Sashe 26
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shayi ya jikinsa?" Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce. " an Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya arasa maganar yana fashewa da kuka. "Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?" Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum, sai ka nemi wula anta mana sana'ar wanzanci ne?" Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na fa a ba, yanzu mu je na ga yanayin jikin na sa." Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu an Bishir a yashe a asa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya arasa ya fara karka e masa, ya ago a an zafafe ya ce. "Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda udaje suka bin sa ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba." Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya ri o hannun Fadil jikinsa yana rawa ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?" Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a auke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan an shekara ashirin da yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake sa ar, rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan alubalen." "Wai boka da kake ta afafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk dai ba abu aya ake yi ba?" Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta. Fadil ya cigaba da karka e wa an Bishir uda ya ce. "Gaskiya akwai bambamce-bambamce da dama. Kamar yadda muka sani shayi wacce a kimiyance ake kira (Circumcision) wata aramar tiyata ce da ake cire fatar loba (Foreskin) wacce take zazzagowa ta rufe kan al'aurar namiji(Glans). Kaciya tana da dalilin da ya sa ake yin ta, daga angaren addini zuwa al'ada. Mafi yawancin asashen da suka ci gaba, suna yin shayi ne a rana ta farko da aka haifi jariri. Wasu abilun kuma suna yi bayan suna ko idan an yaye yaro. To amma kin ga a irin yankin abilunmu, yawanci ana yi wa yara daga shekara uku zuwa bakwai. Sannan rashin yin ta babbar barazana ga lafiya ne. Kamar yadda shayi ke da dalili akwai amafanin da take da shi, musamman a angaren lafiya. Domin yin ta yana bayar da kariya daga saurin aukar cutar infection, saboda cututtuka suna iya oyewa a ciki idan ba a cire fatar ba. Tana bayar da kariya daga kamuwa da penile cancer, a angaren mata kuma zai rage musu kamuwa da cervical cencer, har ma da matsalar saurin kamuwa da ciwon (Balanitis) kumburin saman al'aurar namiji. Da ma sauran cututtukan da ban lissafa ba." Jikin Uwale ba aramin sanyi ya yi ba, Baba Sale ya zube a asa kamar wanda aka zare wa laka ya ce. "Yanzu boka duk wannan bayanan a kimiyance ka karance shi? Shi an Bishir wannan ruwan da take yi na me ne ne?" Ganin yadda Baba Sale ya aga hankalinsa, ya sa Fadil ya tsugunna a gabansa ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Baba Sale, wannan ba komai ba ne In Shaa Allah za a kamo bakin zaren matu ar aka je asibiti. Rashin kula da tsaftar wurin ya sa infection ya shiga, har ya haifar da zubar wannan ruwan da kake gani. Idan har aka je asibiti za su duba shi, su yi abin da ya dace su ba shi magunguna. Ni ma don dai ina da uzuri, da zan iya yi masa treatment. Amma ba zai yuwu, a bar yaro haka har tsawon lokacin da zan dawo ba. Sannan yana da kyau a kula da tsaftar raunin, kada a bari udaje da wasu warin su dinga hawa jikinsa; saboda za su iya fesa masa wayoyin cutar da ido ba zai iya gani ba. Rashin kulawa da tsafta, ha e da takatsantsan zai iya haifar da kamuwar cutuka, har ya haifar da fiye da wannan da muke gani wanda ba ma fatan hakan." "Uwale maza auki an Bishir mu tafi asibiti, wallahi ni babban tashin hankalina kada ma abin ya guntule ya fa asa." Baba Sale ya fa a cikin hawaye. Fadil ya jima yana ba su shawarwari da warin gwiwa sosai, sannan suka fito suka shiga mota ya sauke su a asibiti shi kuma ya tafi uzurinsa. Motar Fadil ta fita babu jimawa Mai adaidaita sahu ya sauke Baba anladi, hannunsa aya ri e da matarsa ayan hannun kuma ri e da akwati. Sai da ta sauka sannan ya auko musu akwatinan su ya ajiye a gefe. Ku i ya zaro ya biya mai adaidaita sahun, ya kamo hannunta yana shirin shiga gida Uzee gaye ya arasa wurin bakinsa a washe kamar gonar auduga ya ce. "Oyoyo jirgin ceto, Oga murfi namu na gargajiya, uban gidan kowanne mai cin mushe. Duk wanda kwa arsa ta yi ruwa ya zo a aure masa, ka suturta kuma ka rufa asirin gayu. Ina wanda ya samu 'yar shila ya bige aka samu matsala? In wanda bargon suturarsa yake son yayewa? Ya zo ga mai lullu e masa har ya yi bacci. Oga murfi wannan 'yar shilar ita ma zuwa ta yi a kifar da madafun ikonta ne?" Tun da Uzee guye ya fara maganar kan Baba anladi ya ara girma, ya fa a fara'arsa ya ce. "A dai dinga iya baki Uzee saboda tsaro ba don tsoro ba. Wannan da kake gani ba costomer ba ce, matar da na auro ce." Murmushi ta yi tana jifan Uzee da wani karuwan kallo, wanda kallo aya kawai ya yi mata ya fahimci ita ma 'yar hannu ce. Uzee ya yi asa da murya ya ce. "Wallahi Oga murfi ka zo a daidai, domin yanzu haka akwai wata yarinya da rana ta wace mini. A ta aice dai cikinta wata biyu kenan, don Allah ka rufa mini asiri kamar yadda ka saba ka arar da shi." Baba anladi da irin su Uzee suke kira da Oga murfi ya ce. "Ka ga zuwana kenan, ko cikin gida ban shiga ba. Koda zan dawo bakin aiki sai zuwa nan da sati guda, domin shi kansa chemist in yana bu atar gyara." Uzee gaye ya yi masa godiya, sannan Baba anladi ya shige cikin gida hannunsa ma ale da na matarsa da yake jin ta kamar tsoka aya a miya. Tun daga harbar gidan mutanen cikin gidan suka shiga yi masa barka da zuwa, sai dai kusan kowa bakinsa unshe yake da magana kasancewar ganin Baba anladi rungume da wata mace mai zubin 'yan duniya. Amma da yake ba su ga fuska ba, sai kowa ya tsuke bakinsa. "Lale marhabun wa nake gani haka da hantsin nan?" Inno ta fa a tana washe fuska, turus ta yi ganin anladi sar afe da mace a gefe. Inno ta ance ido tana are mata kallo ganin gashin doki ya yi mata yaro-yaro a fuska. " anladi daga ina ka samo wannan abin?" Inno ta tambaya tana mi e wa tsaye rai a ace. anladi ya saki murmushin soyayya, ya shafo fuskar matarsa cikin so ya ce. "Inno wannan ita ce matar da na auro ai, so nake sai mun zauna na gabatar miki da ita." Inno ta fara bin ta da kallo, tun daga afa har zuwa tsakiyar kanta. "Baby ina bu atar hutu ka san na gaji. Mu je aki ka yi mini tausa." Ta furta tana shafa jikin anladi. Inno salati ta saki tana tafa hannu ta ce. "Yanzu anladi, addarar da ka kwaso mana kenan wannan mai zubin alakwankwan in?" anladi ya sunkuya ya sumbaci matarsa ya ago ya cewa Inno, "Wallahi Inno kamar kin sani wannan ita ce addarata. Jin ta nake har birnin zuciyata. Beb wannan ita ce Mom ina, you know i told you Dad ina ya jima da mutuwa." Ta ago tana taunar cingam ta ce, "Am so sorry Mom, ya kike?" Inno ta saki baki da hanci tana kallon ikon Allah. Jin maganganu a tsakar gida ya sa Mai yasin ya le o yana fa "Inno ke da waye ha..." Maganarsa ce ta ma ale, sakamakon ha a ido da suka yi, lokaci aya wani irin tari ya turnu e shi. Daga can angarenta ita ma ido ta zaro, amma sai ta daidaita nutsuwarta ta basar kamar ba ta san Mai yasin don kada su gano su. 'Me ne ne ala ar wannan yaron da 'yar gwal? Ko dai aurensa ta yi ban sani ba, lallai kuwa dara ta ci gida idan har haka ne.' Mai Yasin ya raya a ransa. anladi ya zaro mukulli a aljihu, ya bu akinsa ya fara jan akwatinansu ya shigar musu da su ciki. 'Yar gwal a wurin ta fara rage kayan jikinta, ta zame mayafinta ta wurga a kan igiya. Ta zamo hular gashin dokin kanta za ta wurga igiya a daidai lokacin Yaya Inu ya shigo cikin gidan, a bisa tsautsayi ta jefa masa a fuska. Warin gashin ya daki hancinsa, a tsantsance ya wurgar da shi gefe rai a ace yake kallonta, cikin tsawa ya ce. "Ke! Wace ce ke?" Daga cikin aki anladi ya ce, "A'a Yaya Inu, kada ka sake ka sake yi