← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 69

Sashe 4

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYU Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke ra e a can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba ba ta ta a ganin ta yi irin haka ba, San ira ta hango ma ale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo ha e da araji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka San iran ya saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda San ira ya dinga zuge ganyen bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya aga hannu ta tafka masa itace a baya. San ira ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan bil'adama ba ne." Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya sarautar na dam a maka yanzu kai ne mai garin." Laraba ta saki murmushin eta ta ri o babbar rigar San ira ta baya, suna gudu tana tafka masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi asa, ya sa San ira ya yi wani araji ya dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. San ira ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da urar asar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya mi e bai sake fa uwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tu e ta ya wurgar. Ya ta are ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama. Laraba ta so yale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa baya da gudu. A lokacin da Mai gari ya arasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman ma oya ya fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar wace kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi. Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga yara da manya sai kowa ya nemi ma oya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar gidan kowa ya fashe sai wani aramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo. Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron ya mi e a zabure yana ihu ya shige akin mahaifiyarta. Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar akin Salame a can ashim gadon arfenta. Ya shiga sauke numfashi da yar yana muzurai, hannunsa ya kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya ce. "Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an kunna fanfo." Inna da kunya, haushi da ba incikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce. "Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ari ka kashe fanfon." A razane Mai gari ya ago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito daga ashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta walla wata irin ara ta yanke jiki ta fa i. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke le owa tsaye suka yi suna kallonta, aka rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yun urin tashinta. Laraba ta an jima a haka sai kuma ta fara bu e idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?" Shiru gaba aya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a an razane ta ce. "Mai gari me nake yi a nan?" Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki fara zuwa gida tukunna." Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta maze tana tafe tana hura hanci tana bu a kafa a har ta je gida. Baba Inu yana shiga gida kai tsaye angarensa ya nufa, tun daga bakin ofa ya tsaya ya yi gyaran murya yana ha e fuska, lokaci aya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma suka shiga tsawatarwa 'yan ananun da ba su yi wayo ba. Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai anana da manyan kwanuka birjik a gabanta. Wa ansu ananan yara ne kusan su hu u wa anda ba su wuce shekara aya zuwa da rabi ba, biyunsu ri e suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama zanin Larai. "Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da wa annan yaran. Ke Kulu zo ki janye mini su don ubanki!" Ta arasa maganar a fusace ta fisge kwanukan hannun yaran. Baba Inu ne ya arewa tukunyar kallo, ya matsa gabanta a kausashe ya ce. "Ke Larai satar mini abinci kika yi? Kika ara a kan wanda na ebar muku, da na ga kin rafka wannan rafkekiyar tukunyar?" Jiki yana rawa Larai ta bu e tukunyar ta ce. "Mai gida tukunyar girkin ce ta ule shi ya sa na ora wannan." Le a tukunyar ya yi ya hango abinci a can asan tukunyar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce akinsa. Mukulli ya saka ya bu e, ya auko wata 'yar madaidaiciyar tukunya ya mi a mata yana daga tsaye ya ce. "Maza umama mini miyar nan." Da sauri Larai ta kar a ta ora a kan murhun, Baba Inu ya koma kan benci ya kasa ya tsare yana ganin yadda take rabon abinci. Kowanne kwano idan ta auko bai fi ta yafita ludayi aya da rabi ba, saboda idan da sabo sun saba a kullum abincin ba isarsu yake yi ba. "Mai gida a zuba maka kana marmarinsa?" Larai ta tambaya tana gyara goyon Fure da ke bayanta. "A'a ku ci kawai!" Baba Inu ya furta a da ile. Larai ta ebi ragowar wanda ta rage masa cikin murna ta shiga ara wa kwanonta. "Ke Larai wallahi son zuciyarki yawa gare shi, ba za ta sa u ba wallahi sai kin ara wa kowa." Hansatu ta yi caraf ta yi maganar ganin abin da Larai take yi. Babu yadda ta iya ganin Baba Inu yana wurin ya sa ta shiga arawa kowanne kwano bai fi cokali ai ba. Bayan ta gama ta ce kowa ya auka, a guje yara da 'yan matasan cikinsu suka auka da sauri, wasu tun a tsaye suka fara zuba loma duk da abincin yana ona su. amshin umamen miyar ne ya fara dukan hancinsu, Larai ta sauke har za ta kai masa aki Baba Inu ya ce ta kawo gaban bencinsa ta ajiye. Abu da ke da tsohon ciki wani irin ayi ya taso mata. Kwanon abincinta ta auka ya arasa wurinsa cikin marairaicewa ta ce. "Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sau in abin da nake ji. Wallahi ayi ne ya addabe ni." Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?" Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake ha e fuska ya ce. "To yanzu ba incikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai mai on, ta ya ya zan iya samun warin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta ha iyi yawu tana kallon farantin da Baba Inu ya zuba miyar da irjin kaza, sai da ya rufe tukunyar ya mi a wa Larai ta mayar masa aki sannan ya ce, "Wallahi ba don cikin jikinki ba, da idan ba ki matsa daga kaina ba sai na sheme ki. Dubi yadda kike ebo mini fuska kamar an matse lemon tsami." Abu babu yadda ta iya, haka ta ja jiki a sanyaye ta koma ofar akinta ta zauna. aton biredi ya auko ya gutsira sannan ya mayar ya saka kwa o ya rufe akin nasa. Kan bencin ya koma ya fara yagar biredin yana dangwalar miyar da ita, daga yaran da suke wurin har iyayensu ban da ha iyar yawu babu abin da suke yi. Wani aramin kwanon sha ya bu e kusan cike yake da nono, ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ullin maganin arin kuzari da ya saya a daren ranar. Ragowar ullin ya kunce ya zuba ya jujjuya ya ajiye shi a gefe, ya ci gaba da yagar kazar yana dangwalar biredi da miya. Baba Saleh sai da ya gama loda duka magungunansa a cikin mota sannan ya koma gida, domin ya yi wa an Bishir sallamar tafiya yawon tallar magani. Yana shiga sashensa, ya samu an bishir yana tsanyara ihu kamar wanda ake walewa idanu. Wani irin bugu irjinsa ya yi, kamar wanda ya yi tozali da gawar mahaifiyarsa. A hargitse ya janyo an Bishir ya
Chapter 4 · 0% Book details