← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 69

Sashe 52

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

furta. "Ga waliyin Jafaru ga waliyin Hauwa kulu an kawo sadaki dubu ari da hamsin lakadan ba ajalan ba. A bisa duka shaidun da ake bu ata sun kammala kowa ya shaida an aura auren Jafar Mamman mai shanu da amaryarsa Hauwa kulu Umaru mai shanu, a kan sadaki naira dubu ari da hamsin lakadan ba ajalan ba." Daga haka ya fara rattabo addu'o'i ana ta saka albarka. Baba Isuhu ya arasa yana yi wa Jafar Allah sanya alheri, ganin shi ne angon wa anda ba su san shi ba suka arasa suna masa fatan alheri. Tamkar butum-butumi haka Jafar ya ame a wuri aya, ta cikin hayaniyar mutane ya sulale kai tsaye ya wuce gida. Na Madina sai wala masa kira yake amma ya yi banza da shi, Jafar kai tsaye akinsa ya shige ya datse yana kai wa da kawowa. "Ga alewa da dabinon aurin auren anki, ki saka albarka domin addu'arki na da muhimmanci a wurinsu. Bayan mun idar da sallah aka aura auren Jafar da Uwani." Daddy ya furta wa Mami bayan ya shiga gida. A fusace Mami ta suri ledar dabinon ta yi wulli da ita, cikin acin rai ta furta. "Daddyn Jafar yanzu tozarcin da za ka yi mini kenan? Wannan tsinannan auren zan saka wa albarka? Wallahi a daren nan sai Jafar ya saki Uwani." Murmushin takaici Daddy ya yi ya ce. "Na riga da na gama magana da Jafar, ki sani idan kika tilasta shi ya saki yarinyar nan wallahi sai na sauke miki igiyar aurenki uku daga kaina." Baki sake Mami ta bi Daddy da ya wuce akinsa da kallo, saboda takaici sai kawai ta fashe da kuka. Su Shukra ne suka arasa suka fara lallashinta. Cikin anin lokaci garin ya auka 'Yar ashin gwiwa ta yi aure, wasu masu arfin halin har gidan suka shiga yin tsegumi. Uwani duk wainar da ake toyawa ba ta sani ba sai daga baya Dada take sanar da ita, babu wani abu da ya aga mata hankali abin da ya fi damunta ciwon jikin dukan da su Mami suka yi mata, wanda ta ci alwashin gaba aya za ta ladaftar da su aya bayan aya. Washegari ne ya kama sunan gidan Baba Isuhu sai dai tsamin jikin da Uwani take fama da shi ya hana ta walwala, don ta ci burin ko yaya ne ta tarwatsa 'yan taron suna. Yamma li is Uwani da awarta Kubra na tafe suna hira Kubra ta ce. "Oh 'Yar ashin gwiwa yanzu dai aurenku da ansandan nan ya tabbata, to kema 'yar sanda za ki zama?" Uwani ta yi jim sannan ta ce. "Da dai tu in jirgin sama nake son koya na dinga lulawa a jirgi ta cikin gajimare, an ce fa idan ka na jirgi har ta o gajimare ana yi da hannu idan aka zira hannu. Amma dai yanzu tun da na auri ansanda gaskiya ina jin ni ma 'yar sanda zan zama, ko ba komai Yaya Jafar ba zai mini baraza da bindiga ba tun da kar ta san kar..." Maganar Uwani ta ma ale sakamakon hango Shukra da saurayinta a ofar gida, suna jingine a jikin mota Shukra sai karairaiya take masa tana fari, a can gefen wata bishiya ta hango wani mahaukaci da ake yi masa la abi da 'Ba ka da nauyi.' abi'arsa ce ya auki mace ko namiji ya dinga yawo da kai a gari yana ce wa ba ki da nauyi, kuma ba zai dire ka a ko ina ba sai tsakiyar kwata. A fili Uwani ta she e da dariya Kubra ta ce. "Lafiya kike dariya 'Yar ashin gwiwa?" Gya a marau in hannunta ta kalla sannan ta ce. "Zo mu je wurin ba ka da nauyi." Kubra ta zaro ido, da sauri Uwani ta ha e fuska. "Malama tsaya a nan wallahi kika ata mini shiri sai na sa shi ya auki Baffanki gobe." Kubra ta ja baki ta tsuke don ta tabbata Uwani za ta aikata fiye da haka. "Baka da nauyi za ka ci gya a marau?" Uwani ta fa a tana ka a ledar gya ar a gaban mahaukacin. Washe baki ya yi cikin katuwar muryarsa ya ce. "Anci gya a." "To bari kaji ina da gya a marau soyayyiya da yawa, idan kana son na baka to ka ga waccen saurayi da budurwar ka je ka auki budurwar ka zaga gari da ita, duk wanda ya zo cetonta ka ha a masa jini da majina ni na sa ka. Na maka al awari zan ara maka wata, ila ma ba baka kwano guda..." Tun Uwani ba ta gama magana ba, Baka da nauyi ya fisgi ledar gya ar hannunta ya saka a aljihu, kai tsaya ya nufi wurin su Shukra ya tsaya a gabansu yana sakin shashashar dariya. A yatsine Shukra ta dube shi ganin yadda kayan jikinsa suke du un-du un ya sa Shukra ta tsartar da yawu sannan ta ce. "Malam mene ne haka ka zo ka saka mutane a gaba? Haka kawai ka saka mu tashin zuciya, dalla matsa daga nan." Ta yi maganar a yatsine ita a dole ta yi birga a gaban Salim. Salim ya ka a mukullin motarsa yana shirin yin magana sai gani ya yi Baka da nauyi ya suri Shukra yana dariya, da mamaki Salim ya dube shi fuska a ha e ya ce. "Kai Malam wannan wane irin iskanci ne..." Tun Salim bai rufe baki ba Ba ka da nauyi ya sa gwiwar hannunsa, ya yi masa mahangur a a fuska ya kusa ha a masa jini da majina. Wani haske Salim ya gani ya gifta masa kansa ya yi wani irin nauyi dum. Cikin gigita ya fa a cikin gidan da gudu, da yake sashen Dada shi ne yake kallon ofa da sauri ya fa a ciki a guje cikin fitar hayyaci, Dada na tsaye da aurin irji za ta sauya kaya sai ganin mutum ta yi ya shigo a guje yana wuri-wuri da wawure-wawure. "Hasbunallahu wa ni'imalwakeel kai wane gansamemen aton ne haka..." Kalaman Dada suka ma ale sakamakon jin Salim na fisgar zanin jikinta ta asa yana tura kai don shi ma oya yake nema. "Kai don ubanka ba ka ganin ni tsohuwa ce, wai me kake nema a ciki ne?" Salim ya sake hanka e kansa yana shirin banka e Dada ta fa i a asa, ganin haka ya sa Dada ta saka kuka tana fa "Yau wane salon kwartanci ne haka ido biyu tun dare bai yi ba." Dada ta furta tana fisgar zanin shi ma Salim yana ja. Ganin Salim da gaske tura kansa yake yana yun urin sauke zanin Dada a asa ya sa ta fasa ihu tana fa "Jama'a ku kawo mini auki ku ceci tsohuwa a hannun kwarto." "Don Allah ki oye ni zai sauke mini fuskata daga jikin kaina." Salim ya fa a cikin tashin hankali, yana sake fisgar zanin Dada yana tura kansa ciki. "Don Ubanka ka rasa a ina za ka oye sai a cikin zanina, kai amma dai yau Allah Ya ha a ni da lalatattun kwaratan zamani." Salim bai bi ta kan Dada ba ya sure zanin jikinta ya yi uwar akinta a guje, sai ga Dada daga ita sai an tofi shi ma ya zazzago asa saboda kiciniyar da suka sha da Salim. Shukra ban da ihu da zille-zille babu abin da take yi, don Ba ka da nauyi ya sauke ta amma ya i, yara kuwa sai bin su suke a guje suna masa wa a da tafi. Wannan ya sake ingiza shi ya ci gaba da gudu da Shukra a saman kansa, ankwali da mayafinta tuni suka cire tun a ofar gida. Sai da ya gaji don kansa ya je wata atuwar kwata ya tsoma ta a ciki. "Allah Ya isa tsakanina da kai." Shukra ta furta cikin kuka. Hannu ya zira a aljihu ya ciro wata atuwar goruba ba ta yi aune ba sai ji ta yi wal ya buga mata a goshi, ya juya ya ci gaba da tafiya. Azaba ta sa Shukra ta rushe da kuka, ga zurfin kwatar ya mata nisa ba za ta iya fitowa ba ga zafin dukan goruba a goshi. Kafin wani lokaci tuni goshinta ya yi wani malolo a daidai wurin da ya wala mata. Cike da takaici Dada ta rushe da kuka sannan ta ce, "Jama'a ku zo ya wace mini zanin jikina, ku kawo mini auki kwarto har uwar akin tsohuwa." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [12/06/2024, 12:03] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 52 · 0% Book details