← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 69

Sashe 7

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan Sallar Isha'i
Zaune yake a matsakaicin
akin da aka ware masa, daga gabansa wani
aton fulas ne cike da farfesun kaji.
Sai da ya zuge tsokar cinyar kazar hannunsa, sannan ya
aga
aramar wayarsa ya danna wata lamba. Bugu
aya ta yi ya ji an
auka, ya yi
asa da murya ya ce.
"Barka da hutawa 'Yar gwal!"
Malam mai Yasin ya furta yana kur
ar romon naman, amsa masa ta yi sannan ta ce.
"Ni fa na gaji wallahi..."
Da sauri ya katse ta.
"Haba 'Yar gwal, na fa
a miki kwantan
auna na yi wa mutanen gidan nan, har na samu na aure tsohuwar nan. Ni na san Inno ba za ta ba ni matsala ba sai dai 'ya'yanta, amma ina aure ta magana ta
are. Tatsarta zan ta yi har na tara mana ku
in da za mu hole, kada ki ji muryata
asa-
asa har yanzu nuna musu nake ba ni da lafiya."
Daga can
angaren 'Yar gwal ta saki dariya ta ce. "Shege Malam Gambo wallahi ko shai
an bai kai ka shai
anci ba."
Malam mai Yasin ya saki dariyar shakiyanci, suka cigaba da hira sannan suka yi sallama.
Ya kai kusan awa guda a zaune a bakin gadon yana yi mata firfita, saboda ko ka
an ba ya son abin da zai dagula lissafinta. A hankali Rahina ta bu
e idanunta ta sauke su a kan mai gidanta Labaran, murmushi ya sakar mata ganin za ta tashi ya sa ya
ago ta zaune sannan ya rungume ta sakar mata kiss a goshi.
"Barka da tashi masoyiya!"
Labaran ya furta cike da so yana jin kamar zai lashe Rahina. Fari ta yi masa da ido ta ce, "Wai tun da na kwanta kana zaune masoyi?"
"Ina zan matsa daga wurinki
aunata. Yanzu dai bari na sirka miki ruwa ki yi wanka. Ya
arasa maganar ya fita daga
akin."
Rahina ta bi bayansa da kallon soyayya tana jin tamkar ita ka
ai ta yi dacen miji a duniya. Tana nan zaune ya dawo ya ri
o ta, ganin za ta tu
e kaya ya saka hannu ya fara rage mata.
Rahina ta
aura zani ta yafa
an kwali a kanta, Labaran ya ri
e mata hannu
ayan hannun nasa yana ri
e da kwandon wanka suka nufi hanyar ban
aki. Sai da ya ga ta shiga ban
akin, sannan ya koma domin ya zuba mata abincin da za ta ci idan ta fito. Rahina irin matannan ne masu tsayi da
iba, shi kuma Labaran
an tsamurmuri ne ko tsayin kirki ba shi da shi. Yadda yake son Rahina da kishinta ji yake zai iya aikata komai a kanta.
Malam mai Yasin yana daga zaune a
akinsa ta labule ya hango wucewar Rahina, ya jima ransa yana biyawa da ita don haka bayan tafiyar Labaran ya yi zaraf, bayan ya ji ta fara she
a ruwa ya nufi ban
akin cikin san
a. A hankali ya tura
ofar ban
akin, da yake dare ne sai Rahina ta yi tsammanin ko Labaran ne ya shiga domin ya tayata wankan. Malam mai Yasin yana shiga da sauri ya wara hannuwansa ya dadumo ta, cike da so da
auna Rahina ta ce.
"Wallahi ba don kada na saka son zuciya ba, da sai na ce duk duniya babu matar da ta kai ni sa'ar miji masoyi."
Malam mai Yasin don kar ya yi magana ta ji muryarsa sai kawai ya ce, "Ummmmm!" Ya cigaba daduma hannunsa a jikinsa. Rahina tana shafo fuskarsa ta ji gemunsa da gashin bakinsa sun yi mata
ababa, a razane ta ja da baya da ta ce. "Wayyooo Allah! Masoyi ka zo kwarto a ban
akin nan."
Da gudu Malam mai Yasin ya fice daga ban
akin ya fa
akinsa, Labaran da ke
aki jin ihun Rahina ya sa ya zaro wani kafcecen almakashi irin na aikin gona ya tafi da shi.
Yana zuwa ban
akin ya shiga jera mata tambayoyi, ba ta tanka masa ba sai ji ya yi ta fashe da kuka. Ganin ba shi da wata mafitar ya sa shi ma ya rushe da kuka har da majina, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce.
"Kwarto ne ya shigo mini ban
aki, kuma tas ya gama lalube ni."
Wani abu ne ya soki
irjin Labaran tsananin soyayya da kishinta ya rufe shi.
"Sai da na laluba gemu da gashin bakinsa, na gane ba kai ba ne tun ba ka da shi." Rahina na
ara fa
in haka ta sakin kuka. Jikin Labaran ne ya shiga karkarwa zuciyarsa tana zafi, cikin huci ya ce.
"Na tabbata Ado ne! A cikin gidan nan shi ne tuzuru sako zaninki ki tafi
aki, wallahi yau sai na guntule shi da almashin hannun nan nawa. Nan gaba sai na ga da me zai nemi yin kwartoncin."
Labaran yana gama magana ya fita a guje yana wani irin ihu kamar wanda zai tunkari ma
iya a filin ya
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam
[02/02, 15:02] Ameerah Adam
: *GIDAN LIKITOCI*
Chapter 7 · 0% Book details