← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 69

Sashe 45

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

su Lami za su haike mini." Uwani na daga aki ban da dariya babu abin da take she awa, saboda tsabar dariya har kwanciya ta yi asa. Suna cikin haka sai jin muryar Goggo Sala suka yi a bakin ofa ta fara lashe baki tana fa in, "Allah na gode maka da har yanzu lokaci bai ure mini ba." A zabure baba Isuhu ya aga Jafar, take jikinsa ya fara karkarwa ta fara tunkaro shi yana ja da baya. "Wayyo Allah Dada ki zo Goggo Sala za ta sa a cinye ni." A madadin Jafar ya gudu tun da ya samu ya tsira sai ya bi baba Isuhu da kallo, saboda ba aramin mamaki ya ba shi ba. Dada da ke cikin aki ta kai wa Uwani duka tana ce wa. "Dariyar me kike yi Uwani mu da ya kamata mu fara yun urin watar kanmu." Kafin Uwani ta yi magana suka ji baba Isuhu ya zuba ihu. "Wayyo ta shanye mini afafu, Jafaru, Dada ku zo ku kawo mini auki." Goggo Sala ba ta bi ta kan baba Isuhu ba ta shatalo afafuwansa za ta sunkuta shi a baya sai ga baba Mustafa da baba Idris sun shigo. "Subhanallahi kai Isuhu lafiya kuwa?" Suka arasa maganar suna arasawa wurin Goggo Sala, baba Isuhu da yake ya gama tsorata sai ji suka yi sharaf ya fa o jikinsu da alama ya suma. Suka kama shi suka kwantar a asa sai kawai Goggo Sala ta fashe da kuka. "Yanzu shi kenan rayuwata ta zo arshe." Da mamaki suke bin ta da kallo, Baba Mustafa ya dubi Jafar da ya yi la was a gefe ya ce. "Kai Jafar wane sakarci ne haka ake yi kai kuma kana zaune?" Jafar ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Baba ni ma ta kaina nake da tuni sun haike mini, dube ni wai fa ni zan shayar da mai sunan Malam." "Gara da Allah Ya kawo ku Idirisa, wallahi Isuhu shi da matarsa sun haukace. Ashe ba su ka ai ba har da Salamatu ita ma, an ya ba gamo suka yi a cikin gidan ba. Ban da haka wai ni Isuhu zai kawowa rigar mama ya ce na saka, sannan su dubi garjejen ato kamar Jafaru su ce ya shayar da me sunan malam." Baba Mustafa ya yi farat ya ce. "Shi Jafarun ne zai shayar da jariri?" Dada ta wara hannuwa ta furta. "Ta ya ni ji dai Mu afa, ka ga dai a kan idona aka haifi Jafaru. Kai arshe ma dai ni na yi jinyar shayin da aka yi masa ballantana na ce ko Jafaru ya koma mata-maza, Jafaru ko ka sauya daga baya zuwa mata-maza ne ban sani ba." A ufule Jafar ya ce, "Wallahi Dada kar ki ara ce mini mata-maza." Kukan da mai sunan malam yake tsanyarawa ne ya sa baba Idris ya yi wa Lami magana, sai da ta share wallar idonta ta ce. "An ce daga jiya kada na ara shayar da shi." A daidai lokacin baba Isuhu ya farfa o sakamakon ruwan da aka yayyafa masa. "Waye ya hana ki shayar da shi?" Shiru gaba aya suka yi, baba Isuhu ya dubi Lami ita kuma ta kalli Goggo Sala sai kawai suka fashe da kuka lokaci aya. Shiru akin ya yi kowa yana bin su da kallon mamaki, ban da Uwani da ke sakin murmushi a fakaice. Sai da suka yi me isar su sannan aka samu da yar Goggo Sala ta ce. "Ni kam na san wannan jawabin da zan yi ila shi ne na arshe a rayuwata don na san kashe ni za su yi." Baba Isuhu ya yi tsammanin bayanin 'yan ungiyar asirin da take ciki za ta fa a, don haka ya zuba mata ido sai ya ji ta ce. "Dama dai uwar garke ba..." Kamar ha in ba ki Lami da Isuhu suka ta fi da gudu suka toshe mata baki, da mamaki mutanen akin suka bi su da kallo. " arya take yi makira ha a ni da 'yan uwana za ta yi." Baba Isuhu ya fa a yana haki kamar wanda ya ci gasar tseren gudu. "Ba ma son shashancin banza da wofi Isuhu, sakar mata baki kada ranka ya yi mummunan aci." Baba Mustafa ya fa a a fusace. Babu yadda suka iya haka suka koma suka zauna jiki a sanyaye, baba Isuhu ya sunkuyar da kai asa gabansa na fa uwa. Goggo sala ta fara wassafo jawabi tiryen-tiryen tana hawaye. Tana gama jawabi gaba aya akin suka auki salati. "Kaico rayuwa ni Kulu me na ha a da sata da Isuhu zai janyo mini mugun hali cikin zuri'ata." Dada ta furta tana zubar da wallah. Malam na Madina da ke gefe ya ce. "An ya Isuhu yanzu rayuwar da ka auko mana kenan? Wallahi ka yi gaggawar yin istigifari kuma ka nemi masu kaya ka mayar musu da abin su. Idan ba haka ba muna cikin Firdausi kana Hawiya, atoh fa ar Allah ce ba ya yafe ha in wani a kan wani." Shiru akin ya yi kunyar duniya ta mamaye baba Isuhu shi da su Lami. Baba Idiris da baba Mustafa suka rufe shi da fa a sosai, don haka ya nuna nadamarsa a fili. Sannan baba Mustafa ya juyo wurin Dada. "Dada ki gafarce ni a game da abin da zan fa a amma tun farko ke ce kika ata Isuhu, saboda Isuhu yana an autanki kika auki son duniya kika ora masa. Hatta makaranta da Baba Sa'idu ya saka shi daina zuwa ya yi kuma kika goya masa baya, duk cikinmu shi ka ai ne bai samu karatun arabi da boko mai zurfi ba. Ga shi nan sana'o'in ma wacce ce ba a nuna masa ba amma kullin a tsalle-tsalle yake ba shi da aiki sai kame-kame, tun wuri ka yi wa kanka fa a domin kullin girma kake ara yi." Dada ta sharce wallar da ke fuskarta ta ce. "Yanzu dama Mu afa ka na da tarin nasihohin nan tutuni ba ka yi mini ba? Ni dai wannan maganar a rufe ta a nan kada Sa'idu ya ji don wallahi sai ya kusa cinye ni anya." Gaba aya suka amsa mata. "Dama wannan abin kunyar ai ba za mu bari ya fita ba Dada, yanzu dai a tambayi Uwani tun da ha inta ne ta yafe masa?" Uwani da ke gefe ta saki murmushin eta ta yi saurin cewa, "Ni dai Baba na riga da na yafe musu baba Isuhu ai tamkar mahaifina na auke shi." Da sauri Jafar ya dube ta don haka kawai ya ji bai yarda da kalaman Uwani ba. "Allah Ya yi miki albarka Uwani, dama a ba sai wanda ka haifa ba kaico rayuwa Allah Ya gafarta wa Yaya Umaru." Baba Isuhu ya fa a yana sharce wallah. Uwani ta saki murmushin eta a ranta ta ce, "Za ka ga a ba sai ka haifa ba." Baba Idris ya yi musu nasiha sannan ya ce shi da kansa a ranar zai kira su Aramma na gangare su yi saukar Al ur'ani a gidan gaba aya. "Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun auki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba. "Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi arfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya fa a, gaba aya suka amsa da Amin. Uwani na ha a ido da Jafar ta sakar masa harara, ha e da murgu a masa baki. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [09/06/2024, 12:01] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 45 · 0% Book details