Sashe 35
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel inmu. SHAFI NA SHA UKU Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ago cike da shau i ya ce. "Innota! Haba Innota, me ya sa kike son aga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki a ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta mi e za ta fita da sauri ya ce. "Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?" Inno ta jingina da jikin ofa ta ce, "Abin kari zan ha a mana..." "Allah Ya sawa e ki fita ki ha a kayan abinci, da kanki kina fama da anyan jiki." Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji da in kulawar da yake ba ta. "Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar in nan." Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?" Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar in banza, ni duk yawan ku i ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya mi a mata, sai da ta auka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata. "Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya." Daga can angaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso." Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya." Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya kar e ki tsohuwar nan." Inno da Goggo suka saki dariya lokaci aya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta aga zuwan sai daga ba ya. Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yun urin bu e idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara bu ewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. anladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan arfe tara na safe. anladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya bu e idonsa ya ci karo da akin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya aci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar akin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a asa tana munshari. A fusace ya arasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta mi e tsaye a gigice. "Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?" Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da akin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?" A harzu anlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama." "Ashe kuwa zan yi miki arin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a asa. Wallahi yau sai kin gane ke aramar waya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta mi e tsaye tana ka ugu ta ce, " wayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan anladi, ganin haka ya sake a ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar arfin namiji da mace ba aya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta auki wani burugali a bayan ofa ta ran wala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa anladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har ha orinta aya na gaba ya fa o. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai she i yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka fa i gefe, ba a auki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin anladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?" Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda acin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta fa o jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi ha uri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi acin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji da i saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a ha e ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya." Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta da e ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan arnar. "Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba, ta ta e baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ru u-ru "An ya akin nan babu aljanu kuwa?" Ya yi tambayar cikinsa yana ka awa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." aladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga arshe dai ta ha ura. Shi da kansa ya shiga gyaran akin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta ta a komai ba. Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake kar ar ku i a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci aya ta yaye, ya mi e a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. ofar gidansu Zuly ya arasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta bu ata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Wa annan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami wa ancan mutanen, na fara shirin tafiya aurin aure." Zuly ta an yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce. "Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali." Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon ku in magungunan da take bin ta. Saboda ba aramin ha i ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta auki ciki. Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga akin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya ha a kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba aramin aga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi da e lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?" Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba." Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi da e, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?" Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nu usar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun