← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 69

Sashe 42

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA UKU Ilahirin arfinsa Malam na Madina ya ware yana cakumar Jafar, idan ya dun ule hannu sai dai ka ji dum! Ya kai masa dundu a baya. Shi kansa Jafar ya yi mamakin arfin dattijon duk da ba fin arfinsa ya yi ba. Na Madina da ya ga ya auki lokaci bai kai Jafar asa ba, ya zuba wata uwar kabbara tamkar wanda yake tsakiyar ya in musulmai da arna yana fa in. "Allahu Akbar." Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta ebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta bu e idonta. Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shai an. Jafar ya ha a hannuwan dattijon wuri aya ya mur e su sannan ya ce. "Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka aya bayan aya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance. Tamkar an biri sai ga na madina ya yi tsalle ya fa asa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga akin. Kai tsaye ya wuce akinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce. "Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta aga an yatsa aya ta ce. "Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah." Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arzi i Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce. "Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta an wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo. "Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce. "Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna ha a ido kamar ha in baki suka fashe da kuka a tare. "Uwani maza auko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka. Da sauri Uwani ta auko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman. "Maza kira mini Mamman." Uwani ta kar i wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gya a kai. Uwani ta kira tana jin an auka ta mi a wa Dada. "Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..." "Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk fa in duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe. "Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye. "Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki wara daga Soja, Rosafti sai an sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba. "Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..." "Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe. Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba aramin aci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce. "To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara auke- auke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas in nan ya fara 'yan zu e-zu e ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya aci." Dada ta an yi jim sannan ta ce. "Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta mi e har za ta fita sai kuma ta wuce uwar akin Dada tana sakin murmushi. A can ashin gado ta ciro bankinta ta ulo ku en da suke ciki, sai da ta irga su kusan dubu aya da ari biyar ne. Ta aure su a ankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake. Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa fa a sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can asan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga ban aki ya watsa ruwa ya wuce akin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba. Uwani na fita can kantin an bala ta wuce ta sayo alawa irin da ra in suna leda biyu, sai ta arasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ai sannan ta aure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta arasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba. "Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara. "Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta fa a tana mi a masa ledar hannunta. Da mamaki ya kar a ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce. "Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban ta a sani ba sai yau?" A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce. "Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..." "Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance shar an. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a ban aki da kuma akinsa. "Eh matar ce na ga afarta da kofato, sai ta mi o mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na fa a maka idan ka wurgar da sa on nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta fa a ya sa jikinsa na rawa ya ha a ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce. "Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin acewa ta yi don kamar iftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi afafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa. Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya fa a cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo arshe. Uwani na daga akin Lami ta hango shi nan da nan ta unshe dariyarta, yana shiga akin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba. "Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta mu e ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar ban akin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka. Lokacin da Uwani ta je wurin ban akin Goggo Sala ta riga da ta tu e har ta fara wanka, a hankali ta sa a ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta sa a sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai an
Chapter 42 · 0% Book details