← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 69

Sashe 11

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA AR DAULA AN YA BAIWA CE? AN BA ARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYAR Ko ka an Indo ba ta damu da ganin arnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a angaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri aya, ta fara mi a masa hannu aya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su mi a wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta mi afa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi afarta ta har o labulen akin ya fa o a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya aci kamar ya tashi ya sha e Indo, saboda wannan sabon iskancin da take arin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara ka o cikin akin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara ka o fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ance murya ta ce. "Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..." Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta fa asa da as! Gwiwoyinta suka bugu da asa. A tsammanin Indo shau in da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wur ila idanu da sunan fari tana wani ban arewa kamar kazar mayu ta ce. "Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..." Takaici ya sake lullu e Yaya Inu, ya aga hannu ya yi wa Indo mahangur a a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta mi e da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da afarsa ta fa a kan miyar kukar da ta zubar. A fusace ya aga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita." Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..." "Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika ha u da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ofa Hansatu da Larai suka araso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta unshe dariyarta cike da eta suka koma aki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan amshi da kallon wula ancin da ta dinga yi musu. A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini aki tas, kika ebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta arasa ta zare rigar mamanta da ke sa ale a wuyansa. Ta auki zaninta ta aura sannan ta shiga kiciniyar gyaran akin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta. Washegari Tun kusan kimanin arfe hu un asuba ya farka yake shar a kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan fa uwa, da sauri ta zaro aramar wayarta a ashin filo ta haske angaren da an Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce. "Me yake faruwa mai gida?" A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin an Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da an Bishir ya yi kusan shekara aya da rabi kenan. "Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake." Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta. Baba Sale ne ya fa a jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce. "Kamar kin manta yau ne za a yi wa an Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika." Baba Sale ya yi maganar yana share walla, ha e da shigewa jikin Uwale kamar wani aramin yaro. Ya ago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce. "Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai ta a lafiyar an Bishir ba na son shi..." Kuka ya sake cin arfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce. "To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci." A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya auro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya arasa masallaci a raka'ar arshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a aya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya aga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi arfin halin zuwa kusa da shi ya ce. "Sale me yake faruwa ne?" Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina bu atar addu'arku. Domin kowa ya san ana aya ne a duniya wato an Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da hu u sai dai kash..." Kuka ya sake cin arfinsa. Gaban su Baba Labaran ya fa i, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka auka mutuwa aka yi masa. Cikin ha in baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce. "Sai dai me?" Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce. "Ku yi mini fatan a yi a gama wa an Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da arfin zuciyar ta guntule an Bishir." Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce. "Kai dai ka zama gantalalle an wahala. Yanzu shayin da za a yi wa an Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace." Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ace. aya bayan aya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka an Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Tun da an Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya auke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin arfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka arasa ofar gidan, Uwale ce ta iya aukar an Bishir ta mi a masa. Domin Baba Sale uwar aki ya shige ya ha a kai da arfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana agawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da yar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya shar a. 'Yan'uwansa ya gani gaba aya a zaune, ya yi mamki matu a don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su aya bayan aya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji da insa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku baki aya." Fuskarsu auke da fara'a gaba aya suka furta. "Ma Shaa Allah, gaskiya wannan abin farinciki ne Inno. Allah Ya sa mu dace." Inno ta sake washe baki fuskarta wasai kamar gonar auduga ta ce. "Amin Ya Rabbi." "Amma Inno wanne abin farinciki ne haka?" Baba Labaran ya tambaya. Inno ta rangwa a kai gefe ta ce, "Dama zan sanar da ku mun gama daidaitawa da Malam, don haka ma na ce zan sanar da ku a aura mana aure ranar Juma'a mai zuwa." Sororo gaba aya suka suna kallonta cikin mamaki Baba Ibrahim ya ce. "Inno aure fa kika ce?" Inno ta ha e rai ta ce, "Eh sunnar Annabi!" Ajiyar zuciya Yaya Inu ya yi ya ce, "Yanzu Inno tuntuni ba ki yi aure ba sai yanzu? Saboda Allah tun da arancin shekarunki bayan da Baffa babba ya rasu ba ki yi ba sai yanzu da girma ya
Chapter 11 · 0% Book details