Sashe 67
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA BIYAR *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* an gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* ar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa* Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti." Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta arasa wurin Mami da ke shar e a asa. Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi. "Kai Jafaru, wai ya aka yi adangare ya shiga har ban akin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina aki." Daga haka gaba aya suka yi jigum-jigum. Abin ka da mai iba Uwani da ta ago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da yar Uwani ta samu ta ja Mami a asa kamar rago, ta arasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta auko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta auko ai kuwa Uwani tana aga wa ta fa i a wurin tana yata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta mi e ta fara kiciniyar saka wa Mami. Da yar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta le a waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka kar i Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa. Lokacin da Mami ta farka gaba aya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yun ura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana fa in. "Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya ri o ta, Mami ta ago kai tana are masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gaba aya su fita, don yana son ba ta kulawa babu bu atar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba aramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita. Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti aya ba ta sake farfa owa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas ma ale a idonsa. "Wato wannan karon riki e mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na waci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk wa annan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko iftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu. "Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yun ura ta tashi zaune tana an dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon arfen nan da ake ma ala ledar arin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwa a masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta aga arfen ta ba shi wal. Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar akin yana fa "Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa arfen tana fa "Wato don ubanka har surar Nasara kake riki ewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya ta are cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient in nan za ta halaka ni." Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su bu ofar, sai dai da yake Mami na jingine da ofar tana jin alamun za a bu e ta sake danna ofar da arfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya fa ashin gadon asibitin, da yar su Daddy suka turo ofar suna ganin ta da arfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya mur e hannun Mami ya kar arfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu aya bayan aya sannan ta ce. "Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?" Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga akin, glass da takalmansa kusan lokaci aya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar akin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ebi abin sa. Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana fa in. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar aramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru. Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar adangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin ban akin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su ka ai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na raku e a gefe ta yi zuru tana arewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zu e a wuni guda, suna ha a ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe. Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da yar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata arin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko ka an ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta i yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta. Su Shukra sun auki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya auki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya issima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a aura musu aure. Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara fa uwa a hankali ya yi ta maza ya arasa jikin gate in ya fara wasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta. "Waye nan?" "Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya mi a masa mukullin motarsa ya ce. "Shiga ka tu o motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya da e ni da ko mashin ban iya tu awa ba, ina ni ina tu a mota?" "Lado amma gidan nan ba ku ka ai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da arfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce. "Ranka shi da e naka ai mai sau i ne." To yau dai in fa a maka tik da ka sani haka adangare ya tarfa Hajiya tum ur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gaba aya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka ta a jin adangare ya auri mutum? Wai adangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka ta a ganin adangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana adangare? To azun nan sun zo iban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta fa a mini." Take cikin Salim ya sake ka awa, ganin ya an fara ja da baya Lado ya ce. "Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har adangare zai auri Hajiya ni waye da angaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta mur ushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa