← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 69

Sashe 3

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta." Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari. Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. San ira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a ha e ta ce. "Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!" Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?" Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce. "Ke Laraba waye wannan?" Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban ahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa." Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna Huwaila wacce ta kai arar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta sake ance ido ta ce. "Wannan kam Lado eya ne!" Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado eya dama ka dawo daga Legas?" Haushi ne ya lullu e mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon acin ranta. Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga mata gigitaccan mari, har sai da ta ga wa ansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe kunci saboda marin ba aramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko. A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake auke fuskarta da mari, abinka da farar fata lokaci aya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya aci ta dube shi a fusace ta ce. "Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..." "Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike aure mata, wallahi mai gari sisina ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da maha i kusan dubu biyar na kashe." Sa'a mai ragadada ta fa a a ufule. Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya mi e tsaye yana bu a kafa u ya ce, "Inno tun da haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan ai ali ya ji irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ila ma ya aikata gidan yari." Jin haka ya ka a hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce. "Ke Laraba ki yi magana." Laraba ta yi wa Mai gari uri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya ka a amma sai ya basar ya ce. "Laraba kin tare ahe kin cinye masa ragadada kin tula masa asa a ciki, ita kuma Huwaila kin jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?" Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado eya tun da ka dawo garin nan yaushe muka ha u da kai!" Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu Laraba ta rasa da wa za ta ha a ni sai Lado eya?" Mai gari ya kalli San ira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin San ira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya mi a wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai fa uwa yake yi. Rai a ace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta are ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu. Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi. Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da wa a, saboda tun da suke ba su ta a ganin abin da ya saka Laraba kuka ba. Laraba mai kuka ye ye. Ga majina da yawu ahayye. Gobe ma ta ara ye ye. Ku zo mu yi mata an tusa a tsakar ka. Idan suka kai baitin wa ar sai su arasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka. Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce. "Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa kenan. Ina Inno take?" Cike da jin haushi a da ile Inno ta ce, "Ga ni." "Za ki biya Huwaila da Sa'a ku arnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce. "Ai kuwa ba za ta sa u ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya." Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta mi e zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki. Don irin zaburar da ta yi ba aramin tsoro ta ba shi ba, ba shi ka ai ba, hatta ragowar mutanen wurin sai da suka ja da baya. Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su aya bayan aya abinka da mai manyan idanu sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu aya bayan aya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon mutanen gefensa Tana zuwa arshe, sai kawai suka ga ta iba a guje ta fice daga cikin fili ta nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana fa "Laraba! Ke Laraba ina za ki je?" Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce. "Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin nan." Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta auke da wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da wabi a haukace tana wani irin araji. Lokaci aya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau uku babbar rigarsa tana ta e shi. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam : *GIDAN LIKITOCI*
Chapter 3 · 0% Book details