← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 69

Sashe 39

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce. "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana fa "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kala a. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na kar o miki ayi, ni za a kashe da ullutun ba inciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi. "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya auke mini uwar garke ya mi a wa Mai gari ta katanga." "Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga akin tana fa in, "Wallahi ko sama da asa za ta ha e sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya auki karkarwa don haka ta mi e cikin sauri ta bi bayan Uwani. Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa aya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya mi a wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke. "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya bu ofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" "Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. "Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lullu a wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ora a saman tashi, cikin mamaki ya furta. "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da irjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk fa in gidan nan a rasa wanda za a la a wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya aryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne arawon da kuke zargi a fa a mini nawa ne ku inta zan biya." Ganin yadda ran Baba Isuhu ya aci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna da ar ha e da rushewa da matsanancin kuka. "Tsakanina da wannan arawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai ha a mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata atuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka. "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya ka ai zan saya miki ba, kina son an mara in sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa an mara in sa. Saboda haka ta gya a masa kai tana goge hawaye, a gefe aya tana kuma udurtar irin fansar da za ta auka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gaba aya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake auka ta fito kamar za ta ban aki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin san a, ta ci sa a bai rufe ofa ba don haka tana la e daga bakin ofar akinsa ta ji Lami na fa "Isuhullena ai ka birge ni da ka aryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama arje dabgen kan uwar garke." A gefe aya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. "Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu le a ka gani..." Lami ta fa a da sauri. "Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki le a mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin afarsa har tsakiyar kansa. "Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta fa a a tsorace. "Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke la e ta sake ma ale murya ta fa a da yanayin kukan uwar garke, tana gama fa a ta dokon auren akin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka fa a uwar aki, Goggo Sala da ke aure da aurin irji tun a falo zanin jikinta ya fa i ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ofar uwar aki ita kuma Lami ta ma ale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar an fatarin (Under wear) da ke ugunta, ga irjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a asa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke ri e da an fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce. "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa anwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya mi e tsaye sai jin irjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana agowa suka ha a ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini irji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam [06/06/2024, 10:23] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ASHIN GWIWA*
Chapter 39 · 0% Book details