← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 69

Sashe 60

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ebi kudina ki ba shi." Ta arasa maganar fuska a ha "Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa. "Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?" "Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da ku inki har ma ya ara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici. "Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki ku in nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko ka an." Indo kishiyar Maryama ta furta asa- asa. "Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani da in zama da shi suke ji ba. Wuni aya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman uncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da yar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka ka a, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan. Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta auke shi ta oye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya fa o mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ayan hannunta auke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ofa turakar Aramma take, daga akinsa kuma sai akin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta iba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta le akin ta hango Aramma a kwance ya shar e sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu iba ga uban tumbi. Tana shiga akin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya mi e yana dafe da goshi, "Wane an iskan ne a tsohon daren." "Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta fa a da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta bu a shi, sai ta ara fa i ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi. "Mu sababbin awayen 'yarka da ta ba unci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shai anu ne domin fatattaka an adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani mi a wuya gaba. Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce. "Ku dubi Allah ku yi ha uri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi. "Zo nan maza-maza, matso nan." "Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya fa a fuska ha e da hawaye da majina. "Za fa ka taka an tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa ti i-ti i sai ha a gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a asa, hannun Uwani mai auke da ludayin da ke cikin hijabi ta aga da sauri ta sake ba shi raaal a eyarsa. A zabure Aramma ya mi e sai da ya yi tsalle uku ya fa i a can gefe cikin azaba. "Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu kar e musu kake yi, a jiya ma ka kar e wa uwar marigayya ku enta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai ku i. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ungiyar asiri aiki, za ka zama ku i wayyo ku i, ku i masu da i." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana aga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama. "Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ara mata yanzu zan ara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce. "Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su ka ai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake arkewa da kuka. "Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya ha iye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu aga maka afa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu ku inta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa." "Duka na ji kuma na yi al awari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa. "Ba ma bu atar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..." Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka. "Wallahi na ha ura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari." "To kuwa ya zama wajibi ka za aya, ko mu auke ka ta arfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce. "Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta ora da cewa. "Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matu ar ka le o to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagi ewa gefe tana tura wuya gaba. Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya arama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon akin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan akin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya uri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya aga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma asa- asa, da ita kanta sa on fatalwar da take fa a. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ofar akinsu tana an wani gurnani, take fitsari ya ji e zanin Yaya arama. Uwani na aga labulen akin ta hango yadda aka jere yara a asa, aya bayan aya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya arama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa afarta, jiki na rawa ta ce. "La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah." "Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe wayar idonki." Uwani ta fa a da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma wa ancan yaran zan ba wa ananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na arasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta auko yaro aya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin aki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya arama suka banka uwar aki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana fa in. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [13/06/2024, 13:37] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 60 · 0% Book details