← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 69

Sashe 24

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A angare aya, yawan zu ar taba da shan giya duk yana daga cikin abubuwan, da za su iya saka wani sashe na jiki ya dinga motsi, kamar ki ji hannu, ido ko tsokar cinya tana motsi. Idan kina son gujewa haka, sai dai ki kiyaye wa annan abubuwan da na lissafa, yawaita shan ruwa, samun hutu da bacci da yawan cin kayan marmari. Masu zu ar taba kuma, muna ba su shawarar guje wa zu ar taba da shan giya, ha e da takatsantsan wurin shan magunguna masu auke da caffeine. Idan kuma matsalar ta ta'azzara sai mutum ya wuce asibiti, domin ya ga likita." A fusace Inno ta wawauro muhuci ya ra a wa Fadil ta ce, "Fice ka ba ni wuri, mutumin banza da wofi. Yanzu ni kake zama ka cewa ina shan giya, giya fa boka..." Sai kawai Inno ta arke da kuka, Fadil ya fice yana shafa kafa a don dukan ba aramin shigarsa ya yi ba. Tun daga aki su Hansatu, suka fara jin yadda Yaya Inu yake wurgo ullin kaya da kwanukansu tsakar gida. Kusan lokaci aya Hansatu da su Indo suka yi carko-carko, a ofar akin suna kallonsa. "Mai gida Lafiya wai? Dubu yadda kake jefo mana kaya tsakar gida." Hansatu ta fa a tana tattarawa kayan wankinta. A daidai lokacin Yaya Inu ya sake wurgo wata tukunya da farantin Indo suka fashe lokaci aya. Ranta ba aramin aci ya yi, ta kwashe cikin masifa ta ce." Malam mene ne haka muna magana ka yi shiru?" Yaya Inu ya tako yana kallonsu a wula ance ha e da yamutsa fuska kamar ya ga kashi, ya dafa ofar akin ya yi bake-bake ya ce. "Gaba ayanku ku kwashe mini wannan tarkacen haukan, saboda gobe za a aura mini aure. Kuma a yanzu ne na san zan yi aure, zan auri farincikina mai faranta mini rai. Wacce ta san mutumci da imar aure, tun a yanzu ta fara shagwa a ni tana lailaya ni. Wallahi idan ta zo duk wacce ta koya mata azanta da mugun hali sai na ci mutumcinta. Saboda a kullum idan na kalli ku fuskokinku kama kuke yi mini da sumammun birirrika." Da sauri Hansatu ta saka hannu ta rufe bakinta saboda mamaki da acin rai. "Mai gida cin zarafin naka har ya kai ka kira mu da birrai?" Hansatu ta fa a a zafafe. Indo tana shirin yin magana, suka ji muryar Abu ta shigo gidan tana fa "Yawwa Goggo, mun zo a daidai ma ga shi nan yana gida." ata rai Yaya Inu ya yi yana ance ido ya ce, "Bayan na warware igiyar aurena da ke, uwar me ya kawo ki gidana da farar safiya Abu?" Abu ba ta tanka masa ba, tana zuwa ta aga hijabi ta mi a masa jaririya. Ba Yaya Inu ba, hatta su Indo zaro ido waje suka yi suna kallon yanayin kalar jaririyar. "Ke mene ne wannan? Kuma waye uban wannan abin?" Yaya Inu ya furta yana janye jiki cike da yami. "Kai ne ubanta, kuma a haka ta zo duniya." Ganin kamar Yaya Inu ba zai kar a ba, ya sa ta dire masa jaririyar a asa. Kwana biyu na yi nisan zango, bayan na anyi rashin lafiya sai kuma muka shiga biki. Na gode sosai da kulawarku, Allah Ya bar zumunci. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam : *GIDAN LIKITOCI*
Chapter 24 · 0% Book details