Sashe 29
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
muke shirin fa a kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina arfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce. "Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake na ewa." Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya na e su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa na in da ya fi na huhun goro." Gaba aya suka saka dariya. Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma li is, saboda bayan likita ya gwada an Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matu ar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana an wari. Likitan ya garga e su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani an matashin saurayi. "Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?" Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce. "An tafi da Baba ofishin 'yan sanda azu." Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?" "Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar anjamau!" "La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. an Tasi me kunnuwana suke zu o mini? Kada ka ce mini an Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi ri e ni da arfi duhu nake gani." Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin iban karan mahaukaciya da shi. Da sauri Tasi'u ya ri e shi yana kiran sunansa da arfi, "Baban an Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake fa a sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan." Kamar sabon an maye haka suka tafi Tasi'u yana ri e da shi, don har suka arasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani. "Wallahi tallahi yalla ai ban ta a sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son fa a. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori uruciya ba..." Wata irin ara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya fa a ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji afafuwansa ba za su iya aukarsa ba. Kalaman Bala na arshe suka sa ya ga wani ba in duhu ta lullu e idonsa, numfashinsa ya auke. "Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?" Wani kurtun ansanda ya arasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station in. Ruwa aka ebo aka zuba masa, a hankali ya farfa o yana daga kwance yake kallon mutane ai. Ya yun ura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Yalla an Bishir, kun bincika mini an Bishiriri." Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?" Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yalla ..." Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfa owa. Sai dai su kansu abin da ya fi aga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfa owa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfa o ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki. Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara wala masa kira. "Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama." "Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?" Baba Labaran ya furta a zafafe. Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata fa an da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin fa a a maganarta ba. "Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu aya kamar ha in baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce. "Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka ro a." Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana fa in. "Kanki ake ji, ni na gama fa ar ra'ayina." Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ora hannunta a kan aramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Ha a Labaran ya cika butulu." Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya. Damuwa ha e da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar ha in baki, lokaci aya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan oye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya kara e ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana ha e rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama. Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta fa o masa. Ya saki murmushi ya nufi ofar gidansu. aramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a auki lokaci ba ta fito tana taunar cingam. "Haskena ashe kaine da yamma haka?" Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke ka ai ce hasken da ke yaye duhun da ke anfare a ciki." Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa ku i har dubu goma ya mi a mata. "Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma hasken zuciyar Inusa." Alewa ta bu e ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta mi a masa cike da kissa. Cikin so da auna Yaya Inu ya kar i alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata atuwar Mp3 da wani faffa an kwando mai auke da magungunan maza a ciki. "Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tu a sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza ka ai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar kar a, indai matsalarka a angare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka kar a sadakar alilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida." Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya arasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya arasa ta wurin zai wuce. "Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?" Cewar Gambo. Mai maganin ya ago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?" Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?" Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi." Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce fa uwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan