← Book details Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 69

Sashe 20

Gidan Likitoci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa." Inno ta yi kicin-kicin ta ha e rai ta ce. "Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a akin miji." "Wallahi idan na sake ganin Laraba a ofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike aure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai." Dr Fadil ya furta a zafafe yana barin wurin, a daidai lokacin Nabila ta arasa tana jin abin da yake faruwa. Inno tana shirin yin magana suka ji wani sabon kukan daga ofar shigowa. Salame 'yar gidan Larai ce ta arasa cikin kuka, kowannesu fuska auke da mamaki suka wurga mata tambaya. "Lafiya Salame?" Sai da ta share hawaye sannan ta ce, "Jamilu ne ya sake ni." Kusan lokaci aya suka auki salati, cikin kumfar baki Yaya Inu ya ce. "Uban me kika yi masa da zai sake ki a daren nan ga tsohon ciki a jikinki." Salame ta ja majina ta ce, "Saboda ya sayo shayi ruwan bunu da awara zai sha, ni kuma na ji sha'awarsu na auki waya biyu da shayin na sha. Shi ne kawai ya sake ni." Ta arasa maganar cikin kuka, takaici ya mamaye mutanen da suke tsaye. Yaya Inu a ufule ya ce. "Shayin banza da wofi da har zai sake ki a kansa, wannan ai rashin hankali ne. Bai ga halin da kike ciki ba ne?" Larai da ke tsaye ta saki murmushin takaici ta ce. "Dama gwano ai ba ya ta a jin warin jikinsa, yanzu mai gida har kana da bakin magana don an sako maka 'yarka, kuma a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Ai na sha fa a maka, wannan auri sakin da kake yi ba zai haifar mana da samun a mai ido ba, domin kai ma uba ne kuma duk abin da ka yi wa 'yar wani sai an yi wa ta ka. Idan ba ka manta ba fa, Raliya a kan osai ka sake ta. Mariya kuma a kan man shanu, ga Abu kuma a kan kai yara almajiranci. Ni ma da kake zaune da ni saboda na zama kujera ce, duk tarkacen yaran da ake tafiya a bar maka ni nake ri e su. Ka ga yanzu kai ma kana da zaurawa uku kenan a gida, wannan ka ai ya isa ya zame maka izina..." A fusace ya katse ta. "Larai ni za ki yi wa rashin mutumci a gaban mutane?" Baba Ibrahim ya ce, "A duk maganganun Larai babu cin mutumci, sai zallar gaskiyar da har yau ka gagara gane ta Yaya Inu, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka. Aure-auren da kake yi ya yi yawa wallahi, yanzu ko wu a aka saka mini ba zan iya lissafa adadin mata nawa ka aura ba. Ka gyara zamantakewarka da iyalinka, sai ka ga Allah Ya daidaita lamuranka. Duk da dama aure da mutuwa yana wurinsa, amma ka sani akwai jarabtar da Allah yake yi wa bawa a kan abin da yake aikatawa." Mai Yasin da ke gefe ya zuba wa Salame da kuka idanu yana lashe baki, saboda fara ce tas kamar Yaya Inu sai dai 'yar ibar mahaifiyarta da ta auko. 'Yanzu wannan dan waleliyar aka saki, ai kuwa wannan mijin nata an yi sakarai.' Malam ya furta a cikin ransa. "To tsohon munafuki, ai babu ku in kowa a cikin auren da nake yi, kuma babu aton da yake ciyar mini da su idan sun dawo gida. Ke shige gida muje." Yaya Inu ya arasa maganar yana tasa eyar Salame shi ma ya shige ciki, daga haka kowa ya watse. CIKIN DARE Tun da Mai Yasin ya ci karo da Salame ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka kawai ya ji wani abu yana fisgarsa a kanta. Duk da tana yanayin kama da Laraba amma ta fi Labara zama cikakkiyar mace 'yar duma-duma kamar yadda yake muradi, Inno da ke gefensa ta mi e za ta yi masa sallama ta ce. "To Malam ni zan wuce aki ko akwai abin da kake bu ata a yanzu?" Wani munin Inno ya gani saboda yadda Salame ta mamaye zuciyarsa, haushinta ya kama shi don haka ya an yi tsaki a hankali ya ce. "Babu komai za ki iya tafiya!" Inno ta yi mamakin yanayin furucin da ya yi mata, ganin haka ya sa Mai Yasin ya wayance da cewa. "Raina ne duk a ace wallahi, a ce ka saki mace da tsohon ciki wannan ai hauka ne." A fili Inno ta saki ajiyar zuciya cikin jin da i, don yadda Mai Yasin yake nuna wa zuri'arta kulawa abin yana burge ta. "Lamarin babu da i dai sam malam, ni bari na wuce sai da safe." Mai Yasin ya amsa mata yana alla-alla ta fice, shi ka ai ya dinga zarya a aki yana tunanin yadda zai ullowa halin da yake ciki. Wata dabara ce ta fa o masa ya saki murmushi mai sauti, kamar wanda aka yi wa dole haka Mai Yasin ya zauna tunkur har arfe biyun dare ta cika. Daga shi sai gajeren wando ya zare sakatar ofa ya nufi sashen Yaya Inu, wannan ne zuwansa na farko sashen don haka cikin san a ya kama gajeriyar katangar ya dira. Sakatar ofar ya zare ya bar ofar a bu e saboda koda rana ta wace masa ba zai sha wahalar guduwa ba.
Chapter 20 · 0% Book details