Sashe 5
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
rungume yana jin zuciyarsa tana zafi ya ce. " an bishiririna, waye ya ta a ka? Me aka yi maka?" an Bishir ya sake narkewa yana wani tale baki irin na shagwa un yaran da aka sangarta ya ce. "Innaaaaaa! Inna ce ta dungure mini kai. Wayyo Allah kaina." Jikin Baba Saleh har karkarwa yake, saboda a duk duniya idan da abin da yake aga masa hankali ganin kukan an Bishir. Ya nuna Uwale idanu cike da masifa ya ce. "Sau nawa zan ce ki daina zalintar yaron nan Uwale? Ke wacce irin uwa ce kamar ba ke kika haife shi ba tsabar rashin imani, wallahi ba don kin ci darajar ke kika haife shi ba yau sai ranki ya yi mummunan aci." Ran Uwale ya gama aci ta nuna masa randar ruwan da suke sha ta ce. "Wallahi Mai gida wannan abin da kake yi ba soyayya ba ce, ata tarbiyyarsa kake yi. Dubi fa randar ruwan shan mu ya auki omo da mai ya zuba mini, don na dungure masa kai kake yi mini wannan tijarar? To wallahi na gaji, na gaji da wannan abin da kake yi mini. Kai kuma don ubanka ko yau ka sake yi mini irin wannan arnar sai na dungure ka." Uwale ta arasa maganar tana sakarwa an Bishir ozo a ka. Wata irin gantsarewa ya yi yana canyara ihu tamkar wanda aka caka wa wu a, a fusace Baba Saleh ya kai wa randar duka ta bada tus! Ruwanta ya mamale a tsakar akin, cikin araji ya ce. "Ba dai a kan randa za ki illata mini an Bishir ba? To wallahi idan ba ki da gaske ba, yadda na ragargaje randar nan kema sai na ragargaza ki." Baba Saleh ya yi furcin yana sunkutar an Bishir da zai yi shekara shida a tsaye, ya auke shi yana shafa bayansa zuwa kansa yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Ya rungume shi a irji cike da so, ya waiga yana wurga wa Uwale mugun kallo. Har lokacin an Bishiri bai daina tale baki yana kuka a shagwa e ba, Baba Saleh ya kalle shi har lokacin zuciyarsa zafi take ya ce. "Me kake so ka ci an Bishirina." an Bishir ya wale baki yana duban mahaifiyarsa tana mata harara sannan ya ce. "Namaaaa!" Baba Saleh ya sauke shi ya ce, "Don nama banza an Bishir, bari na je na yanko maka na zabi ko kaji." "Na zabiiiiiiiiii." an Bishir ya fa a a sangarce. Harara ya wurga wa Uwale sannan ya fice daga sashensu, yana zuwa ofar gida ya yi turus ganin abokinsa Sani yana ba wa yaro sakon a kira shi. "Ga ni na zo a daidai ya aka yi?" Sani ya are masa kallo tun daga sama har asa, sannan ya sauke idonsa a kan jakar wanzaman da ke rataye a kafa ar Baba Saleh. "Karenka ya kai tsaiko ko Sale? Wai har ni za a kira na cire beli na yi wa jaririya aski, amma sai na ji labarin ka yi mini shigar urtu alhalin ka sani ni an gado ne a harkar wanzanci ba an ka-ta-haye kamar kai ba?" Baba Sale ya saki tsaki cikin halin ko-in-kula ya ce. "To mene ne marabar dambe da fa a? Don kana an gado ka koya mini harkar wanzanci, na zo ni kuma Allah Ya saka mini nasibi duka costomers inka sun dawo wurina wani avu ne? Wai ma da kake wannan abin, kai da kake jin ka an gado da ni ta-ka-haye ba duka wanzamai za a ce mana ba? Kai matsa ka ba ni wuri an Bishiri ya aike ni, don aikensa ya fi mini wannan sokiburutsun banzan da kake yi mini." Baba Sale ya gegara ya wuce shi, ya nufi wurin Sadau mai nama. Bayan fitar Baba Saleh cikin takaici Uwale ta auko zani ta shiga tsane ruwan tana matsewa. Mugun kallon da take jifan an Bishir da shi ya sa ya yi saurin ficewa daga akin. Kai tsaye sashen Baba Inu ya nufa don tun da ya ji shiru ya san abinci suke ci. an Bishir irin kwa ayayyun yaran nan ne da duk abin da suka ga ni, za su ce suna ci koda a hannun babba ne. Sangartar da Baba Sale ya yi masa ce ta sa ya koyi wannan mummunar abi'ar. A lokacin da ya shiga sashen Baba Inu da bencinsa ya fara cin karo, ya hangi Baba Inu a can ofar akinsa yana rabawa yaransa wa ansu ananun alewa. ragowar naman kazar da ya gani ya saka hannu ya auka, ya kai ba ki ya fara zuge tsokarta yana lumshe ido. Sai da ya gama cinyewa tas, sannan ya auki kindirmon nonon da Baba Inu ya zuba magani ya aga kansa ya aka, a shagwa e ya wurgar da kwanon asa bayan ya shanye ya auki ashin kazar ya fara tauna. arar jefar da kwanon ce ta ja hankalin Baba Inu, da yara da suke gabansa. Ganin abin da an Bishir ya yi ya sa Baba Sale ya arasa wurinsa rai a ace ya kai masa duka a baya. an Bishir ya tale baki a shagwa e ya saka kuka yana yi wa Baba Inu da uwa ha e da fa "Uwakaaaa!" Zuciyar Baba Inu ce ta fara tafasa, ya saka hannu zai dake shi da sauri an Bishir ya fita da gudu yana fa "Allah Ya isa." Zucya tana tafasa Baba Inu ya rufa masa baya, suna zuwa mararrabar hanyar da take ha a kowa da ke cikin gidan ya samu nasarar cafko shi, bai yi wata-wata ba ya tsinke shi da mari. A daidai lokacin Baba Sale ya arasa wurin, ganin abin da aka yi wa an bishir ya sa shi wata irin zabura a haukace ya yi kukan kura ya tunkari wurin da suke tsaye. Share pls 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam : *GIDAN LIKITOCI*