Sashe 46
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gaba aya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan amshi suke yi suna kallon mutane ai, don ko maganar arzi i ba ta cika ha a ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wula anci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba. Asalin Tarihinsu Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin auyen lambar unci, aya daga cikin ananan auyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan auyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure aya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai aninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko atan wata babu wacce ta ta a yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu. Baffajo tun da uruciyarsa yakan ebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa hu u suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba. A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya fa a tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sar arfi sai suka yi masa wacen shanu da yawa, ka an ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji. Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka ha a kai shi da an uwansa suka bar garin gaba aya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani auye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka. Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, ba ar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo an gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba oyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu aya ubansu aya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai ta a samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina ka ai suka rage wa anda suke uwa aya uba aya. A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa. Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba aya. Malam ya ha u da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a auki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka aura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya ha a ta da anwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya bu aci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya ro i arzi in a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya ha ura ya bar masa ita. Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman ( an sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi). Baba Sa'idu ( anin malam) Yana da mata aya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da an'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi arfi a garin Zaria, don haka ya auki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gaba aya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji. Malam Sa'idu ya ka u da rashin an uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya ri e dukiyar an uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati ka ai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci. Baba Mamman yana da matar aure aya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko ka an. Mace ce mai fa in rai da ta ama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hul a da matan masu ku i. Wannan halin na ta ya sa ko ka an ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su Shukra suka kwasa gaba aya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida. Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya ha a kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne ka ai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da angarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki. Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a ra a wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna on bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin da i. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka aura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata aya da yara hu u. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko ka an ita da kishiyarta ba sa jin da in zama da shi sakamakon mugun halinsa. Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi ri on Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba aramin da i ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha hu u a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar ashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce ka ai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara. Jafar ma'aikacin an sanda ne mai auke da mu amin ASP,