← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 69

Sashe 37

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gari yana zuwa masallaci ana gama aurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya mi a wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka aura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ari. Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta arasa, almajirai ne suka shiga da ullin kayanta. Inno tana hango ta, ta arasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana fa "Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?" "Idan kika bibiya ta fita ta auko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan yalli da kike yi haka." Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari." Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, irjinsa ne ya yi wata irin bugawa da arfi. Haka kawai ya ji gabansa yana fa uwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba. Da sallama auke a bakin Inno suka shiga akin, Mai Yasin yana aga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin. "Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka la e bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta fa uwa asa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da allagaggen aurenka a kaina." Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gaba aya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan aki da za a yi mata. Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fan ararrun awayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa akin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a akin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce. "Ku wa anne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tun ele da dare?" Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tam elen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko urarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce akinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige aki ta kwanta. Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." irjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha ba i." Zuly ta an tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi ha uri ka tashi, don ni in salu e namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai ta a auro fitsararsiyar mace irinta ba. A angare aya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta mi e tsaye tana warware ankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma la abin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani." Zuly ta arasa maganar tana fisgo siraran afafuwan Yaya Inu. Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce bada alar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba a ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su an Bishir? Yar gwal da anladi zaman su zai ore? Duka wa annan tambayoyin da ma wa ansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI. AlhamduLillah, a nan na kawo arshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [05/06/2024, 16:52] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 37 · 0% Book details