← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 69

Sashe 59

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TAKWAS Uwani saboda dariya har kwanciya ta yi a asa, Ba ka da nauyi ya arasa wurinta tun bai yi magana ba ta mi a masa ayar ullin gya "Ba ki da nauyi ta yi malolo." Haka yara suka dinga yi wa Shukra wa a suna tafi, ban da kuka babu abin da take yi saboda tsananin kunya da acin rai. Da yar wasu matasa suka kori yaran suka yi kama-kama suka tsamo ta a cikin kwata. Tana tafe ruwan kwata na iga wasu daga cikin yaran suka fara yi mata wata wa oyi, oyi oyi. oyi damalma kashi. oyi tukunyar kashi. A haka Shukra ta arasa gida nan ma wasu daga cikin tsurarin yara suka bi ta Uwani na take musu baya, Shukra na shiga sashensu ta arke wa Mami da wani irin kuka. "Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim in?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu aya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta fa a musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ofar gida. Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai an tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta ta a sauya kaya a gaban mutane. "Dada lafiya?" Hannu na rawa ta nuna uwar akin. "Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar aki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka le akin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke du e a ashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isu hu, da sauri ya arasa hannunsa auke da atuwar gora ya fisgo Salim. Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya. "Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?" Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku oye ni. Ya auke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya mi a wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta. "Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa azu kana ofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka arasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi. Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta auka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta. "Ke kuwa Maryama da uruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba." "To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da ha uri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta. "Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika al awarin da aka auka, Uwani dai an aura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji da i don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin aurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta. "Dada dama kiranki na yi na fa a miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata al awarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta mi a wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama. Kimanin arfe goma na safe su Dada suka isa auyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gaba aya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki. "Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da aryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana dur ushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya." "Barka dai." Dada ta amsa a da ile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta mi e tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa. "Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta fa a a ranta. Maryama jiki a sanyaye ta mi e za ta wuce da su aki. "Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin ba i ba za ki kai su aki ba." Aramma ya fa a cikin fa a shi a dole sai ya birge su Dada. aki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji da in irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da ha uri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo ku in sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ari biyar mai dubu aya duk suka ha a mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun auki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata ra "Dama ku in da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gya a kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana aga musu hannu. "Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta fa a tana tura ba ki gaba. Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce. Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo. "Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan ha a a yi abincin rana." Tamkar kazar da wai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta mi e jiki ba wari ta kunto ku in wurin su Baba Idris ta mi a masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye ba in halin tsiya ne." Ran Maryama ba aramin aci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ace ta ce. "Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya auke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta. "Baba bari na mi o maka ku in a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na mi o maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza mi o mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama." Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba ku in a ciki, ta ebo su duka ta mi a masa. "Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin annen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da ba en maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu aya bayan aya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya. Sai da mutane suka ragu a akin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta
Chapter 59 · 0% Book details