Sashe 61
Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TARA Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya arama ce ka ai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar akin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta fa o uwar akin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ofar uwar akin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wu a a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru an wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce. "Ga wani wage da shi za mu fara." Uwani ta arasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara hu u ba. "Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don iri- iri ya ga wu ar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan aya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya arama ta ce. " arama don Allah ku kawo mini auki Naziri zai tafi." Yaya arama da ke uryar uwar aki ta ce. "Sa'a ki ha ura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi ka ai ne anta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ran wala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta fa a uwar akin tana fa in. "Wayyo Naziru." Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana fa in. "Iyata wayyo Iyata." Yaya arama ce ta yi sauri ta banka ofar akin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya. "Idan kun rufe ofa za mu ullo ta ashin asa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu bu atar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi aya bayan aya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun sa ule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da argon jikinku. Amma za mu aga muku afa zuwa nan da an wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a iyama." Uwani ta furta a lokacin da ta fita da Naziru tsakar gida da ke wala ihu. A yadda ta lura kusan ilahirin mutanen gidan duka sun tashi, wata dabara ce ta fa o mata don haka ta buga tsalle a tsakar gidan ta ce. "Wa anda kuke le enmu muna gano ku, ke wato har da ke ko. Wallahi aya bayan aya za mu bi ku mu wale idanunku idan ba ku koma kun kwanta ba." Ta saki hannun Naziru ai kuwa da gudu ya fa aki yana ihu, sai ta tafi da gudu ta nufi akin mahaifiyarta, a guje ta ji mutanen akin suna shigewa uwar aki wasu na hantsilawa. Nan ma ta nufi akin kishiyar mahaifiyarta ta razana su, sai da ta tabbatar da sun gama tsorata kowa ya shige uwar aki sannan ta lalla a ta isa ban aki ta wanke fuskarta. Ta du une hijabin Inna Suwaiba ta soke a hammata, sai da ta shirya sosai sannan ta nufi akin mahaifiyarta da gudu tana fa in. "Wayyo Allah! Ku taimaka mini za su ara janye ni." Tana shiga akin ta tarar falon mahaifiyarta babu kowa an banke uwar aki sai ananan yara da ke kuka suna buga ofa, saboda kada a gano Uwani ita ma ta fara bubbuga ofar tana ihu. Da ta lura ba za su bu e mata ba sai ta janyo ofar falo ta datse. Har aka yi assalatu babu wanda ya yun urin fitowa daga akin, duk da duka ba in gidan a zuciyarsu kowa ya ayyana gari na wayewa tafiya zai yi. Amma da sun tuna kashedin da aka yi musu a kan kada wanda ya bar gidan har sai an yi sadakar uku sai jikin kowannensu ya yi sanyi. Sai da gari ya yi tangararan sannan Indo ta yi arfin halin bu ofa, kamar sababin munafukai haka mutane suka dinga le owa aya bayan aya suna fitowa suna yin alwala suna sallah. Duk wannan abin da ya faru bayan da gari ya waye babu mutum aya da ya jajantawa kowa, domin kowa a tsorace yake. Su Uwani suna zaune sai ga Aramma ya shiga akin kansa ya yi wa ansu ulalai sun fi biyar, daidai tsakiyar hancinsa har wani ja ya yi yana mai o. Da mamaki suka bi shi da kallo, Aramma ya zauna da ar jikinsa zafi zau da zazzabi. Gaishe shi mutanen akin suka yi, suna son jin abin da ya faru da shi suna tsoro. Hannu ya sa a aljihu ya zaro ku in ya ce. "Ungo wannan Maryama, ku inki na jiya ne. Wannan kuma kyautar dubu hamsin ce na ba ki ita ma Indo zan mi a mata nata." Baki sake Maryama ta bi shi da kallo, ta ce. "Malam dubu hamsin fa? An ya ba mantawa ka yi ba?" Aramma ya dube ta a fusace da ya tuna garga in fatalwa sai ya wayance ya sassauta murya ya furta. "Maryama shaidar da za ki yi wa mijinki kenan? Kyautatawa ce kawai ta sa na ba ku." Maryama hannu na rawa ta sa ta kar a tana zuba masa godiya, Aramma har ya mi e zai fita Inna Suwaiba ta ce. "Aramma ungo shafa-shafa sai ka shafa a malolon nan na ka, Allah dai ya sawa e sanyi haka yake lokaci aya ka ga wuri ya luluye. Ko kuma bige wa ka yi ne da dare?" Aramma da ba ya son a ja doguwar magana ya kar a ya yi gaba ba tare da ya amsa mata ba, akin Indo ya fa a ita ma ya sallame ta ya koma akinsa don ilahirin jikinsa ciwo yake masa. Aramma na shiga aki sai ga Indo jiki na rawa ta shiga wurin Maryama suka fara tattaunawa cikin mamaki, ba su ara nutsa wa a tekun mamaki ba sai da suka ji Aramma ya ce a yi shinkafa da miyar dage-dage da rana. Wannan sabon sauyi da suka samu daga wurin Aramma ba aramin da i ya yi musu. A na gobe Uwani za ta koma gida wurin arfe goma sha biyu na dare ana zaune ana an hira, ta hangi Aramma ya suri buta ya yi ban aki. Sai da ta tabbatar da hankulan mutane ba ya kanta ta saci jiki ta nufi ban aki, da yake ban akin ya yi nesa da akuna don haka ta la e a can kusurwar bango ta fara magana. "Baba ga tawagar 'ya'yanka sun dawo. Kada ka tsorata mune dai fatalen nan." Aramma da ke tsugunne a kan masai sai abin ya yi masa a daidai, saboda wata sabuwar gudawa ce ta tsarge shi. Gumi ya fara tsattsafo masa ya ce. "To 'ya'yana don Allah kada ku ta a lafiyata, wallahi har yanzu ban warke ba." "Ba za mu sake cutar da kai ba, domin awarmu wato matacciyar 'yarka ta ce ta ga irin kyautatawar da kake yi wa iyayenta da 'yan uwanta. Ki yi masa magana ya ji sabuwar muryarki ta cikin jinsin fatalwa." Uwani ta yi maganar tana wani fuffuka, sannan ta ma ale murya ta furta. "Baba ni zan tafi da kai na fi so na dinga ganinka." Tamkar an bu e fanfo haka cikin Aramma ya birge, ya ci gaba da sakin gudawa babu autawa. Cikin tashin hankali ya ce. "Na yafe don Allah ki je ki auki mahaifiyarki." "Shi kenan Baba zan dai dinga kawo muku ziyara a oye duk dare ina ganin rayuwar da kuke yi, idan na ga sa anin abin da ka fara yi wallahi cikin tumbinka zan shiga, na kanna e hanjinka ita kuma kodarka na fansarwa shugaba." Uwani ta furta tana gimtse dariyarta. "Wallahi komai zan ci gaba da yi idan na sa a ki mini duk abin da za ki yi mini." "Mu zamu tafi Baba sai mun sake zagayowa." Uwani na gama fa ar haka ta fara wata fuffuka tana gurnani sannan ta sa a ta bar wurin. Saboda yadda Aramma ya razana bayan da ya gama uzurinsa a du e ya dinga tafiya, saboda yadda ya ji afafuwansa sun yi sanyi har sun gagara aukar nauyin gangar jikinsa. Ranar da aka yi sadakar uku dai tun da safe wasu daga cikin 'yan gaisuwa suka fara watsewa, domin dama wasu tamkar a kan aya suke. Ita ma Uwani sai da aka yi sallar la'asar sannan Aramma ya zo ya sanar da Maryama an zo aukan Uwani, ta so Uwani ta ara kwanaki amma babu yadda ta iya haka ta danne. Wasu daga cikin 'yan uwan mahaifiyarta sai tsokanarta suke suna amarya sai sun zo biki. Kafin Uwani ta fita sai da Maryama ta sata a gaba ta yi mata nasiha sosai. Fakare Uwani ta yi tana sauraronta kamar nasihar na shigarta, sai gya ai kai take tana amsawa. Sai da ta gama sauraron mahaifiyarsa sannan ta ce. "Ni kam Inna don Allah zan fa a miki wata magana amma don Allah kada ki fa a wa kowa." Take gaban Maryama ya fa i amma sai ta basar ta ce. "Ina jin ki babu wanda zai ji Uwanina." Duk abin da ya faru tun daga farko har arshe ta sanar da ita tana dariya, ita kanta Maryama dariya take she awa sanna ta ri e baki ta furta. "Allah Ya shirye ki Uwani ni dai wallahi ban san halin wa kika auka ba, mahaifinki dai har ya fi ni sau in kai. Allah Ya shirya ki ko ba komai kin samar mana 'yanci." Suna cikin haka suka ji arar horn da sauri Uwani ta sungumi jakar kayanta, ta auko hijabinta ta saka. Sai da ta yi wa mutanen gidan sallama da Aramma sannan ta arasa bakin motar