake ankarar da ita yunwar da ke cin ta. Kitchen ta fa a ta fara duba tukwane, ta ci karo da guntuwar Indomie da Jafar ya ci ya rage. Tukunyar ta auko ya zuba shayi ta koma falo ta zauna ta ci, sannan ta bu e bokitin dubulan in ta ta ebo alkaki da dubulan na gararta ta baje a asa ta ci gaba da loda wa cikinta. Tana cikin ci suka ji bugun ofa kamar za a alle ta. "Ranka ya da e! Ranka ya da e akwai abin da yake faruwa a sashen Hajiya." Jafar shi da Uwani kusan lokaci aya suka mi e a zabure, da sauri Jafar ya bu ofar ya ga Lado da Baba tsoho, a imauce ya ce. "Lafiya Lado?" "Ranka ya da e bugun ofa nake ji a sashen hajiya kuma idan aka buga bayan wani lokaci sai na ji shiru, kuma sama-sama nake jiyo muryar Hajiya kamar tana kuka." Jafar tun bai gama jin kalaman Lado ba shi da Uwani suka zuba a guje suka yi sashe ta, ganin haka ya sa Lado da Baba tsoho suka rufa musu baya. Jafar na zuwa akin Mami ya nufa, abin mamakin komai tsaf yake babu wata hayaniyar tashin hankali. Wani rin numfarfashi suka ji a cikin ban aki, da sauri Jafar ya dinga buga ofar yana kiran sunanta. Bugun da Jafar yake yi ne ya sake farfa o da Mami daga suman da ta yi, wanda ta yi suma a cikin ban akin babu adadi. "Jafar! Wayyo Jafar ka shigo ka taimaka mini, wallahi adangare ne zai haike mini." Mami ta yi maganar a galabaice don saboda wahalar da ta sha ko motsin kirki ba ta yi. Da arfi Jafar ya dinga buga ofar amma a ame take yam ta i bu uwa, "Ranka shi da e wannan ba shi ne mabu in na?" Lado ya ago key in da ke kan gadon Mami. Da sauri Jafar ya kar a ya bu e yana bu ewa adangaren ya yo bakin ofar a guje, ganin haka ya sa daga Lado har Jafar suka iba a guje. Sai da suka ga ya shige ashin gado sannan suka fara le owa, Mami da rarrafe da jan ciki ta fara tahowa Baba tsoho ya tunkari ofar ban akin da niyyar taimaka mata, yana le awa ya hangi Mami tum ur da sauri ya juya da baya yana fa "Kai a'uzubillahi wannan lamari da muni yake." Baba tsoho ya nufi bakin ofa su Jafar na ganin yadda ya dawo jiki a sanyaye Lado ya je zai shiga da sauri Baba tsoho ya girgiza kai ya furta. "Ummm-ummm ku dawo Lado abin babu kyawun gani." Lado na zuwa ya ci karo da Mami na jan ciki, Mami da take a yunwace da neman taimako ta fara jan afar wandon Lado tana fa in. "Ku fitar da ni daga gidan, idan ba haka ba za su kashe ni." Ganin yanayin da Mami take ciki ya sa Lado ya fisge a guje yana fa in. "Subhanallahi wannan lamarin ya munana Baba tsoho me ya sa ba ka bu an aiki ba? Haka kawai zan one idanuna." Jafar ya nufi wurin ban akin, kamar ha in baki Lado da Baba tsoho suka yi wata uwar sufa suka dafe kafa un Jafar suna fa in. "Wallahi al'amarin akwai muni Jafar kada ka shiga." A ufule Jafar ya fisge ya ce. "Ni da uwata ne za ku yi mini iyaka? Duk halin da take ciki ni ba zan guje ta." Jafar ya fisge da arfi ya tunkari wurin da Mami take. Cikin hukunci Ubangiji gobe ne za mu kammala Free pages inmu, idan kina bu atar ci gaba za ki biya 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar ta wannan lambar 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [23/06/2024, 12:50] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 66 · 0% Book details