Sashe 2
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA Jar mota irar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ima- iman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot in motar a bu e yake wa ansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu ri e da jarkokin magunguna suna agawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ura da jar asa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ara volum in recording in tallan magungun da yake yi. "Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku ku inku. Ina mai fama da sanyin ashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a ba ini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum in recording in, sai ya zuro kansa ta window ganin ya araso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce. "Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma an kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su." Baba Inu da ke kishingi e a kan benci ya tashi zaune, ya ance ido yana arewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba ba insa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer. "Kai mai magani, zo nan." Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking in motar yana kaikaitata a daidai ofar gidan. "Babana da Innata ga an baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa." Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. uri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai ba o ne a garin nan ko?" Mai maganin ya gya a kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai ba "Mi o mini wancan maganin na jarka, nawa ne ku insa?" Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da ji un itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya mi a masa yana fa "Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka aga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani." Baba Inu bai jira cewarsa ba ya alle murfin robar, ya aga ta sama sai da ya ga maganin ya are sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?" Horn in da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa. "Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun araso." Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya arasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya arasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya aga ya shanye. Da sallama ya arasa wurinsa ha e da fa "Yaya barka da hutawa." Baba Inu ya an kalle shi a she e ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?" Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya alau Yaya." Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a mi o maka maganin ne?" Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam." Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace aya har ya bugi irji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke." Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce. "Yanzu Yaya hanyar da ka auko wa kanka mai illewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da ji e-ji en magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci wa anda kake sha babu wata a'ida kai tsaye kake hanka a wa cikinka, kuma mafi yawa masu ha a magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu auki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba." Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa. "Yaya da ace ku en nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ananan wayayan ake sake yashe maka." Baba Inu ya ago fuska a ha e ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba." Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Na gama." "To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin za e ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini wayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura ba inciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin wayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba." Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka fa a, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na one maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba." A an tsorace Baba Inu ya dafe irji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce. "Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya fa a kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya hu u, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin aina ba." Ganin Baba Inu bai auki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce. "Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba aramin ata masa rai yake ba. Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da aton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara wa Komai ba in cikin tsololon ato. Wallahi sai dai ya yi ototo. Na zama kainuwa a wannan loto. aryar mai ba inciki ya ga bayana, har masu in sayan maganina. Yana gama fa ar haka ya fizgo aton buhunsa da yake ja da yar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da afar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a asa. Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce. "Wai Yaya dama kana nan ofar gida? Ikon Allah sannu!" Ya arasa maganar yana arin ri o hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ace ya ce. "Wallahi duk ba incikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan da e na yi arko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan ma iyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini ha in komai da ruwanka." Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya a ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya bu e ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe. Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta ri e da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce. "Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan." Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?" "Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare ahe an gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin an bokiti ban da son zuciya?" Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake su e hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada. Baba